{"id":7679,"date":"2025-12-06T09:40:17","date_gmt":"2025-12-06T09:40:17","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=7679"},"modified":"2025-12-06T09:40:17","modified_gmt":"2025-12-06T09:40:17","slug":"amurka-ta-fa%c9%97a%c9%97a-jerin-%c6%99asashen-afrika-da-ta-sanya-wa-takunkumin-visa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/amurka-ta-fa%c9%97a%c9%97a-jerin-%c6%99asashen-afrika-da-ta-sanya-wa-takunkumin-visa\/","title":{"rendered":"Amurka ta Fa\u0257a\u0257a Jerin \u0199asashen Afrika Da ta Sanya wa Takunkumin Visa"},"content":{"rendered":"<p>Amurka ta fa\u0257a\u0257a yawan \u0199asashen da ta sanyawa haramcin samun bizar shiga \u0199asar zuwa 32 \u0199ar\u0199ashin jagorancin Donald Trump da ke tsaurara matakan shiga wannan \u0199asa ta yammacin duniya saboda abin da ya kira barazanar \u0199asashen ga tsaron Washington da kuma kange kwararar \u01b4an cirani.<\/p>\n<p>Sakatariyar tsaron cikin gida ta Amurka Kristi Noem yayin wasu kalamanta a shirin kai tsaye ta gidan talabijin, ta ce dole ne Amurka ta dakatar da bizar ga duk wata \u0199asa da ke turo mata baragurbi wa\u0257anda ke wargaza tsaro da zaman lafiyarta.<\/p>\n<p>Duk da cewa Noem bata bayyana sunayen \u0199asashen ba, amma wasu bayanai da suka fita daga ma\u2019aikatar sirrin \u0199asar sun ce galibinsu \u0199asashe ne na Afrika ciki kuwa har da Kenya da Angola da Masar da Habasha da Ivory Coast sai kuma Najeriya a gaba-gaba.<\/p>\n<p>Wasu majiyoyi sun ce, daga cikin dalilan da ya sanya Amurka saka haramcin visa kan \u0199asashen har da yadda wasunsu suka \u0199i amincewa da kar\u0253ar \u01b4anciranin da Washington ke tisa \u0199eyarsu, sai kuma batutuwa masu ala\u0199a da rashin isassun takardun shaida daga \u01b4an \u0199asashen kana rashin inganci fasfo.<\/p>\n<p>A cewar Noem yanzu haka ana ci gaba da tantance wa\u0257annan \u0199asashe don fitar da jerinsu, matakin da ke zuwa bayan tun a ranar 28 ga watan Nuwamban da ya gabata shugaba Trump ya sanya haramci visa kan mutanen da ke shigowa Amurkan daga \u0199asashe matalauta ko masu fama da ya\u0199i.<\/p>\n<p>Matakin na Amurka na zuwa bayan harin ranar 26 ga watan na jiya, da ya kai ga kisan wani Soja guda, harin da ake zargin wani \u0257an \u0199asar Afghanistan da kaiwa wanda aka ce ya shiga Amurkan don neman mafaka a shekarar 2021.<\/p>\n<p>Ko a watan Yuni Amurka ta sanya haramcin visa kan \u0199asashen Chadi da Congo da Equatorial Guinea da kuma Eritrea baya ga Libya da Somalia da kuma Sudan.<\/p>\n<p>A wani mataki na daban kuma gwamnatin ta Amurka ta bu\u0199aci tsauri kan matafiyan da ke shiga \u0199asar daga Burundi da Saliyo da kuma Togo.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Amurka ta fa\u0257a\u0257a yawan \u0199asashen da ta sanyawa haramcin samun bizar shiga \u0199asar zuwa 32 \u0199ar\u0199ashin jagorancin Donald Trump da ke tsaurara matakan shiga wannan \u0199asa ta yammacin duniya saboda abin da ya kira barazanar \u0199asashen ga tsaron Washington da kuma kange kwararar \u01b4an cirani. Sakatariyar tsaron cikin gida ta Amurka Kristi Noem yayin wasu [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":18,"featured_media":7681,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,12],"tags":[1756,204,1825,1826,1737,1827,843],"class_list":["post-7679","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-ketare","tag-afrika","tag-amurka","tag-faaa","tag-asashe","tag-sanya","tag-takunkumi","tag-visa"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/12\/FB_IMG_1765013965585.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7679","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/18"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=7679"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7679\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":7680,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7679\/revisions\/7680"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/7681"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=7679"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=7679"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=7679"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}