{"id":7598,"date":"2025-11-28T20:41:07","date_gmt":"2025-11-28T20:41:07","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=7598"},"modified":"2025-11-28T20:41:07","modified_gmt":"2025-11-28T20:41:07","slug":"asibitin-kula-da-masu-lalurar-%c6%99wa%c6%99walwa-na-kaduna-na-bun%c6%99asa-ta-fannoni-daban-daban","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/asibitin-kula-da-masu-lalurar-%c6%99wa%c6%99walwa-na-kaduna-na-bun%c6%99asa-ta-fannoni-daban-daban\/","title":{"rendered":"Asibitin Kula Da Masu Lalurar \u0198wa\u0199walwa Na Kaduna Na Bun\u0199asa Ta Fannoni Daban-Daban"},"content":{"rendered":"<p>Asibitin Kula da masu lalurar kwakwalwa da ke Kaduna na Jagorantar Sauye-Sauren Lafiyar \u0199wa\u0199walwa a Arewacin Najeriya \u2014 Farfesa Aishatu Armiya\u2019u Ta Bayyana Muhimman Nasarori a Shugabanci da Ayyuka da Hadin Gwiwa<\/p>\n<p>Shugabar gudanarwa kuma daraktar lafiya ta Asibitin kula da masu lalurar \u0199wa\u0199walwa dake Kaduna, Farfesa Aishatu Yusha\u2019u Armiya\u2019u, ta tabbatar da kudirin asibitin na ci gaba da jagorantar gyaran tsarin kula da lafiyar kwakwalwa a Arewa, inda ta ce an samu gagarumin ci gaba wajen fafutukar manufofi, kara yawan ayyuka, da karfafa hadin gwiwa tsakanin sassa daban-daban a cikin shekaru uku da suka gabata.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-7599\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/11\/IMG-20251128-WA0022-300x138.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"138\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/11\/IMG-20251128-WA0022-300x138.jpg 300w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/11\/IMG-20251128-WA0022-1024x470.jpg 1024w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/11\/IMG-20251128-WA0022-768x352.jpg 768w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/11\/IMG-20251128-WA0022.jpg 1101w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/p>\n<p>Farfesa Armiya\u2019u ta bayyana cewa horon da ta samu a shirye-shiryen shugabancin harkokin lafiya na Africa ya taka muhimmiyar rawa wajen inganta salon shugabancinta da kare muradun lafiyar kwakwalwa, da kuma gina \u0199warewa a fannin.<\/p>\n<p>Ta bayyana shirin a matsayin ginshi\u0199i wajen karfafa mata kwarewar tsara manufofi da aiwatar da gyare-gyaren tsarin lafiya.<\/p>\n<p>Sauya Fasalin Babban Asibitin na kasa dake Kaduna<\/p>\n<p>A matsayinta na shugabar daya daga cikin manyan asibitocin kula da lafiyar kwakwalwa guda goma na tarayyar Najeriya, Farfesa Armiya\u2019u ta jagoranci sauye-sauren da suka mayar da Asibitin Kaduna cibiyar kula da lafiya ta tunani da jiki, bincike, da horas da kwararru a hanya mai dacewa da al\u2019adu.<\/p>\n<p>A karkashin jagorancinta, asibitin ya kafa dimbin yarjejeniyar hadin gwiwa da kungiyoyin cikin gida da na waje don bunkasa lafiyar kwakwalwa ga al\u2019umma.<\/p>\n<p>Daya daga cikin manyan hadin gwiwar ita ce wadda ake yi da Hukumar Rigakafin Shan Miyagun Kwayoyi da Kula da Lafiyar \u0199wa\u0199walwa ta Jihar Kaduna wadda ta taimaka wajen samun ci gaba sosai a bangaren manufofi da ayyuka a jihar.<\/p>\n<p>Manyan Nasarorin Manufofi a Jihar Kaduna<\/p>\n<p>Ta hanyar hadin gwiwa da KADSAMHSA, asibitin ya bada goyon bayan fasaha wajen tsara dokoki da tsarin aiki da ake amfani da su wajen sauya fasalin kula da lafiyar kwakwalwa a fadin jihar. Muhimman nasarorin sun hada da:<\/p>\n<p>Sanya magungunan psychotropic a cikin Jerin Muhimman Magungunan Jihar Kaduna na 2025, wanda zai tabbatar da samunsu a cibiyoyin lafiya na matakin farko da na biyu.<\/p>\n<p>Taimakawa wajen tabbatar da dokar Lafiyar \u0199wa\u0199walwa ta Jihar Kaduna, da amincewa da wata manufa da ke ha\u0257a lafiyar kwakwalwa da cibiyoyin kiwon lafiya na al\u2019umma.<\/p>\n<p>Shirin horaswa da ya kara yawan aikace-aikacensu a fadin jihar, wanda ya bai wa ma\u2019aikatan lafiya 165 horo a manyan asibitoci 15, ciki har da masu kula da samari masu dauke da cutar HIV.<\/p>\n<p>Ta kuma ce asibitin yanzu yana da tsofaffin dalibai 10 na Africa CDC Mental Health Leadership Programme \u2014 wa\u0257anda aka horar a Ibadan, Nairobi, da Cairo \u2014 kuma kowannensu yana jagorantar muhimman ayyukan gyara.<\/p>\n<p>Inganta Walwalar Ma\u2019aikata da Ingancin Ayyuka<\/p>\n<p>Farfesa Armiya\u2019u ta jaddada cewa jin dadin ma\u2019aikata na daga cikin manyan abubuwan fifiko, inda aka kirkiro sababbin shirye-shiryen da ke inganta lafiyar jiki, tunani da zamantakewa.<\/p>\n<p>Wadannan sun hada da makon lafiya na kowane kwata, wasanni, tarukan zamantakewa, da ingantaccen tsarin inshorar lafiya.<\/p>\n<p>Asibitin ya kuma hade kula da lafiyar jiki cikin ayyukan lafiyar kwakwalwa, tare da kyautata muhalli domin karfafawa da rage wariya.<\/p>\n<p>Wadannan matakai sun kai ga samun babban gamsuwa daga marasa lafiya, inda sama da kashi 90 cikin dari suka bayyana jin dadi da kulawar da suka samu.<\/p>\n<p>Fadada Ayyuka Ta Hanyar Karin Hadin Gwiwa<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-7600\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/11\/IMG-20251128-WA0024-300x169.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"169\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/11\/IMG-20251128-WA0024-300x169.jpg 300w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/11\/IMG-20251128-WA0024-1024x577.jpg 1024w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/11\/IMG-20251128-WA0024-768x432.jpg 768w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/11\/IMG-20251128-WA0024.jpg 1101w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/p>\n<p>Asibitin na kara fadada tasirinsa ta hanyar aiki tare da rundunar sojoji, cibiyoyin ilimi, kungiyoyin farar hula, da sauran abokan hulda.<\/p>\n<p>Wadannan hadin gwiwar na taimakawa wajen ba da dama ga karin al\u2019umma su samu kula da lafiyar kwakwalwa a Arewa, tare da karfafa kula da marasa lafiya a cikin al\u2019umma.<\/p>\n<p>Shirye-Shiryen Gaba: Kirkire-Kirkire da Kula da Al\u2019umma<\/p>\n<p>Dangane da makomar asibitin, Farfesa Armiya\u2019u ta bayyana cewa za a kara karfafa tsarin kula da lafiyar kwakwalwa na al\u2019umma, habaka bincike da kirkire-kirkire, fadada amfani da kayan aikin lafiyar kwakwalwa na dijital, da gina karfin ma\u2019aikatan lafiya domin biyan bukatun al\u2019umma da ke ta ci gaba da sauyawa.<\/p>\n<p>Ta jaddada himmar gina tsarin lafiyar kwakwalwa mai tausayi, wanda ba ya takaituwa ga manyan cibiyoyi kawai, kuma ya dace da al\u2019adu \u2014 wanda za a iya yada shi a fadin kasar.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Asibitin Kula da masu lalurar kwakwalwa da ke Kaduna na Jagorantar Sauye-Sauren Lafiyar \u0199wa\u0199walwa a Arewacin Najeriya \u2014 Farfesa Aishatu Armiya\u2019u Ta Bayyana Muhimman Nasarori a Shugabanci da Ayyuka da Hadin Gwiwa Shugabar gudanarwa kuma daraktar lafiya ta Asibitin kula da masu lalurar \u0199wa\u0199walwa dake Kaduna, Farfesa Aishatu Yusha\u2019u Armiya\u2019u, ta tabbatar da kudirin asibitin [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":7601,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[3,1,11],"tags":[1811],"class_list":["post-7598","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-ilimi","category-labarai","category-labaran-gida","tag-asibitin-kaduna"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/11\/IMG-20251128-WA0025.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7598","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=7598"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7598\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":7602,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7598\/revisions\/7602"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/7601"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=7598"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=7598"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=7598"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}