{"id":7732,"date":"2025-12-08T18:51:24","date_gmt":"2025-12-08T18:51:24","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=7732"},"modified":"2025-12-08T18:52:23","modified_gmt":"2025-12-08T18:52:23","slug":"asuu-ssu-ta-zargi-vc-da-karydokokin-jamiar-jihar-sakkwato","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/asuu-ssu-ta-zargi-vc-da-karydokokin-jamiar-jihar-sakkwato\/","title":{"rendered":"ASUU-SSU Ta Zargi VC Da Kary Dokokin Jami\u2019ar Jihar Sakkwato"},"content":{"rendered":"<p>\u0198ungiyar Malaman Jami\u2019o\u2019i ta Nijeriya (ASUU), reshen Jami\u2019ar Jihar Sakkwato (ASUU-SSU), ta zargi Mataimakin Shugaban Jami\u2019ar (Vice-Chancellor) da kin bin umarnin Gwamnan Jihar Sakkwato game da sauke Bursar da ya kai lokacin ritaya.<\/p>\n<p>A cikin wata sanarwa da ta fitar a Sakkwato a ranar Litinin, 8 ga Disamba 2025, \u0199ungiyar ta ce Gwamna Dr. Ahmed Aliyu Sakkwato, wanda shi ne Visitor na Jami\u2019ar, ya amince da bu\u0199atarsu na tabbatar da bin dokokin Jami\u2019ar ta hanyar amincewa da ritayar Bursar \u0257in.<\/p>\n<p>ASUU-SSU ta bayyana cewa Ofishin Shugaban Ma\u2019aikatan Gwamnatin Jihar Sakkwato ya aika da takardar umarni mai lamba HS\/ADM\/101\/VOL-1, \u0257auke da kwanan wata 18 ga Nuwamba 2025, wadda ta umurci Bursar ya mi\u0199a ragamar ofis ga jami\u2019in da ya fi kowa girma a sashen Bursary, har sai an na\u0257a sabon Bursar bisa tanadin dokar Jami\u2019ar Jihar Sakkwato ta 2009.<\/p>\n<p>Sai dai \u0199ungiyar ta ce kusan wata guda ke nan VC \u0257in bai aiwatar da umarnin ba.<\/p>\n<p>Shugaban reshen ASUU-SSU, Kwamared Bello Musa, ya bayyana cewa sun rubuta wa VC takardar tunatarwa da wata takarda ta biyu, amma ba su samu amsa ba.<\/p>\n<p>Haka kuma, sun gudanar da taro biyu da shi, amma ya dage cewa akwai wata amincewa da Ma\u2019aikatar Ilimi Mai Zurfi ta jihar ta bayar a 2024 game da matsayin Bursar.<\/p>\n<p>Sai dai ASUU ta ce wannan hujja \u201cba ta da tushe\u201d, domin sabon umarnin Gwamna \u201cya fi \u0199arfi kuma ya shafe duk wani tsohon matsayi\u201d, musamman ma ganin cewa Bursar ya kai lokacin ritaya tun 3 ga Oktoba 2024.<\/p>\n<p>A cewarta, Ma&#8217;aikatar Kula Da Ma&#8217;aikata ta riga ta aika masa da takardar ritaya ta hannun Ma\u2019aikatar Kudi ta jihar.<\/p>\n<p>\u0198ungiyar ta ce ci gaba da bari tsohon ma\u2019aikaci ya ratta\u0253a hannu kan muhimman takardun Jami\u2019a \u201cna karya doka, kuma na tauye ikon Jami\u2019a (University Autonomy).\u201d<\/p>\n<p>ASUU-SSU ta yaba wa Gwamnan jihar bisa \u201c\u0199arin nuna biyayya ga doka da bu\u0257e \u0199ofar sauraron \u0199orafe-\u0199orafe\u201d, tare da bu\u0199atar ya tabbatar da cewa ba a katse hanyoyin isar da sahihan koke-koke zuwa gare shi ba.<\/p>\n<p>\u0198ungiyar ta ce zanga-zangar lumana da ta gudanar a Jami\u2019ar na nufin matsa wa VC lamba ya aiwatar da umarnin Gwamna ba tare da \u0253ata lokaci ba, domin tabbatar da zaman lafiya da daidaiton aiki.<\/p>\n<p>Ta kuma sha alwashin \u0257aukar \u201cmataki mafi tsauri\u201d idan ba a aiwatar da umarnin ba.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>\u0198ungiyar Malaman Jami\u2019o\u2019i ta Nijeriya (ASUU), reshen Jami\u2019ar Jihar Sakkwato (ASUU-SSU), ta zargi Mataimakin Shugaban Jami\u2019ar (Vice-Chancellor) da kin bin umarnin Gwamnan Jihar Sakkwato game da sauke Bursar da ya kai lokacin ritaya. A cikin wata sanarwa da ta fitar a Sakkwato a ranar Litinin, 8 ga Disamba 2025, \u0199ungiyar ta ce Gwamna Dr. Ahmed [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":7733,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[1843],"class_list":["post-7732","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-asuu-ssu"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/12\/images-49.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7732","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=7732"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7732\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":7735,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7732\/revisions\/7735"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/7733"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=7732"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=7732"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=7732"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}