{"id":8020,"date":"2026-01-02T09:27:37","date_gmt":"2026-01-02T09:27:37","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=8020"},"modified":"2026-01-02T09:27:37","modified_gmt":"2026-01-02T09:27:37","slug":"an-bukaci-kiristocin-kwara-su-taimaki-wasu-a-sabuwar-shekara","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/an-bukaci-kiristocin-kwara-su-taimaki-wasu-a-sabuwar-shekara\/","title":{"rendered":"An Bukaci Kiristocin Kwara Su Taimaki Wasu a Sabuwar Shekara"},"content":{"rendered":"<p>An yi kira ga Kiristoci a jihar Kwara da su yi amfani da ni\u2019imomin da Allah Ya hore musu wajen inganta rayuwar sauran al\u2019umma, musamman masu bukata, a wannan sabuwar shekara.<\/p>\n<p>Bishop na Cocin Anglican, Right Reverend Sunday Adewole, ne ya yi wannan kira a cikin sakon sabuwar shekararsa da ya gabatar wa mabiya a cocin St. Barnabas Cathedral da ke Ilorin.<\/p>\n<p>Ya ce akwai matu\u0199ar bu\u0199atar masu hali su tallafa wa marasa galihu domin faranta musu rai da rage musu wahalhalu.<\/p>\n<p>A cewarsa, idan lokaci ya yi na zuwa wurin aiki, bai dace mutum ya kasance yana coci yana ibada ba, domin kowane abu yana da lokacinsa.<\/p>\n<p>Bishop Adewole ya jaddada cewa lokaci ya yi da ya kamata kowa ya \u0257auki aikinsa da muhimmanci sosai, tare da guje wa sakaci da lalaci a harkokin kasuwanci ko aiki.<\/p>\n<p>Ya \u0199ara da cewa ya dace a ba kowane abu muhimmancin da ya dace da shi, yana mai cewa duk wanda ke neman wadata da ci gaba, ya nemi taimakon Allah ta hanyar ro\u0199on Ubangiji.<\/p>\n<p>Bishop Adewole ya kuma shawarci mabiya da su nuna \u0199auna da himma a aikinsu, su saita manufofi domin tabbatar da ci gaba da bun\u0199asa rayuwa a wannan sabuwar shekara.<\/p>\n<p>Limamin ya \u0199ara da kiran da ya yi musu na ci gaba da kasancewa masu yawan addu\u2019a, tare da sadaukar da kansu ga karatun Littafi Mai Tsarki a kowane lokaci, domin samun nasara a rayuwarsu.<\/p>\n<p>Haka kuma ya gargade su da su kasance masu gamsuwa da abin da suke da shi, tare da ladabi da bin doka, domin hakan ne zai taimaka musu wajen cimma burinsu a rayuwa<\/p>\n<p><strong>Ali Muhammad Rabiu<\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>An yi kira ga Kiristoci a jihar Kwara da su yi amfani da ni\u2019imomin da Allah Ya hore musu wajen inganta rayuwar sauran al\u2019umma, musamman masu bukata, a wannan sabuwar shekara. Bishop na Cocin Anglican, Right Reverend Sunday Adewole, ne ya yi wannan kira a cikin sakon sabuwar shekararsa da ya gabatar wa mabiya a [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":8021,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[175],"class_list":["post-8020","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-kwara"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/01\/0f013172-b0d8-4aaf-8f6a-8111cb0df341.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8020","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=8020"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8020\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":8022,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8020\/revisions\/8022"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/8021"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=8020"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=8020"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=8020"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}