{"id":7726,"date":"2025-12-08T19:07:51","date_gmt":"2025-12-08T19:07:51","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=7726"},"modified":"2025-12-08T19:07:51","modified_gmt":"2025-12-08T19:07:51","slug":"zaben-2027-nnpp-ta-sha-alwashin-maye-gurbin-tinubu-da-radda","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/zaben-2027-nnpp-ta-sha-alwashin-maye-gurbin-tinubu-da-radda\/","title":{"rendered":"Zaben 2027: NNPP Ta Sha Alwashin Maye Gurbin Tinubu da Radda"},"content":{"rendered":"<p style=\"text-align: left\"><strong><em>Daga Isma\u2019il Adamu<\/em><\/strong><\/p>\n<p>Jam\u2019iyyar NNPP ta bayyana cewa tana da kwarin gwiwar lashe karin mukaman siyasa a zaben shekarar 2027, ciki har da na shugaba kasa da gwamnan Jihar Katsina.<\/p>\n<p style=\"text-align: left\">Sabon shugaban jam\u2019iyyar da aka rantsar a Jihar Katsina, Alhaji Armaya\u2019u AbdulKadir ne ya bayyana haka a zaben shugabannin jam\u2019iyyar da aka gudanar a Katsina.<\/p>\n<p style=\"text-align: left\">Ya ce jam\u2019iyyar, wacce ta ba da muhimmanci ga ilimi, walwalar jama\u2019a, karfafa matasa da ci gaban abubuwan more rayuwa, ta kara samun farin jini a wajen jama\u2019a saboda ingantaccen jagoranci da wakilcin da take bayarwa ta hannun mambobinta da ke rike da\u00a0 mukamai a matakin kananan hukumomi, jihohi da tarayya.<\/p>\n<p style=\"text-align: left\">\u201c<em>Masu zabe sun ga abin da jam\u2019iyyarmu ke aiwatarwa. \u2018Yan majalisa da sauran wadanda aka zaba suna aiki a matakai daban-daban tun daga kananan hukumomi har zuwa matakin tarayya. \u2018Yan Najeriya sun shaida kwarjininmu, shi ya sa muke da tabbacin lashe karin kujeru a zaben 2027<\/em>.<\/p>\n<p style=\"text-align: left\">\u201c<em>Jagoranmu na kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya kuduri aniyar karbar shugabancin kasa, yayin da a nan Jihar Katsina kuma muke shirin tsayar da kwararru masu kwarewa da kuzari da za su iya lashe kujerar Gwamna da sauran mukaman zabe<\/em>.\u201d<\/p>\n<p style=\"text-align: left\">AbdulKadir, wanda ya jaddada cewa NNPP na kara samun karbuwa a tsakanin \u2018yan Najeriya, ya ce hakan ya nuna a kwanan nan ta hanyar sauya sheka da wasu \u2018yan wasu jam\u2019iyyu suka yi zuwa NNPP. Ya kuma bukaci mambobin jam\u2019iyyar da su kara samun magoya baya domin tunkarar zaben 2027.<\/p>\n<p style=\"text-align: left\">Zaben shugabannin jihar, wanda ya samar da mambobi 38 ta hanyar maslaha, ya samu kulawar INEC da hukumomin tsaro, tare da halartar wakilan jam\u2019iyyar daga kasa da yankin Arewa maso Yamma, da kuma daruruwan mambobin jam\u2019iyyar.<\/p>\n<p style=\"text-align: left\">Alhaji Armaya\u2019u AbdulKadir ya\u00a0 kasance Shugaban jam\u2019iyya, Sani Arga mataimaki na farko, Tijjani Zakari sakatare, Umar Musa sakataren shirya ayyuka, sannan Hauwa Abubakar ta zama shugabar mata.<\/p>\n<p style=\"text-align: left\">Tunda farko, shugaban kwamitin gudanar da taron, Alhaji Muhammad Yusuf-Fagge, ya yaba wa wakilai da mambobin jam\u2019iyyar a jihar bisa ladabi da natsuwar da suka nuna a yayin taron, da kuma yadda suka amince da hanyar maslaha wacce \u201cta sau\u0199a\u0199a aikin.\u201d<\/p>\n<p style=\"text-align: left\">Ya yi kira ga mambobin jam\u2019iyyar a jihar da su ci gaba da kasancewa cikin hadin kai, biyayya da ladabi, tare da kara yawaita mambobi da samun goyon baya ga jam\u2019iyyar a jihar.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Isma\u2019il Adamu Jam\u2019iyyar NNPP ta bayyana cewa tana da kwarin gwiwar lashe karin mukaman siyasa a zaben shekarar 2027, ciki har da na shugaba kasa da gwamnan Jihar Katsina. Sabon shugaban jam\u2019iyyar da aka rantsar a Jihar Katsina, Alhaji Armaya\u2019u AbdulKadir ne ya bayyana haka a zaben shugabannin jam\u2019iyyar da aka gudanar a Katsina. [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":7736,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,2],"tags":[145,1844],"class_list":["post-7726","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-siyasa","tag-katsina","tag-nnpp"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/12\/IMG-20251208-WA0021.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7726","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=7726"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7726\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":7737,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7726\/revisions\/7737"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/7736"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=7726"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=7726"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=7726"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}