{"id":8030,"date":"2026-01-02T09:35:12","date_gmt":"2026-01-02T09:35:12","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=8030"},"modified":"2026-01-02T09:35:43","modified_gmt":"2026-01-02T09:35:43","slug":"ndlea-kano-ta-kama-mutane-1389-tare-da-kwace-tan-7-7-na-miyagun-%c6%99wayoyi-a-2025","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/ndlea-kano-ta-kama-mutane-1389-tare-da-kwace-tan-7-7-na-miyagun-%c6%99wayoyi-a-2025\/","title":{"rendered":"NDLEA Kano Ta Kama Mutane 1,389 a 2025"},"content":{"rendered":"<p>Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun \u0198wayoyi ta \u0198asa (NDLEA), reshen <strong>Kano<\/strong>, ta samu gagarumar nasara a shekarar 2025, inda ta kama mutane <strong>1,389<\/strong> da ake zargi da laifukan da suka shafi miyagun \u0199wayoyi, tare da kwace <strong>kilogiram 7,773.06<\/strong> na nau\u2019o\u2019in miyagun \u0199wayoyi daban-daban, ciki har da tabar wiwi, da ta aljannu da kokin da a farci kasa da kuma \u0199wayoyin maye na kwakwalwa.<\/p>\n<p>Wadannan alkaluma, kamar yadda Jami\u2019in Hul\u0257a da Jama\u2019a na hukumar, <strong>Sadiq Muhammad Maigatari<\/strong>, ya bayyana, sun nuna irin gagarumar nasarar da rundunar ta samu \u0199ar\u0199ashin jagorancin Kwamanda <strong>CN D.Y. Lawal<\/strong> wajen ya\u0199i da fatauci da shan miyagun \u0199wayoyi a fa\u0257in jihar Kano.<\/p>\n<p>Daga cikin wa\u0257anda aka kama, <strong>1,346 maza ne yayin da mata 43<\/strong> ne. Haka kuma rundunar ta samu <strong>hukunci 141<\/strong> a kotu, lamarin da ya zama darasi ga masu shirin aikata irin wa\u0257annan laifuka, inda manyan dillalan miyagun \u0199wayoyi guda hu\u0257u suka samu hukuncin da ya kai <strong>shekaru 33<\/strong> a gidan yari gaba \u0257aya.<\/p>\n<p>Baya ga kamen mutane da gurfanarwa, rundunar ta kuma samu nasarar <strong>kwace wani gida<\/strong> da aka mallaka ta hanyar kudaden miyagun \u0199wayoyi, tare da <strong>kwace wasu kadarori biyu na wucin gadi<\/strong>, yayin da <strong>shari\u2019o\u2019i 133<\/strong> ke ci gaba da sauraro a Kotun Tarayya.<\/p>\n<p>A fannin gyara da wayar da kan jama\u2019a, NDLEA Kano ta ba da muhimmanci ga shirin farfa\u0257o da masu shaye-shaye da hul\u0257a da al\u2019umma. Mutane <strong>94<\/strong> sun kammala shirye-shiryen gyaran hali na musamman, yayin da <strong>mutane 1,009<\/strong> (ciki har da mata 28) suka samu shawarwari na gajeren lokaci.<\/p>\n<p>Rundunar ta gudanar da <strong>kamfe 254<\/strong> na ya\u0199i da miyagun \u0199wayoyi a makarantu, kasuwanni da cibiyoyin al\u2019umma, inda ta kai sa\u0199on wayar da kai ga <strong>mutane 86,939<\/strong> (maza 41,225 da mata 45,714) ta hanyar taruka da shirye-shiryen wayar da kai kan illolin shan miyagun \u0199wayoyi.<\/p>\n<p>Haka kuma, hukumar ta gudanar da <strong>gwaje-gwajen shan miyagun <\/strong><strong>\u0199<\/strong><strong>wayoyi 527<\/strong>, inda <strong>mutane 64<\/strong> suka nuna alamun shan \u0199wayoyi. Daga cikin wa\u0257anda aka yi wa gwajin har da sarakunan gargajiya da shugabannin al\u2019umma, domin jaddada muhimmancin shugabanci mara ala\u0199a da miyagun \u0199wayoyi a jihar.<\/p>\n<p>A cikin ha\u0257in gwiwa da sauran hukumomin tsaro da na sa ido, NDLEA Kano ta mi\u0199a wasu shari\u2019o\u2019i ga <strong>\u2019Yan Sanda, Sojoji, DSS, NAFDAC da EFCC<\/strong>, wa\u0257anda suka shafi laifuka irin su safarar makamai, \u2019yan bindiga, damfara, sata da kuma magungunan bogi.<\/p>\n<p><strong>Khadijah Aliyu<\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun \u0198wayoyi ta \u0198asa (NDLEA), reshen Kano, ta samu gagarumar nasara a shekarar 2025, inda ta kama mutane 1,389 da ake zargi da laifukan da suka shafi miyagun \u0199wayoyi, tare da kwace kilogiram 7,773.06 na nau\u2019o\u2019in miyagun \u0199wayoyi daban-daban, ciki har da tabar wiwi, da ta aljannu da kokin da [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":8031,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[489],"class_list":["post-8030","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-ndlea"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/01\/e0fbfc0b-da7d-430f-ba7f-475b561e184a.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8030","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=8030"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8030\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":8033,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8030\/revisions\/8033"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/8031"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=8030"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=8030"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=8030"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}