{"id":7577,"date":"2025-11-26T21:31:19","date_gmt":"2025-11-26T21:31:19","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=7577"},"modified":"2025-11-26T21:31:19","modified_gmt":"2025-11-26T21:31:19","slug":"gwamna-radda-ya-sanya-hannu-kan-kasafin-2026-ya-zama-doka","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamna-radda-ya-sanya-hannu-kan-kasafin-2026-ya-zama-doka\/","title":{"rendered":"Gwamna Radda Ya Sanya Hannu Kan Kasafin 2026 Ya Zama Doka"},"content":{"rendered":"<p><b><em>Daga<\/em>\u00a0<em>Isma\u2019il Adamu\u00a0<\/em><\/b><\/p>\n<p>Gwamna Dikko Radda na Jihar Katsina ya sanya hannu kan kudirin kasafin kudin jihar na 2026 na Naira Biliyan 897, makonni uku bayan gabatar da shi a gaban majalisar dokokin jihar.<\/p>\n<p>Yayin rattaba hannu a Fadar Gwamnati da ke Katsina, a gaban &#8216;yan majalisar dokokin jihar, gwamnan ya jinjinawa majalisar bisa gaggawar amincewa da kasafin, tare da tabbatar da cewa za a aiwatar da shi yadda ya dace.<\/p>\n<p>Ya bayyana cewa kashi 82 cikin \u0257ari na kasafin an ware shi ne ga manyon ayyuka(capital expenditure), yayin da kashi 18 cikin \u0257ari aka ware ga ayyukan yau da kullum(recurrent expenditure), rabo wanda ya ce ya fi abin da doka ta baya ta tanada, wadda ke bukatar kada kudaden gudanarwa su haura kashi 30 cikin \u0257ari.<\/p>\n<p>Gwamna Radda, wanda ya bayyana kasafin a matsayin \u201ckasafin jama\u2019a,\u201d ya ce an tsara shi ne daga shawarwarin da aka tattara a tarukan jin ra\u2019ayin jama\u2019a da aka gudanar a fadin kananan hukumomi 34 na jihar.<\/p>\n<p>Yayin da yake jinjinawa &#8216;yan majalisar dokokin jihar bisa kyakkyawar alakar aiki da suke da ita da bangaren zartarwa, gwamnan ya bukaci kwamitocin majalisar su gudanar da aikinsu na sa ido don tabbatar da cewa an aiwatar da kasafin yadda ya kamata.<\/p>\n<p>Tun da farko, yayin mika kudirin kasafin domin rattaba hannu, Shugaban Majalisar Dokokin Jihar, Alhaji Nasir Yahaya, ya ce &#8216;yan majalisar sun duba tare da amince da kasafin cikin makonni uku, lamarin da ya sanya Katsina ta zama jihar farko da ta samu dokar kasafin kudin shekara ta 2026.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga\u00a0Isma\u2019il Adamu\u00a0 Gwamna Dikko Radda na Jihar Katsina ya sanya hannu kan kudirin kasafin kudin jihar na 2026 na Naira Biliyan 897, makonni uku bayan gabatar da shi a gaban majalisar dokokin jihar. Yayin rattaba hannu a Fadar Gwamnati da ke Katsina, a gaban &#8216;yan majalisar dokokin jihar, gwamnan ya jinjinawa majalisar bisa gaggawar amincewa [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":7578,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[1800,145],"class_list":["post-7577","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-kasafin-2026","tag-katsina"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/11\/IMG-20251126-WA0033.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7577","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=7577"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7577\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":7579,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7577\/revisions\/7579"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/7578"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=7577"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=7577"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=7577"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}