{"id":7625,"date":"2025-12-02T15:41:03","date_gmt":"2025-12-02T15:41:03","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=7625"},"modified":"2025-12-02T15:41:03","modified_gmt":"2025-12-02T15:41:03","slug":"shugaba-tinubu-ya-nada-janar-christopher-musa-sabon-ministan-tsaro","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/shugaba-tinubu-ya-nada-janar-christopher-musa-sabon-ministan-tsaro\/","title":{"rendered":"Shugaba Tinubu Ya Nada Janar Christopher Musa Sabon Ministan Tsaro"},"content":{"rendered":"<p><strong><em>Daga Bello Wakili<\/em><\/strong><\/p>\n<p>Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Janar Christopher Gwabin Musa a matsayin sabon Ministan Tsaro.<\/p>\n<p>A wata wasika da ya aike wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, Shugaba Tinubu ya mika sunan Janar Musa domin ya maye gurbin Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, wanda ya yi murabus a ranar Litinin.<\/p>\n<p>Janar Musa, mai shekaru 58, wanda zai cika 59 a ranar 25 ga Disamba, jajirtaccen soja ne da ya jagoranci rundunonin tsaro a matsayin Shugaban Hafsoshin Tsaro daga 2023 zuwa watan Oktoban 2025.<\/p>\n<p>An haifi Janar Musa a Sakkwato a 1967, inda ya yi makarantar firamare da sakandare kafin ya tafi College of Advanced Studies a Zariya. Ya kammala a 1986 sannan ya shiga Kwalejin Horas da matsakaitan Sojoji (NDA) duk dai a wannan shekarar, inda ya samu digiri na daya a fannin kimiyya a 1991.<\/p>\n<p>An daga Janar Musa zuwa matsayin babban Laftanar\u00a0 (Second Lieutenant) a 1991, kuma tun daga lokacin ya yi aiki a manyan mukamai iri-iri. Daga cikin mukamansa akwai: Babban Jami\u2019in Ma\u2019aikata a bangaren Horaswa da Ayyuka a Hedikwatar Runduna ta 81;<br \/>\nKwamandan Bataliya ta 73;<br \/>\nMataimakin Darakta, Kayayyakin Aiki, Sashen Tsare-tsaren Rundunar Soja;<br \/>\nWakilin Sojin Kasa a Kwamitin Horaswa na Hedikwatar Soji ta Najeriya.<\/p>\n<p>A 2019, ya yi aiki a matsayin Mataimakin Babban Jami\u2019in Ma\u2019aikata na Horaswa da Ayyuka a Hedikwatar Cibiyar Sojin Kasa;<br \/>\nKwamandan Sashe na 3 na Rundunar Lafiya Dole; da kuma Kwamandan Sashe na 3 na Rundunar Hadin Gwiwar Kasashen Yankin Tafkin Chadi (Multinational Joint Task Force).<\/p>\n<p>A 2021, an nada shi Kwamandan\u00a0 Operation Hadin Kai, inda daga baya ya zama Kwamandan Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, kafin daga bisani Shugaba Tinubu ya nada shi Shugaban Hafsoshin Tsaro a 2023.<\/p>\n<p>A cikin wasikar da ya aikewa Majalisar Dattawa, Shugaba Tinubu ya bayyana cikakken kwarin gwiwa kan \u0199warewar Janar Musa wajen jagorantar Ma\u2019aikatar Tsaro tare da \u0199ara inganta tsarin tsaron Najeriya.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Bello Wakili Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Janar Christopher Gwabin Musa a matsayin sabon Ministan Tsaro. A wata wasika da ya aike wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, Shugaba Tinubu ya mika sunan Janar Musa domin ya maye gurbin Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, wanda ya yi murabus a ranar Litinin. Janar Musa, [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":7626,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,8],"tags":[888,963,89],"class_list":["post-7625","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-tsaro","tag-ministan-tsaro","tag-nadi","tag-tinubu"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/12\/G7I-bIsXAAA9Lxt.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7625","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=7625"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7625\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":7627,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7625\/revisions\/7627"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/7626"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=7625"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=7625"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=7625"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}