{"id":8116,"date":"2026-01-16T16:08:10","date_gmt":"2026-01-16T16:08:10","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=8116"},"modified":"2026-01-16T16:08:10","modified_gmt":"2026-01-16T16:08:10","slug":"matasan-kauru-sun-yi-allah-wadai-da-mulkin-%c6%99arfi-sun-bu%c6%99aci-adalci-da-ha%c9%97in-kai","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/matasan-kauru-sun-yi-allah-wadai-da-mulkin-%c6%99arfi-sun-bu%c6%99aci-adalci-da-ha%c9%97in-kai\/","title":{"rendered":"Matasan Kauru Sun Yi Allah-wadai da Mulkin \u0198arfi, Sun Bu\u0199aci Adalci da Ha\u0257in Kai"},"content":{"rendered":"<p>&nbsp;<\/p>\n<p><strong><em>Daga Yusuf Zubairu<\/em><\/strong><\/p>\n<p>Wata \u0199ungiyar matasa a \u0198aramar Hukumar Kauru ta Jihar Kaduna ta bayyana cewa shugabanci na bai-\u0257aya ba tare da nuna rinjaye a bangare daya ba, shi ne ginshikin dorewar dimokura\u0257iyya da ha\u0257in kan al\u2019umma a yankin.<\/p>\n<p>\u0198ungiyar, wato Kauru Youth Ambassadors (KYA) ta yi wannan kira ne yayin mayar da martani ga kalaman wani mai suna <strong><em><a href=\"https:\/\/www.facebook.com\/share\/v\/1C1GUNVcAu\/\">Musa Waziri ne a wani bidiyo da ya karade kafafen yanar gizo<\/a><\/em><\/strong>, inda ta jaddada cewa Kauru ta \u0199unshi sassa uku ne da suka hada da\u00a0 Masarautar Kauru, Sarautar Kumana da Sarautar Chawai.<\/p>\n<p>A cewar \u0199ungiyar, kowanne daga cikin wa\u0257annan sassa uku na da masu ilimi, \u0199warewa da kishin \u0199asa, wa\u0257anda suka cancanci rike mu\u0199amai a kowane fanni.<\/p>\n<p>Da yake magana a madadin KYA, Kwamared Junaidu Ishaq Maisalati ya ce \u0199ungiyar ta soki ikirarin Waziri na cewa <em data-start=\"118\" data-end=\"161\">\u201cana \u0199wace iko ne, ba a bayar da shi ba,\u201d<\/em> inda ya bayyana cewa mafi akasari\u00a0 siyasa na karkata ne ga wa\u0257anda ke da rinjayen yawan jama\u2019a, da albarkatun kasa da damar shiga tsarin jam\u2019iyya.<\/p>\n<p>Ya bayyana cewa tsarin raba mulki (zoning) ba wajibi ba ne a harkar siyasa, illa hanya ce ta kaucewa watsi da wani yanki, tare da tabbatar da wakilci na adalci a al\u2019umma mai bambance-bambance kamar Kauru.<\/p>\n<p>\u0198ungiyar ta kuma bayyana cewa ba daidai ba ne a ce tsarin karba-karba wato zoning na haifar da shugabanni marasa \u0199warewa, alhali kuma ana da tabbacin cewa akwai \u0199wararru a dukkan sassan Kauru.<\/p>\n<p>Ta jaddada cewa tsarin na karba-karba ba ya rage \u0199a\u2019idar shugabanci, sai dai yana \u0199arfafa kowanne yanki ne ya gabatar da mafi cancantar \u2019ya\u2019yansa idan aka ba shi dama.<\/p>\n<p>A cewar \u0199ungiyar, mulki na karba karba\u00a0 yana \u0199arfafa tarbiyyar shugabanci, gina \u0199warewa da kuma \u0199arfafa cibiyoyin siyasa.<\/p>\n<p>Saboda haka, ta yi garga\u0257i cewa ci gaba da ke\u0253ance wasu sassa na iya haifar da rashin yarda, sakaci da \u0253acin rai, wanda hakan ke tauye ci gaba da ha\u0257in kan al\u2019umma.<\/p>\n<p>\u0198ungiyar Kauru Youth Ambassadors (KYA) ta nanata cewa ya zama wajibi a tabbatar da adalci domin samun ha\u0257in kai, zaman lafiya da ci gaba mai \u0257orewa a Kauru.<\/p>\n<p><!--\/data\/user\/0\/com.samsung.android.app.notes\/files\/clipdata\/clipdata_bodytext_260116_151153_978.sdocx--><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>&nbsp; Daga Yusuf Zubairu Wata \u0199ungiyar matasa a \u0198aramar Hukumar Kauru ta Jihar Kaduna ta bayyana cewa shugabanci na bai-\u0257aya ba tare da nuna rinjaye a bangare daya ba, shi ne ginshikin dorewar dimokura\u0257iyya da ha\u0257in kan al\u2019umma a yankin. \u0198ungiyar, wato Kauru Youth Ambassadors (KYA) ta yi wannan kira ne yayin mayar da martani [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":8126,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,2],"tags":[949,1676,1424,341,1905],"class_list":["post-8116","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-siyasa","tag-adalci","tag-hain-kai","tag-kauru","tag-matasa","tag-mulki"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/01\/kaduna-map-1.png","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8116","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=8116"}],"version-history":[{"count":6,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8116\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":8125,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8116\/revisions\/8125"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/8126"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=8116"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=8116"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=8116"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}