{"id":7665,"date":"2025-12-06T08:28:48","date_gmt":"2025-12-06T08:28:48","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=7665"},"modified":"2025-12-06T08:28:48","modified_gmt":"2025-12-06T08:28:48","slug":"dorinar-ruwa-ta-yi-ajalin-mutane-biyu-ta-raunata-shida-a-gombe","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/dorinar-ruwa-ta-yi-ajalin-mutane-biyu-ta-raunata-shida-a-gombe\/","title":{"rendered":"Dorinar Ruwa ta Yi Ajalin Mutane Biyu, ta Raunata Shida a Gombe"},"content":{"rendered":"<p>Mutanen garin Dadin-Kowa da ke \u0198aramar Hukumar Yamaltu Deba a Jihar Gombe, sun shiga damuwa kan yadda wata Dorinar ruwa ta addabi yankin, ta hanyar kashe mutane da kuma lalata gonaki.<\/p>\n<p>Cikin watanni biyu, Dorinar ta kashe mutum biyu, ta karya wasu biyu, sannan ta jikkata wasu hu\u0257u, wa\u0257anda yawanci manoma da masunta ne a Dam \u0257in Dadin-Kowa.<\/p>\n<p>Matsalar ta sa \u0257an Majalisar Tarayya na Yamaltu Deba, Inuwa Garba, ya kai koke gaban Majalisar Wakilai, inda ya nemi gwamnati ta hanzarta kawo wa mazauna yankin \u0257auki.<\/p>\n<p>Ya ce, \u201cTa\u2019addancin Dorinar ya yi yawa. Idan ba a taimaka mana ba, za ta ci gaba da kashe mutane da lalata amfanin gona.\u201d<\/p>\n<p>A makon da ya gabata, Dorinar ta farmaki wani matashi mai suna Sama\u2019ila Garba (Mai Lasa), bayan ya fa\u0257a cikin ruwa.<\/p>\n<p>Shaidu, sun ce dabbar ta yi \u0199o\u0199arin kashe matashin, ta yadda hanjin cikinsa sai da ya fito, kafin a ceto shi.<\/p>\n<p>Garba Zafi, \u0257an uwansa, ya ce Sama\u2019ila ya je bakin ruwa ne kawai sai ya ji ya fa\u0257a, daga nan Dorinar ta afka masa.<\/p>\n<p>Wani mazaunin garin, Akilu Gyara Sa\u2019a, ya ro\u0199i gwamnati ta kai musu agaji duba da yadda rayuwar mutane ke da muhimmanci.<\/p>\n<p>Ya ce: \u201cDorinar tana lalata gonaki, tana kashe mutane. Gwamnati ta hanzarta magance matsalar kafin abin ya ta\u2019azzara.\u201d<\/p>\n<p>Da aka tuntu\u0253i kakakin rundunar \u2019yan sandan jihar, DSP Buhari Abdullahi, ya ce zai bincika domin samun cikakken bayani kan lamarin.<\/p>\n<p>Ya zuwa lokacin ha\u0257a wannan rahoto bai yi \u0199arin haske kan lamarin ba.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Mutanen garin Dadin-Kowa da ke \u0198aramar Hukumar Yamaltu Deba a Jihar Gombe, sun shiga damuwa kan yadda wata Dorinar ruwa ta addabi yankin, ta hanyar kashe mutane da kuma lalata gonaki. Cikin watanni biyu, Dorinar ta kashe mutum biyu, ta karya wasu biyu, sannan ta jikkata wasu hu\u0257u, wa\u0257anda yawanci manoma da masunta ne a [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":18,"featured_media":7667,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[1818,1820,1817,964,347,1819],"class_list":["post-7665","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-ajali","tag-dadin-kowa","tag-dorinar-ruwa","tag-gombe","tag-mutane","tag-raunata"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/12\/FB_IMG_1765009691397.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7665","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/18"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=7665"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7665\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":7666,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7665\/revisions\/7666"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/7667"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=7665"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=7665"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=7665"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}