{"id":7776,"date":"2025-12-10T17:09:30","date_gmt":"2025-12-10T17:09:30","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=7776"},"modified":"2025-12-10T17:09:40","modified_gmt":"2025-12-10T17:09:40","slug":"karamar-hukumar-agwara-ta-jinjinawa-gwamnati-bisa-tabbatar-da-tsaron-rayuka-da-dukiyoyin-jamaa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/karamar-hukumar-agwara-ta-jinjinawa-gwamnati-bisa-tabbatar-da-tsaron-rayuka-da-dukiyoyin-jamaa\/","title":{"rendered":"Karamar Hukumar Agwara ta Jinjinawa Gwamnati Bisa Tabbatar da Tsaron Rayuka da Dukiyoyin Jama\u2019a"},"content":{"rendered":"<p><b><em>Daga Aliyu Lawal<\/em>\u00a0<\/b><\/p>\n<p>Karamar Hukumar Agwara da ke Jihar Neja ta ce za ta ci gaba da hada kai da Gwamnatin Tarayya ta Jiha Neja wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama\u2019arta, musamman masu rauni.<\/p>\n<p>Shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Iliyasu Zakari, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya rattaba hannu da kansa, wadda ya rabawa manema labarai a Minna, babban birnin jihar Neja.<\/p>\n<p>Alhaji Iliyasu Zakari, wanda ya jaddada cewa kare rayuka da dukiyoyin jama\u2019a shi ne ginshikin mulkinsa, ya kuma yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaro (NSA) Nuhu Ribadu, hukumomin tsaro da Gwamna Mohammed Umar Bago bisa rawar da suka taka wajen tabbatar da sakin dalibai \u0257ari da aka sace a makarantar Cocin Saint Mary\u2019s Catholic da ke Papiri.<\/p>\n<p>Alhaji Iliyasu Zakari ya ce: <em>\u201cMuna matu\u0199ar godiya ga Shugaba Tinubu, Gwamna Umar Bago, Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaro, Nuhu Ribadu, da jaruman jami\u2019an tsaro bisa jajircewarsu wajen kare lafiyar \u2019ya\u2019yanmu.\u201d<\/em><\/p>\n<p>Shugaban ya kuma yi kira da a ci gaba da yin addu\u2019a da bayar da goyon baya ga hukumomi domin tabbatar da dawowar sauran \u0257alibai da malamai da har yanzu ba a same su ba, yana mai cewa: <em>\u201cMuna da yakinin cewa, da irin wannan ha\u0257in kai da kula da tsaro, sauran yara da malamansu za su dawo cikin iyalansu ba da jimawa ba.\u201d<\/em><\/p>\n<p>Sai dai Alhaji Iliyasu Zakari ya yi kira ga iyaye, al\u2019ummar Neja da \u2019yan Najeriya gaba \u0257aya da su kwantar da hankalinsu domin Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Neja na aiki tare da hukumomin tsaro wajen tabbatar da sakin sauran \u0257alibai da malamai da ke tsare a hannun masu garkuwa da mutane.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Aliyu Lawal\u00a0 Karamar Hukumar Agwara da ke Jihar Neja ta ce za ta ci gaba da hada kai da Gwamnatin Tarayya ta Jiha Neja wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama\u2019arta, musamman masu rauni. Shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Iliyasu Zakari, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya rattaba hannu da kansa, [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":7777,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,8],"tags":[1852,836,23],"class_list":["post-7776","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-tsaro","tag-agwara","tag-neja","tag-tsaro"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/12\/IMG-20251210-WA0019.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7776","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=7776"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7776\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":7778,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7776\/revisions\/7778"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/7777"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=7776"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=7776"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=7776"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}