{"id":8053,"date":"2026-01-03T09:21:40","date_gmt":"2026-01-03T09:21:40","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=8053"},"modified":"2026-01-03T09:21:40","modified_gmt":"2026-01-03T09:21:40","slug":"an-bukaci-mazauna-rukunin-gidaje-harmony-su-rika-biyan-bashin-gidajensu","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/an-bukaci-mazauna-rukunin-gidaje-harmony-su-rika-biyan-bashin-gidajensu\/","title":{"rendered":"An Bukaci Mazauna Rukunin Gidaje Harmony Su Rika Biyan Bashin Gidajensu"},"content":{"rendered":"<p>An bukaci mazauna Rukunin gidajen Harmony da ke jihar Kwara da su \u0199ara \u0199aimi wajen biyan bashin lamunin gidajensu (mortgage), domin bai wa wasu ma damar cin gajiyar shirin mallakar gidaje.<\/p>\n<p>Manajan reshen Bankin Lamunin Gidaje na Tarayya (Federal Mortgage Bank of Nigeria \u2013 FMBN) na jihar Kwara, Alhaji Nurudeen Aliyu Muhammed, ne ya yi wannan kira a yayin bikin rantsar da mambobin kwamitin mazauna Harmony Estate da aka gudanar a Ilorin.<\/p>\n<p>Ya bayyana cewa yawancin mazauna gidan ba su cika ka\u2019idojin mallakar gidajen ba saboda rashin cika sharuddan biyan bashin.<\/p>\n<p>A cewarsa, bankin ya yi ha\u0199uri tsawon lokaci tare da barin masu zama a gidajen ba tare da biyan ku\u0257a\u0257en da suka dace ba.<\/p>\n<p>Alhaji Nurudeen ya gargadi mazauna da su yi abin da ya dace domin kauce wa korar su daga gidajen.<\/p>\n<p>Ya kuma bayyana cewa nan ba da jimawa ba bankin zai fara gina wani sabon rukuni na gidaje da za a sayar da kowanne a kan ku\u0257i Naira miliyan 25.<\/p>\n<p>Manajan ya \u0199ara da cewa za a samar da sabbin matakan tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da tsaron lafiyar al\u2019ummar yankin.<\/p>\n<p>A nasa jawabin yayin bikin rantsar da kwamitin, Shugaban Mazauna Harmony Estate Ilorin, Malam Otepola Adeolu, ya shawarci mambobin kwamitin da su kasance masu halartar tarurrukansu cikin lokaci.<\/p>\n<p>Ya ce manufar kafa kwamitin ita ce bai wa mambobin damar samun sahihin bayani kai tsaye kan al\u2019amuran da suka shafi mazauna gidan.<\/p>\n<p>Malam Adeolu ya kuma shawarci mazauna yankin da su tabbatar suna biyan ku\u0257a\u0257en wata-wata da na wutar lantarki da ruwa yadda ya kamata.<\/p>\n<p>Haka zalika, ya bukaci mambobin kwamitin da su rika adana bayanan ayyuka da kuma cikakkun bayanai na dukkan mazauna gidaje kusan 500 da ke cikin estate \u0257in.<\/p>\n<p>Shugaban ya yi kira ga hadin kan dukkan mambobi domin tabbatar da nasarar aiwatar da ayyukansu a sabuwar shekara.<\/p>\n<p><strong>Ali Muhammad Rabiu<\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>An bukaci mazauna Rukunin gidajen Harmony da ke jihar Kwara da su \u0199ara \u0199aimi wajen biyan bashin lamunin gidajensu (mortgage), domin bai wa wasu ma damar cin gajiyar shirin mallakar gidaje. Manajan reshen Bankin Lamunin Gidaje na Tarayya (Federal Mortgage Bank of Nigeria \u2013 FMBN) na jihar Kwara, Alhaji Nurudeen Aliyu Muhammed, ne ya yi [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":8054,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[5,1,11],"tags":[540],"class_list":["post-8053","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-kasuwanci","category-labarai","category-labaran-gida","tag-gidaje"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/01\/9796a69e-ed35-4266-8fa8-2e9e33272855.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8053","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=8053"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8053\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":8055,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8053\/revisions\/8055"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/8054"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=8053"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=8053"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=8053"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}