{"id":7888,"date":"2025-12-17T13:52:40","date_gmt":"2025-12-17T13:52:40","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=7888"},"modified":"2025-12-17T13:52:40","modified_gmt":"2025-12-17T13:52:40","slug":"nlc-ta-gudanar-da-gangamin-lumana-a-kano","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/nlc-ta-gudanar-da-gangamin-lumana-a-kano\/","title":{"rendered":"NLC Ta Gudanar da Gangamin Lumana a Kano"},"content":{"rendered":"<p><strong><em>Daga Abdullahi Jalaluddeen<\/em><\/strong><\/p>\n<p>Kungiyar \u0198wadago ta Najeriya (NLC) ta gudanar da gangamin lumana a jihar Kano domin jawo hankalin jama\u2019a kan \u0199alubalen tsaro da ke addabar \u0199asa, tare da mi\u0199a wasikar bukatu ga Gwamnatin Jihar Kano.<\/p>\n<p>Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Ma\u2019aikatan Gidan Gwamnatin Jihar Kano, Dakta Suleiman Sani Wali, wanda ya wakilci Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya ce gwamnatin jihar na da kyakkyawar alaka da \u0199ungiyoyin \u0199wadago, inda ya bayyana gangamin a matsayin shaida ta zaman lafiya da fahimta tsakanin gwamnati da ma\u2019aikata.<\/p>\n<p>Ya bayyana gamsuwarsa bisa yadda aka gudanar da gangamin cikin lumana da tsari, yana mai cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da jajircewa wajen yin mu\u2019amala mai kyau da \u0199ungiyoyin \u0199wadago.<\/p>\n<p>Shugaban Ma\u2019aikatan ya tabbatar wa NLC cewa ana \u0257aukar batutuwan tsaro da muhimmanci a jihar, inda ya ce dukkan hukumomin tsaro na aiki gwargwadon \u0199arfinsu domin ci gaba da tabbatar da zaman lafiya a Kano.<\/p>\n<p>Ya kuma ce gwamnan zai duba wasikar da NLC ta gabatar tare da tabbatar da cewa an isar da abubuwan da ke cikinta ga hukumomin da suka dace, ciki har da Shugaban \u0198asa.<\/p>\n<p>Tun da fari, wakilin Shugaban NLC na \u0199asa, Mista Muttaqa Yusha\u2019u, ya ce gangamin ya yi daidai da kudurin Kwamitin Zartarwa na \u0198asa (NEC) na NLC na shirya gangamin lumana a fadin \u0199asar domin wayar da kan jama\u2019a kan matsalar rashin tsaro da kuma inganta zaman lafiya.<\/p>\n<p>Yusha\u2019u ya jaddada cewa rashin tsaro na shafar ma\u2019aikata a kowane fanni, ciki har da malamai, ma\u2019aikatan lafiya, manoma, \u2019yan kasuwa da jami\u2019an tsaro, yana mai cewa ba za a samu ci gaba ba tare da tsaro da zaman lafiya ba.<\/p>\n<p>Ya yi kira da a samar da tsarin hadin gwiwa tsakanin gwamnatocin tarayya, jihohi da kananan hukumomi, tare da shugabannin al\u2019umma da \u0199ungiyoyin ma\u2019aikata, domin shawo kan matsalolin tsaro yadda ya kamata.<\/p>\n<p>Haka nan, Shugaban NLC na Jihar Kano, Mista Kabiru Inuwa, ya yaba wa Gwamnatin Jihar Kano bisa ci gaba da tabbatar da zaman lafiya a jiharjisai dai ya bukaci a \u0199ara \u0199aimi domin hana ya\u0257uwar rashin tsaro daga sauran sassan \u0199asar.<\/p>\n<p>Inuwa ya jaddada bu\u0199atar inganta walwala da tallafi ga jami\u2019an tsaro da iyalansu, yana mai bayyana cewa ha\u0257in gwiwa tsakanin gwamnatoci da \u0199ungiyoyin \u0199wadago shi ne hanya mafi dacewa ta samar da tsaro mai \u0257orewa.<\/p>\n<p>Kungiyar NLC ta sake jaddada aniyar ta na goyon bayan duk wata gwamnati da ke bada fifiko ga walwalar ma\u2019aikata, zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki da zamantakewa.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Abdullahi Jalaluddeen Kungiyar \u0198wadago ta Najeriya (NLC) ta gudanar da gangamin lumana a jihar Kano domin jawo hankalin jama\u2019a kan \u0199alubalen tsaro da ke addabar \u0199asa, tare da mi\u0199a wasikar bukatu ga Gwamnatin Jihar Kano. Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Ma\u2019aikatan Gidan Gwamnatin Jihar Kano, Dakta Suleiman Sani Wali, wanda ya wakilci [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":7889,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[1868,39,17],"class_list":["post-7888","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-gangami","tag-kano","tag-nlc"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/12\/NLC-1.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7888","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=7888"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7888\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":7890,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7888\/revisions\/7890"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/7889"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=7888"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=7888"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=7888"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}