{"id":7920,"date":"2025-12-18T13:34:12","date_gmt":"2025-12-18T13:34:12","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=7920"},"modified":"2025-12-18T13:34:12","modified_gmt":"2025-12-18T13:34:12","slug":"gwamnan-zamfara-ya-sanya-hannu-kan-dokar-kasafin-2026","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamnan-zamfara-ya-sanya-hannu-kan-dokar-kasafin-2026\/","title":{"rendered":"Gwamnan Zamfara Ya Sanya Hannu Kan Dokar Kasafin 2026"},"content":{"rendered":"<p><strong><em>Daga Aminu Dalhatu\u00a0<\/em><\/strong><\/p>\n<p>Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya sanya hannu kan dokar Kasafin Ku\u0257in Shekarar 2026, bayan Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta amince da shi.<\/p>\n<p>An gudanar da bikin sanya hannun ne a Fadar Gwamnati da ke Gusau.<\/p>\n<p>Sai dai a wajen taron, gwamnan bai bayyana jimillar adadin kasafin ku\u0257in shekarar ta 2026 ba.<\/p>\n<p>Tun a ranar 4 ga watan Disamba ne Gwamna Dauda Lawal ya gabatar da kasafin ku\u0257i da ya haura naira biliyan 861 na shekarar 2026 ga Majalisar Dokokin Jihar Zamfara domin amincewa.<\/p>\n<p>Manyan jami\u2019an da suka halarci taron sun ha\u0257a da Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara, Mani Malam Mumini; Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, Bilyaminu Isma\u2019il Moriki; Sakataren Gwamnatin Jihar (SSG); Shugaban Ma\u2019aikata (Chief of Staff); kwamishinoni da sauran manyan jami\u2019an gwamnati.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A baya, Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta riga ta amince da Kudirin Kasafin Ku\u0257in 2026 ya zama doka, bayan gabatar da rahoton Kwamitin Majalisar kan Ku\u0257i da Kasafi.<\/p>\n<p>Kudirin ya tanadi jimillar kasafin ku\u0257i na naira biliyan 871.337 domin shekarar\u00a0 2026.<\/p>\n<p>Yayin gabatar da rahoton kwamitin, Shugaban Kwamitin, Rilwanu Marafa Na Gambo, ya bayyana cewa dukkan Ma\u2019aikatun Gwamnati, Hukumomi da Cibiyoyi (MDAs) a jihar sun bayyana gaban kwamitin tare da kare kasafin ku\u0257insu. Ya \u0199ara da cewa an samu gagarumin ci gaba a tsarin samun ku\u0257a\u0257en shiga na yawancin hukumomi.<\/p>\n<p>Na Gambo ya kuma bayyana cewa kwamitin ya ba da shawarar \u0199ara naira biliyan 8 domin ayyukan ci gaba (capital expenditure) a Ma\u2019aikatar Kananan Hukumomi da Harkokin Sarauta, tare da \u0199ara naira biliyan 2 domin ku\u0257a\u0257en gudanarwa (recurrent expenditure) ga Majalisar Dokokin Jihar Zamfara.<\/p>\n<p>A lokacin amincewa da kudirin, Shugaban Majalisar, Bilyaminu Isma\u2019il Moriki, ya ce Majalisar ta yi la\u2019akari da manyan abubuwan da ya kamata gwamnati ta fi bai wa fifiko yanzu, da suka ha\u0257a da tsaro, noma, lafiya, ilimi da gine-gine.<\/p>\n<p>Ya ce an tsara kasafin ku\u0257in ne domin ya dace da bu\u0199atu da muradun al\u2019umma a matakin \u0199ananan hukumomi da sauran fannoni, tare da tabbatar da daidaiton kasafi da mai da hankali sosai kan adalci da ha\u0257a kowa da kowa.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Aminu Dalhatu\u00a0 Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya sanya hannu kan dokar Kasafin Ku\u0257in Shekarar 2026, bayan Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta amince da shi. An gudanar da bikin sanya hannun ne a Fadar Gwamnati da ke Gusau. Sai dai a wajen taron, gwamnan bai bayyana jimillar adadin kasafin ku\u0257in shekarar ta 2026 ba. [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":7922,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,9],"tags":[1800,115],"class_list":["post-7920","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-tattalin-arziki","tag-kasafin-2026","tag-zamfara"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/12\/IMG-20251218-WA0006.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7920","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=7920"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7920\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":7923,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7920\/revisions\/7923"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/7922"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=7920"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=7920"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=7920"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}