{"id":7612,"date":"2025-12-01T11:45:25","date_gmt":"2025-12-01T11:45:25","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=7612"},"modified":"2025-12-01T11:45:25","modified_gmt":"2025-12-01T11:45:25","slug":"najeriya-ta-kara-%c6%99aimi-wajen-kawar-da-cutar-hiv-nan-da-2030","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/najeriya-ta-kara-%c6%99aimi-wajen-kawar-da-cutar-hiv-nan-da-2030\/","title":{"rendered":"Najeriya Ta Kara \u0198aimi Wajen Kawar da Cutar HIV Nan da 2030"},"content":{"rendered":"<p><strong><em>Daga Bello Wakili\u00a0<\/em><\/strong><\/p>\n<p>Najeriya ta \u0199arfafa \u0199o\u0199arinta na kawar da cutar HIV nan da shekarar 2030, inda Uwargidar Shugaban Kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta yi kira ga \u2019yan Najeriya, shugabanni da jami\u2019an lafiya su ha\u0257a hannu wajen cimma wannan manufa.<\/p>\n<p>Yayin jawabi a bikin ranar Yaki da Cutar AIDS ta Duniya ta 2025 da aka gudanar a Fadar Shugaban \u0198asa, Oluremi Tinubu ta jaddada cewa za a iya kawar da cutar HIV a Najeriya idan aka ci gaba da yin aiki cikin tsari, ha\u0257in kai da kuma samun tallafi.<\/p>\n<p>Ta ce duk da cewa an samu cigaba a fannoni na rigakafi, magani da kulawa, ana bu\u0199atar ci gaba da dagewa domin tabbatar da cewa kowane \u0257an Najeriya na samun kariya.<\/p>\n<p>Ta yi nuni da muhimmancin yaki da wariya, hantara da nuna bambanci, abubuwan da har yanzu ke hana mutane neman taimako.<\/p>\n<p>Ta kuma jaddada aikin da ake yi a matakin \u0199asa na dakile yaduwar cutar daga uwa zuwa jariri, fa\u0257a\u0257a magungunan yara masu dauke da HIV, da dorewar shirye-shiryen al&#8217;amuran da suka shafi cutar ta HIV a cikin gida.<\/p>\n<p>Uwargidar Shugaban \u0198asar ta yabawa Shirin \u0198asa na Ya\u0199i da Cutar AIDS da STDs saboda ci gaban da aka samu, tare da tallafin Global Fund.<\/p>\n<p>Oluremi Tinubu ta lura cewa ko da yake masu tallafawa daga waje na taka muhimmiyar rawa, gwamnatin tarayya ta amince da dala miliyan 200 domin \u0199arfafa shirye-shiryen HIV, tarin fuka da zazzabin cizon sauro.<\/p>\n<p>Ta kuma yaba wa cigaban da Hukumar Kula da\u00a0 Cutar HIV ta Kasa (NACA) ke samu wajen ha\u0257in gwiwa da gwamnatocin jihohi domin tabbatar da dogon tsari da \u0257orewar shirin \u0199asa na dakile cutar ta HIV.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Bello Wakili\u00a0 Najeriya ta \u0199arfafa \u0199o\u0199arinta na kawar da cutar HIV nan da shekarar 2030, inda Uwargidar Shugaban Kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta yi kira ga \u2019yan Najeriya, shugabanni da jami\u2019an lafiya su ha\u0257a hannu wajen cimma wannan manufa. Yayin jawabi a bikin ranar Yaki da Cutar AIDS ta Duniya ta 2025 da aka [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":7613,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,4],"tags":[826,1812],"class_list":["post-7612","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-lafiya","tag-hiv","tag-oluremi-tinubu"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/12\/Oluremi-Tinubu-1.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7612","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=7612"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7612\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":7614,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7612\/revisions\/7614"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/7613"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=7612"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=7612"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=7612"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}