{"id":7565,"date":"2025-11-26T13:34:59","date_gmt":"2025-11-26T13:34:59","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=7565"},"modified":"2025-11-26T13:34:59","modified_gmt":"2025-11-26T13:34:59","slug":"tabarbarewar-tsaro-na-barazana-ga-siyasar-%c6%99asar-nan-gabanin-za%c9%93en-2027-ado-doguwa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/tabarbarewar-tsaro-na-barazana-ga-siyasar-%c6%99asar-nan-gabanin-za%c9%93en-2027-ado-doguwa\/","title":{"rendered":"Tabarbarewar Tsaro na Barazana ga\u00a0Siyasar \u0198asar Nan Gabanin Za\u0253en 2027-Ado Doguwa"},"content":{"rendered":"<p><strong><em>Daga Salihu Tsibiri<\/em><\/strong><\/p>\n<p>Tsohon shugaban masu rinjaye na Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa, ya bayyana tabarbarewar tsaro da ake fuskanta, wato ta\u2019addanci, garkuwa da mutane da kuma hare-haren \u2019yan bindiga, a matsayin barazana ga\u00a0 siyasar \u0199asar nan gabanin za\u0253en 2027.<\/p>\n<p>Ya yi wannan tsokacin ne a jawabinsa yayin bude zaman taron musamman na yini biyu da Majalisar Wakilai ta shirya kan halin tsaro da \u0199asar ke ciki.<\/p>\n<p>Alhassan Ado Doguwa, wanda ya yaba da ayyukan da hukumomin tsaro ke ci gaba da gudanarwa, ya ce halin da Arewa ke ciki abin takaici ne \u0199warai, la\u2019akari da yawan mutanen da ke hannun masu garkuwa da kuma wa\u0257anda ke rayuwa cikin tsananin rashin tabbas.<\/p>\n<p>Tsohon shugaban ya jaddada cewa duk da cewa su ma gwamnoni suna da alhakin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama\u2019a tare da gwamnatin tarayya, lokaci ya yi da za a duba batun tsaro a matsayin barazana da ba ta da ala\u0199a da jam\u2019iyya, addini ko \u0199abila.<\/p>\n<p>Ya kara da cewa idan matsalar tsaro ta ci gaba da ta\u2019azzara, akwai bukatar a rufe majalisa gaba \u0257aya tare da ayyana dokar ta-baci, har sai an \u0257auki matakin gaggawa don kare \u0199asar daga halin da take ciki.<\/p>\n<p>A nasa bangaren, shugaban kwamitin majalisar kan harkokin \u2019yan sanda, Makki Abubakar Yalleman, ya bayyana tsaro a matsayin alhakin kowa, inda ya yaba wa umarnin shugaban \u0199asa na janye \u2019yan sanda daga wasu manyan mutane domin \u0199ara \u0199arfi a yaki da laifuka a fadin \u0199asar.<\/p>\n<p>Sai dai Makki Yalleman ya yi kira da a samar da isasshen ku\u0257i da na&#8217;urorin zamani domin inganta \u0199warin gwiwa da \u0199warewar rundunar \u2019yan sandan Najeriya a yakin da take yi da ta\u2019addanci, garkuwa da mutane da kuma \u2019yan bindiga.<\/p>\n<p>A nasa bangaren, shugaban marasa rinjaye na majalisar, Kingsley Chinda, ya danganta matsalolin tsaro da ake fuskanta ga gazawar bangarorin gwamnati uku wajen tabbatar da bin tanade-tanaden kundin tsarin mulki, musamman kan ta\u2019addanci, garkuwa da mutane, \u2019yan bindiga da kuma masu yi wa gwamnati tawaye.<\/p>\n<hr \/>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Salihu Tsibiri Tsohon shugaban masu rinjaye na Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa, ya bayyana tabarbarewar tsaro da ake fuskanta, wato ta\u2019addanci, garkuwa da mutane da kuma hare-haren \u2019yan bindiga, a matsayin barazana ga\u00a0 siyasar \u0199asar nan gabanin za\u0253en 2027. Ya yi wannan tsokacin ne a jawabinsa yayin bude zaman taron musamman na yini biyu [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":7567,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,8],"tags":[163,23],"class_list":["post-7565","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-tsaro","tag-siyasa","tag-tsaro"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/11\/Alhassan-Ado-Doguwa.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7565","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=7565"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7565\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":7568,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7565\/revisions\/7568"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/7567"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=7565"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=7565"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=7565"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}