{"id":781,"date":"2024-04-01T07:41:25","date_gmt":"2024-04-01T07:41:25","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=781"},"modified":"2024-04-01T07:41:25","modified_gmt":"2024-04-01T07:41:25","slug":"ramadan-gidauniyar-dangote-ta-raba-buhunan-shinkafa-miliyan-%c9%97aya-a-bana","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/ramadan-gidauniyar-dangote-ta-raba-buhunan-shinkafa-miliyan-%c9%97aya-a-bana\/","title":{"rendered":"Ramadan: Gidauniyar Dangote Ta Raba Buhunan Shinkafa Miliyan \u018aaya A Bana"},"content":{"rendered":"<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-782\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/04\/images-1-300x199.webp\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"199\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/04\/images-1-300x199.webp 300w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/04\/images-1.webp 681w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/p>\n<p>Attajirin Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ta hannun Gidauniyar Aliko Dangote, ya \u0199addamar da rabon abinci kyauta ga al\u2019ummar Musulmi su dubu 10 a Jihar Kano, jiharsa ta asali.<\/p>\n<div id=\"pw_22894_instream_1\" class=\"adsbyvli\" data-ad-slot=\"pw_22894\" data-id=\"pw_22894_instream_1\">\n<p>Har ila yau gidauniyar ta kara yawan abincin da take ciyarwa ta hanyar raba buhunan shinkafa miliyan \u0257aya da ku\u0257insa ya haura Naira biliyan 13 a jihohi 36 da Abuja domin rage halin matsin yunwa da al\u2019umma ke fama da shi a kasar nan.<\/p>\n<p>Manufar wannan aiki shi ne a saukaka wa miliyoyin \u2019yan Nijeriya wahalhalun da suke ciki da kuma \u0199alubalen tattalin arziki da ake fama da shi.<\/p>\n<p>Baya ga raba burodi dubu 20 da ake yi kullum ga mazauna birnin Kano da dubu 15 ga mazauna Legas, wannan ciyarwa ta abincin da aka fara tun lokacin cutar Kwarona a 2020 ta dore har zuwa yanzu.<\/p>\n<div id=\"div-gpt-ad-1669908508424-0\" data-google-query-id=\"CN_w8pDAoIUDFaUAVQgdqb0ODQ\">\n<div id=\"google_ads_iframe_\/113471580\/aminiya.com_inarticle-1_0__container__\">\n<p>Abincin da ake dafawa ana rabawa sun ha\u0257a da shinkafa dafa-duka, shinkafa da miya, dafa dukan taliya, doya, wake da naman kaji da na shanu da robar ruwa ga kowane mutum \u0257aya.<\/p>\n<p>Ana raba \u0199unshin abincin ne a masallatan Juma\u2019a da tituna da gidajen yari da gidajen marayu da sauran wurare a birnin Kano da kewaye.<\/p>\n<p>Wani wanda ya ci gajiyar abincin mai suna Malam Musa Maikatako mazaunin Unguwar Tarauni ya bayyana jin da\u0257insa da wannan karamci, ya ce ya taimaka masa wajen yin bu\u0257a-baki cikin sau\u0199i.<\/p>\n<p>Malam Maikatako, ya ce samun wannan abinci na kyauta zai taimaka wajen rage wa al\u2019umma wahalhalun da suke ciki, wanda in ba don wannan abinci ba, jama\u2019a da dama ba za su iya yin bu\u0257a-baki sai da ruwa kawai, ganin matsalar tattalin arziki da \u2019yan Nijeriya ke fuskanta.<\/p>\n<p>\u201cBa zan iya bayyana irin farin cikin da nake ciki ba, wannan abinci ya taimaka matu\u0199a ga talaka irina, domin mun samu abin da za mu yi bu\u0257a-baki baki da abinci mai kyau.<\/p>\n<p>\u201cNa san mutane da yawa a jihar nan wa\u0257anda za su yi bu\u0257a-baki da ruwa kawai. Don haka wannan abinci ya kawo mana sau\u0199i,\u201d in ji shi.<\/p>\n<p>Malam Musa Maikatako ya yi godiya ga Gidauniyar Dangote bisa wannan karimci, inda ya yi addu\u2019ar Allah Ya \u0199ara masa arziki ya kuma ci gaba da sanya albarka a kasuwancinsa.<\/p>\n<div class=\"google-auto-placed ap_container\"><ins class=\"adsbygoogle adsbygoogle-noablate\" data-ad-format=\"auto\" data-ad-client=\"ca-pub-7943548946436796\" data-adsbygoogle-status=\"done\" data-ad-status=\"unfilled\"><\/p>\n<div id=\"aswift_3_host\">Wata wadda ta ci gajiyar tallafin, Hajiya Inna Tukur, ta bayyana jin da\u0257inta ga rabon abincin, wanda a cewarta Gidauniyar Aliko Dangote ta kawo mata \u0257auki.<\/div>\n<div>\n<p>A cewar Inna, \u201cNa yi farin ciki da na samu abinci mai da\u0257i kuma kyauta a cikin irin wannan hali na wahalhalu da ake ciki. A cikin wannan wahala da muke ciki a ce ka samu abinci irin wannan ai sai godiya.<\/p>\n<p>\u201cBa abin da zan ce sai dai in yi godiya ga Alhaji Aliko Dangote, ina ro\u0199on Allah Ya \u0199ara masa albarka,\u201d in ji Inna.<\/p>\n<p>Baya ga rabon burodi da ake yi a shekara 4, an shafe sama da shekara 30 ana ci gaba da ciyar da mabu\u0199ata a Kano da Gidauniyar Aliko Dangote ke yi.<\/p>\n<p>Ana yin haka ne daga gidan mahaifiyarsa da ke Koki da wuraren girki daban-daban da aka tanada.<\/p>\n<p>Wannan shirin ciyarwa yana ciyar da mazauna Kano dubu 10 a kullum tare da samar da abin karin kumallo da abincin rana da kuma abincin dare, duk wannan aiki mai tarin fa\u2019ida ana gudanar da shi fiye da shekara 30.<\/p>\n<\/div>\n<p><\/ins><\/div>\n<\/div>\n<\/div>\n<\/div>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Attajirin Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ta hannun Gidauniyar Aliko Dangote, ya \u0199addamar da rabon abinci kyauta ga al\u2019ummar Musulmi su dubu 10 a Jihar Kano, jiharsa ta asali. Har ila yau gidauniyar ta kara yawan abincin da take ciyarwa ta hanyar raba buhunan shinkafa miliyan \u0257aya da ku\u0257insa ya haura Naira biliyan 13 a jihohi [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":782,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[5,1,11,9],"tags":[29],"class_list":["post-781","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-kasuwanci","category-labarai","category-labaran-gida","category-tattalin-arziki","tag-saye-da-sanarwa"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/04\/images-1.webp","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/781","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=781"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/781\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":783,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/781\/revisions\/783"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/782"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=781"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=781"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=781"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}