{"id":8084,"date":"2026-01-05T07:58:17","date_gmt":"2026-01-05T07:58:17","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=8084"},"modified":"2026-01-05T07:58:17","modified_gmt":"2026-01-05T07:58:17","slug":"tsaro-gwamnan-jihar-neja-ya-nuna-alhini-kan-harin-yan-taadda-a-alummomin-borgu","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/tsaro-gwamnan-jihar-neja-ya-nuna-alhini-kan-harin-yan-taadda-a-alummomin-borgu\/","title":{"rendered":"TSARO: Gwamnan Jihar Neja Ya Nuna Alhini Kan Harin \u2018Yan Ta\u2019adda a Al\u2019ummomin Borgu"},"content":{"rendered":"<p>Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umar Bago, ya bayyana matu\u0199ar ba\u0199in cikinsa kan harin \u2018yan ta\u2019adda da aka kai wa wasu al\u2019ummomi a Karamar Hukumar Borgu ta jihar, wanda ya yi sanadin salwantar rayuka da dama.<\/p>\n<p>A cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Ya\u0257a Labarai na Gwamna, Bologi Ibrahim, ya fitar wa manema labarai a Minna, gwamnan ya bayyana harin a matsayin mugun aiki da ta\u2019asa da rashin imani, wanda ya janyo mutuwar mutane da dama, sace wasu, tare da lalata hanyoyin dogaro da rayuwar jama\u2019a.<\/p>\n<p>Gwamna Umar Bago ya mi\u0199a ta\u2019aziyyarsa ta musamman ga al\u2019ummomin da abin ya shafa, musamman wa\u0257anda harin ya rutsa da su da iyalansu a Kasuwar Daji da \u0199auyen Sukumbara. Ya bayyana cewa wa\u0257anda abin ya shafa sun ha\u0257a da Musulmi da Kiristoci daga sassa daban-daban na Karamar Hukumar Borgu a Jihar Neja.<\/p>\n<p>Gwamnan ya ce abin yana da \u0257aure kai da tayar da hankali ganin an fara sabuwar shekara da irin wannan mummunan lamari. Ya kuma yi kira ga al\u2019ummar jihar da su ci gaba da dogaro ga Allah, yana mai tabbatar da cewa gwamnatinsa na ha\u0257in gwiwa da Gwamnatin Tarayya da hukumomin tsaro domin inganta tsaro a yankunan da abin ya shafa.<\/p>\n<p>A cewarsa, \u0199ungiyar tsaro ta ha\u0257in gwiwa na bin sawun \u2018yan ta\u2019addan da nufin ceto wa\u0257anda aka sace. Ya kuma yi addu\u2019ar Allah Ya ji\u0199an rayukan wa\u0257anda suka rasu, Ya kubutar da wa\u0257anda aka sace, Ya ba wa\u0257anda suka jikkata lafiya.<\/p>\n<p>A halin da ake ciki kuma, Shugaban \u0198asa Bola Ahmed Tinubu, ta bakin Mai Ba Shi Shawara na Musamman kan Harkokin Ya\u0257a Labarai da Hul\u0257a da Jama\u2019a, Bayo Onanuga, ya bayar da umarni ga Sojoji, \u2018Yan Sanda da DSS da su farauto \u2018yan ta\u2019addan da ke da hannu a harin Kasuwar Daji.<\/p>\n<p>PR Aliyu Lawal<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umar Bago, ya bayyana matu\u0199ar ba\u0199in cikinsa kan harin \u2018yan ta\u2019adda da aka kai wa wasu al\u2019ummomi a Karamar Hukumar Borgu ta jihar, wanda ya yi sanadin salwantar rayuka da dama. A cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Ya\u0257a Labarai na Gwamna, Bologi Ibrahim, ya fitar wa manema labarai a Minna, [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":8066,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[23],"class_list":["post-8084","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-tsaro"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/01\/niger-state-map.png","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8084","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=8084"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8084\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":8085,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8084\/revisions\/8085"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/8066"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=8084"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=8084"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=8084"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}