{"id":7968,"date":"2025-12-24T10:42:56","date_gmt":"2025-12-24T10:42:56","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=7968"},"modified":"2025-12-24T10:42:56","modified_gmt":"2025-12-24T10:42:56","slug":"tsadar-kayan-aiki-faduwar-farashi-na-barazana-ga-manoman-najeriya-mikati","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/tsadar-kayan-aiki-faduwar-farashi-na-barazana-ga-manoman-najeriya-mikati\/","title":{"rendered":"Tsadar Kayan Aiki, Faduwar Farashi Na Barazana Ga Manoman Najeriya \u2013 Mikati"},"content":{"rendered":"<p>&nbsp;<\/p>\n<p><strong><em>Daga Yusuf Zubairu\u00a0<\/em><\/strong><\/p>\n<p>Shugaban Kwamitin Amintattu na \u0198ungiyar Masu Samar da Amfanin Gona ta Arewa maso Yamma NOWACAS, Shuaibu Idris Mikati, ya yi gargadin cewa manoman Najeriya na cikin mawuyacin hali sakamakon tsadar noma, yayin da farashin amfanin gona ke kara faduwa.<\/p>\n<p>Mikati ya bayyana wannan gargadin ne a ranar Talata yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Kaduna, inda ya ce halin da ake ciki abin damuwa ne \u0199warai domin zai iya haifar da karancin abinci a kasa muddin ba a \u0257auki matakin gaggawa ba.<\/p>\n<p>Ya ce duk da cewa ana ganin kamar farashin abinci na da tsada idan aka kwatanta da naira, cikakken bincike kan musayar ku\u0257a\u0257e na \u0199asashen waje yana nuna wani yanayi daban.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A cewarsa, idan aka auna farashin wasu amfanin gona da dalar Amurka, za a ga cewa a zahiri sun fi araha a yau fiye da yadda suke a shekarun baya.<\/p>\n<p>Shuaibu Mikati ya ce a halin yanzu ana sayan buhun masara naira dubu 30, bayan da manoman da suka sayi taki kusan Naira dubu 100 kowanne buhu, wanda hakan ba karamar asara ba ce, kuma ba zai haifar da &#8216;Da dai ido ba.<\/p>\n<p>Ya bayyana cewa a da, manomi na iya musanya buhun amfanin gona guda \u0257aya da buhun taki \u0257aya, amma a yau dole ne ya sayar da buhu biyu da rabi zuwa uku kafin ya samu buhun taki guda.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-7975\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/12\/IMG_20251223_135805_217-300x225.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"225\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/12\/IMG_20251223_135805_217-300x225.jpg 300w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/12\/IMG_20251223_135805_217-1024x768.jpg 1024w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/12\/IMG_20251223_135805_217-768x576.jpg 768w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/12\/IMG_20251223_135805_217-1536x1152.jpg 1536w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/12\/IMG_20251223_135805_217-2048x1536.jpg 2048w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/p>\n<p>Ya yi garga\u0257in cewa idan ba a samar wa manoma kayan aiki da taki cikin sau\u0199i da rahusa ba, samar da abinci zai ragu \u0199warai, lamarin da zai zama babbar barazana ga wadatar abinci a Najeriya.<\/p>\n<p>Shugaban NOWACAS ya soki manufofin gwamnati da ke ba da damar shigo da amfanin gona daga waje a farashin da ke gogayya da na gida ba tare da samar da \u0199ayyadadden farashin da zai zamto kariya ga manoman cikin gida ba.<\/p>\n<p>A cewarsa, shigo da kayayyaki daga waje na rage darajar farashin amfanin gona na gida, yayin da manoman Najeriya ba su da wata kariya ko diyar da suke samu sakamakon asarar amfanin gona.<\/p>\n<p>Mikati ya yi kira ga Majalisar Dokoki ta \u0198asa da ta gaggauta zartar da dokar National Trust Receipt (Warehouse Receipt) da ta da\u0257e ana jira, wadda za ta ba manoma damar samun rance ta hanyar amfani da takardun rumbunan ajiya a matsayin jingina.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-7976\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/12\/IMG_20251223_134747_658-300x225.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"225\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/12\/IMG_20251223_134747_658-300x225.jpg 300w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/12\/IMG_20251223_134747_658-1024x768.jpg 1024w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/12\/IMG_20251223_134747_658-768x576.jpg 768w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/12\/IMG_20251223_134747_658-1536x1152.jpg 1536w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/12\/IMG_20251223_134747_658-2048x1536.jpg 2048w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/p>\n<p>Ya kuma soki dakatar da tallafin ku\u0257a\u0257en noma sakamakon yadda wasu suka karkatar da kudaden a baya, yana mai cewa hakan ba adalci ba ne ga manoman gaskiya.<\/p>\n<p>Mikati ya bu\u0199aci Babban Bankin Najeriya (CBN) da ya rika bada tallafin ku\u0257a\u0257en noma ta hannun Bankin Manoma na Kasa (Nigerian Agricultural and Cooperative Development Bank) domin tabbatar da ganin kwalliya tana biyan kudin sabulu.<\/p>\n<p>Ya jaddada shirye-shiryen NOWACAS na yin aiki da gwamnati a kowane mataki, tare da yin kira ga kafafen ya\u0257a labarai da su \u0199ara kaimi wajen yada al&#8217;amuran da suka shafi manoma, yana mai cewa wadata kasa da abinci muhimmin ginshi\u0199i ne ga rayuwa da daidaiton tattalin arzikin Najeriya.<\/p>\n<p><strong><em>Yusuf Zubairu\u00a0<\/em><\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>&nbsp; Daga Yusuf Zubairu\u00a0 Shugaban Kwamitin Amintattu na \u0198ungiyar Masu Samar da Amfanin Gona ta Arewa maso Yamma NOWACAS, Shuaibu Idris Mikati, ya yi gargadin cewa manoman Najeriya na cikin mawuyacin hali sakamakon tsadar noma, yayin da farashin amfanin gona ke kara faduwa. Mikati ya bayyana wannan gargadin ne a ranar Talata yayin wani taron [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":18,"featured_media":7973,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[19,1884,853,1883,1710,381,1885,1882,968],"class_list":["post-7968","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-barazana","tag-faduwa","tag-farashi","tag-kayan-aiki","tag-ungiya","tag-manoma","tag-mikati","tag-nowacas","tag-tsada"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/12\/MIKATI.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7968","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/18"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=7968"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7968\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":7977,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7968\/revisions\/7977"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/7973"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=7968"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=7968"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=7968"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}