{"id":7869,"date":"2025-12-15T21:36:28","date_gmt":"2025-12-15T21:36:28","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=7869"},"modified":"2025-12-15T21:36:28","modified_gmt":"2025-12-15T21:36:28","slug":"gwamnatin-jigawa-za-ta-farfado-da-cibiyoyin-kiwon-dabbobi-a-gumel-birniwa-da-kazaure","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamnatin-jigawa-za-ta-farfado-da-cibiyoyin-kiwon-dabbobi-a-gumel-birniwa-da-kazaure\/","title":{"rendered":"Gwamnatin Jigawa Za Ta Farfado da Cibiyoyin Kiwon Dabbobi a Gumel, Birniwa da Kazaure"},"content":{"rendered":"<p><strong><em>Daga Usman Muhammad Zaria<\/em><\/strong><\/p>\n<p>Gwamnatin Jihar Jigawa ta ware sama da naira biliyan 17 domin bun\u0199asa harkar kiwo a fa\u0257in jihar.<\/p>\n<p>Kwamishinan Harkokin Kiwon Dabbobi na jihar, Farfesa Abdulrahman Salim ne ya bayyana hakan ga manema labarai bayan kare kasafin ku\u0257in da ma\u2019aikatarsa ta gabatar na shekarar\u00a0 2026 a gaban Kwamitin Majalisar Dokokin Jihar Jigawa mai kula da harkokin noma, a Dutse.<\/p>\n<p>Farfesa Abdulrahman Salim ya ce za a yi amfani da ku\u0257a\u0257en wajen aiwatar da manyan ayyuka daban-daban da suka shafi bun\u0199asa kiwo a shekarar 2026.<\/p>\n<p>Ya \u0199ara da cewa ma\u2019aikatar ta shirya kafa wuraren kiwo (ranches) a sassan jihar, inda makiyaya da sauran masu kiwon dabbobi za su zauna.<\/p>\n<p>A cewarsa, a wa\u0257annan wuraren da za a ware domin kiwo, makiyaya za su samu ingantaccen abincin dabbobi, makarantu masu kyau ga \u2019ya\u2019yansu, cibiyoyin lafiya, asibitocin dabbobi, kasuwanni, wutar lantarki da ruwan sha.<\/p>\n<p>Farfesa Salim ya ce hakan zai taimaka wa ma\u2019aikatar wajen rage yawan rikice-rikicen da ke faruwa tsakanin manoma da makiyaya a jihar.<\/p>\n<p>Kwamishinan ya \u0199ara da cewa za a kuma yi amfani da ku\u0257in wajen kafa asibitocin dabbobi a dukkan \u0199ananan hukumomi 27 na jihar, da asibitocin dabbobi na shiyyoyi guda bakwai, tare da babban asibitin dabbobi na tsakiya da zai zama cibiyar tura marasa lafiya (referral centre).<\/p>\n<p>Ya ce duk da suna da \u0199wararrun likitocin dabbobi, akwai bu\u0199atar horaswa da sake horas da ma\u2019aikatan matsakaici da na \u0199ananan matakai.<\/p>\n<p>Haka kuma ya bayyana cewa ma\u2019aikatar ta shirya farfa\u0257o da cibiyoyin kiwon dabbobi guda uku da ke Gumel, Birniwa da \u0199aramar hukumar Kazaure, inda ya ce tuni aka fara aiki a wasu daga cikin cibiyoyin.<\/p>\n<p>Farfesa Salim ya \u0199ara da cewa za a fara ne da kafa wuraren kiwo guda uku a matsayin gwaji, tare da \u0199anana da za a danganta da sarrafa kayan madara ko kayan kiwon dabbobi na makiyaya.<\/p>\n<p>Ya ce ma\u2019aikatar na da ayyuka masu yawa a fannin sarrafa nama, inda aka raba su kashi biyu. Na farko shi ne ayyukan mazabun \u2019yan majalisar dokoki da suka kai kimanin naira miliyan 355, wa\u0257anda suka ha\u0257a da gina wuraren yanka dabbobi da manyan gidajen yanka.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin Jihar Jigawa ta ware sama da naira biliyan 17 domin bun\u0199asa harkar kiwo a fa\u0257in jihar. Kwamishinan Harkokin Kiwon Dabbobi na jihar, Farfesa Abdulrahman Salim ne ya bayyana hakan ga manema labarai bayan kare kasafin ku\u0257in da ma\u2019aikatarsa ta gabatar na shekarar\u00a0 2026 a gaban Kwamitin Majalisar Dokokin Jihar Jigawa [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":7870,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1],"tags":[],"class_list":["post-7869","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/12\/IMG-20251215-WA0010.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7869","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=7869"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7869\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":7871,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7869\/revisions\/7871"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/7870"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=7869"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=7869"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=7869"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}