{"id":8027,"date":"2026-01-02T09:31:23","date_gmt":"2026-01-02T09:31:23","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=8027"},"modified":"2026-01-02T09:31:23","modified_gmt":"2026-01-02T09:31:23","slug":"daliban-buk-300-za-su-ci-gajiyar-horon-aikin-gona-don-kasuwanci","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/daliban-buk-300-za-su-ci-gajiyar-horon-aikin-gona-don-kasuwanci\/","title":{"rendered":"Daliban BUK 300 Za Su Ci Gajiyar Horon Aikin Gona don Kasuwanci"},"content":{"rendered":"<p>Cibiyar Noma a Yankunan Busassu (Centre for Dryland Agriculture \u2013 CDA) ta Jami\u2019ar Bayero Kano (BUK) ta ha\u0257a gwiwa da \u0198ungiyar Ci Gaban Mata Manoma (Women Farmers Advancement Network \u2013 WOFAN) da kuma Kwalejin Aikin Gona, domin horas da daliban aikin gona 300 a duk shekara kan harkokin noma don kasuwanci da \u0199ara darajar amfanin gona, sarrafawa da kuma samarwa, \u0199ar\u0199ashin shirin <strong>SIBLING Project<\/strong>.<\/p>\n<p>Shirin, wanda ya shafi daliban matakai na aji 3 zuwa 4, an bayyana shi ne yayin wata ziyarar girmamawa da tawaga ta ha\u0257in gwiwa daga WOFAN, CDA da Kwalejin Aikin Gona suka kai wa Shugaban Jami\u2019ar, Farfesa Haruna Musa.<\/p>\n<p>A \u0199ar\u0199ashin shirin, CDA ta ware filin gwaji mai girman hekta biyu, yayin da Kwalejin Aikin Gona ta samar da hekta 25 domin noman manyan gonaki da horo na aikace-aikace.<\/p>\n<p>Shirin zai kuma bai wa dalibai damar fahimtar darajar noma da kasuwancin noma da kwarewar aikace-aikace da ke taimakawa bun\u0199asa <strong>aiki<\/strong> mai \u0257orewa.<\/p>\n<p>Da yake jawabi a lokacin ziyarar, Farfesa Haruna Musa ya yaba da ha\u0257in gwiwar, inda ya bayyana ta a matsayin muhimmin tsari na \u0199arfafa matasa da mata, yana mai nuna cewa mata 180 ne daga cikin daliban 300 da za su amfana da shirin.<\/p>\n<p>Da yake karin haske kan ha\u0257in gwiwar, Daraktan CDA, Farfesa Sanusi Gaya Mohammed, ya bayyana cewa CDA da WOFAN sun samu damar amfani da rumbun ajiya na \u0199asa ta hannun Cibiyar \u0198asa ta Inganta Ayyukan Rumbunan Ajiya ta Nijeriya (National Storage Productivity Institute of Nigeria).<\/p>\n<p>A nata jawabin, Daraktar WOFAN a \u0199asa, Dakta Salamatu Garba, ta ce shirin na da nufin sauya yadda mata da matasa ke shiga harkar noma ta hanyar basu kwarewa, samun filayen noma da kayan aiki, tare da kasuwa mai tabbas.<\/p>\n<p>Shi ma yana jawabi, Dekan Kwalejin Aikin Gona, Farfesa Muhammad Auwal Hussain, ya ce shirin ya samo asali ne daga bu\u0199atun dalibai da matan ma\u2019aikata, tare da ha\u0257a al\u2019ummomi biyu daga yankin Zango domin \u0199arfafa hul\u0257ar al\u2019umma da ci gaba mai ha\u0257a kowa da kowa.<\/p>\n<p><strong>Khadijah Aliyu<\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Cibiyar Noma a Yankunan Busassu (Centre for Dryland Agriculture \u2013 CDA) ta Jami\u2019ar Bayero Kano (BUK) ta ha\u0257a gwiwa da \u0198ungiyar Ci Gaban Mata Manoma (Women Farmers Advancement Network \u2013 WOFAN) da kuma Kwalejin Aikin Gona, domin horas da daliban aikin gona 300 a duk shekara kan harkokin noma don kasuwanci da \u0199ara darajar amfanin [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":8028,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[5,1,11],"tags":[736],"class_list":["post-8027","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-kasuwanci","category-labarai","category-labaran-gida","tag-buk"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/01\/a524b04e-c837-4240-9cb9-c07facef31fa.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8027","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=8027"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8027\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":8029,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8027\/revisions\/8029"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/8028"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=8027"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=8027"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=8027"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}