{"id":7569,"date":"2025-11-26T20:38:14","date_gmt":"2025-11-26T20:38:14","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=7569"},"modified":"2025-11-26T20:38:14","modified_gmt":"2025-11-26T20:38:14","slug":"shugaba-tinubu-ya-ayyana-dokar-ta-baci-kan-harkar-tsaro-tare-da-bada-umurnin-daukar-sabbin-jamiai","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/shugaba-tinubu-ya-ayyana-dokar-ta-baci-kan-harkar-tsaro-tare-da-bada-umurnin-daukar-sabbin-jamiai\/","title":{"rendered":"Shugaba Tinubu Ya Ayyana Dokar Ta-baci Kan Harkar Tsaro Tare da Bada Umurnin Daukar Sabbin Jami\u2019ai"},"content":{"rendered":"<p><strong><em>Daga Bello Wakili<\/em><\/strong><\/p>\n<p>Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-baci kan harkar tsaro a duk fadin kasar, sakamakon karuwar kalubalen tsaro da ake fuskanta.<\/p>\n<p>Shugaban ya ce za a dauki sabbin jami\u2019an tsaro nan ba da jimawa ba, wadanda suka hada da na sojiin, \u2018yan sanda da sauran hukumomin tsaro \u2014 domin karfafa matakan tsaron kasa.<\/p>\n<p>A karkashin sabon umarnin, an bai wa Rundunar \u2018Yan Sandan Najeriya ikon daukar karin jami\u2019aaidubu ashirin,\u00a0 wanda hakan zai kawo yawan sabbin\u00a0 jami\u2019an da za a dauka bana zuwa dubu hamsin.<\/p>\n<p>Shugaban kasar ya kuma amince a yi amfani da sansanonin horas da matasa masu yi wa kasa\u00a0 NYSC a matsayin wuraren horaswa na wucin gadi, sakamakon gyare-gyaren da ake yi a makarantun horar da \u2018yan sanda a fadin kasar.<\/p>\n<p>Haka zalika Jami\u2019an da aka cire daga ayyukan tsaron manyan mutane za su samu horo na gaggawa kafin a tura su zuwa yankunan da ke da hadari.<\/p>\n<p>Shugaban ya kuma bai wa Hukumar tsaro ta DSS umarnin gaggauta tura dakaru masu horo na musamman zuwa dazuka domin yaki da \u2018yan ta\u2019adda da \u2018yan bindiga. A don haka, hukumar ta DSS za ta dauki karin ma\u2019aikata don karfafa wannan aiki.<\/p>\n<p>Shugaba Tinubu ya bukaci \u2018yan Najeriya su bada hadin kai ga matakan tsaron da ake dauka.<\/p>\n<p>Ya yaba wa jami\u2019an tsaro bisa ceto daliban Jihar Kebbi 24 da aka yi garkuwa da su, da masu ibada 38 a Jihar Kwara, tare da tabbatar da cewa ana ci gaba da kokarin kubutar da daliban da aka yi garkuwa da su a Jihar Niger da sauran wadanda ke tsare.<\/p>\n<p>Shugaban ya umurci Rundunar Soji ta kara zafafa ayyuka a dukkan yankunan da ake rikici, tare da jaddada muhimmancin ladabi, gaskiya da kin amincewa da cin hanci ko sakaci.<\/p>\n<p>Ya mika ta\u2019aziyya ga iyalan wadanda aka kashe a hare-haren da suka faru a Kebbi, Borno, Zamfara, Niger, Yobe da Kwara, tare da karrama jaruman sojojin da suka rasa rayukansu, ciki har da Birgediya-Janar Musa Uba.<\/p>\n<p>Shugaba Tinubu ya sake tabbatar da goyon bayansa ga jami\u2019an saro na jihohi, tare da kira ga Majalisar Dokoki ta Kasa da ta fara nazarin dokokin da za su bai wa jihohin da ke son kafa \u2018yan sandan jiha damar yin hakan.<\/p>\n<p>Ya shawarci gwamnatocin jihohi su sake duba tsarin kafa makarantun kwana a wuraren da ke da nisa ba tare da wadatattun matakan tsaro ba, sannan ya yi kira ga cibiyoyin addini su kara inganta tsaron wuraren ibada.<\/p>\n<p>Dangane da rikice-rikicen manoma da makiyaya, Shugaban ya bukaci kungiyoyin makiyaya da su rungumi tsarin kiwo na zamani (ranching) tare da yin aiki tare da Gwamnatin Tarayya ta hannun sabuwar Ma\u2019aikatar Raya Kiwo.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Bello Wakili Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-baci kan harkar tsaro a duk fadin kasar, sakamakon karuwar kalubalen tsaro da ake fuskanta. Shugaban ya ce za a dauki sabbin jami\u2019an tsaro nan ba da jimawa ba, wadanda suka hada da na sojiin, \u2018yan sanda da sauran hukumomin tsaro \u2014 domin karfafa [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":1536,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,8],"tags":[1028,1808,89,23],"class_list":["post-7569","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-tsaro","tag-dokar-ta-baci","tag-sabbin-jamiai","tag-tinubu","tag-tsaro"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/Bola-Tinubu-2.png","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7569","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=7569"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7569\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":7570,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7569\/revisions\/7570"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/1536"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=7569"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=7569"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=7569"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}