{"id":8201,"date":"2026-01-26T08:36:42","date_gmt":"2026-01-26T08:36:42","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=8201"},"modified":"2026-01-26T08:45:33","modified_gmt":"2026-01-26T08:45:33","slug":"babban-hafsan-sojin-sama-ya-tattauna-da-tsofaffin-sojoji-a-kaduna","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/babban-hafsan-sojin-sama-ya-tattauna-da-tsofaffin-sojoji-a-kaduna\/","title":{"rendered":"Babban Hafsan Sojin Sama Ya Tattauna da Tsofaffin Sojoji a Kaduna"},"content":{"rendered":"<p>Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta sake jaddada \u0199udirin ta na inganta walwalar jami\u2019anta, masu aiki da kuma wa\u0257anda suka yi ritaya.<\/p>\n<p>Babban Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Sunday Aneke, ya bayar da wannan tabbaci ne a yayin taron shekara ta 2025 na tattaunawa tsakanin Babban Hafsan Sojin Sama da tsofaffin sojoji da ke zaune a Jihar Kaduna.<\/p>\n<p>Air Marshal Sunday Aneke ya danganta nasarori da ci gaban da Rundunar Sojin Sama ta samu da \u0199o\u0199ari da sadaukarwar da tsofaffin sojoji suka yi a lokacin aikinsu.<\/p>\n<p>Da yake wakiltar Babban Hafsan, Babban Jami\u2019in Gudanarwa, Air Vice Marshal Anthony Martins, ya bayyana cewa domin girmama irin gudummawar da suka bayar, Rundunar Sojin Sama ta jajirce wajen kula da walwalarsu da jin da\u0257insu gaba \u0257aya.<\/p>\n<p>A cewarsa, an tsara shirye-shiryen tallafin walwala na musamman domin tsofaffin sojoji, ba wai kawai don inganta rayuwarsu ba, har ma da \u0199arfafa gwiwar jami\u2019an da ke kan aiki, ta hanyar tabbatar musu cewa za a kula da su yadda ya kamata bayan ritaya.<\/p>\n<p>Tun da farko, a jawabinsa na maraba, Kwamandan Rundunar Horar da Sojin Sama Air Vice Marshal Esen Efanga, ya bayyana cewa taron wata dama ce ta nazari kan ainihin ma\u2019anar zama tsohon soja, tare da jaddada cewa Rundunar Sojin Sama da kuma Sojojin \u0198asa gaba \u0257aya za su ci gaba da amfana da tarin gogewarsu.<\/p>\n<p>A nasa jawabin, Shugaban \u0198ungiyar Walwalar Tsofaffin Sojoji, Malam Usman Yusuf mai ritaya, ya nuna matukar farin ciki, yana mai cewa taron zai taimaka matu\u0199a wajen inganta rayuwar tsofaffin sojoji.<\/p>\n<p>Babban abin da ya dauki hankali a taron shi ne zaman tambaya da amsa kai tsaye, tare da shirye-shiryen kula da lafiya.<\/p>\n<p>Usman Sani<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta sake jaddada \u0199udirin ta na inganta walwalar jami\u2019anta, masu aiki da kuma wa\u0257anda suka yi ritaya. Babban Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Sunday Aneke, ya bayar da wannan tabbaci ne a yayin taron shekara ta 2025 na tattaunawa tsakanin Babban Hafsan Sojin Sama da tsofaffin sojoji da ke zaune [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":8219,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,2],"tags":[23],"class_list":["post-8201","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-siyasa","tag-tsaro"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/01\/efd81bf9-2e4d-4c76-946c-629be6a14864.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8201","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=8201"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8201\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":8203,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8201\/revisions\/8203"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/8219"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=8201"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=8201"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=8201"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}