{"id":7511,"date":"2025-11-22T16:00:06","date_gmt":"2025-11-22T16:00:06","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=7511"},"modified":"2025-11-22T16:00:06","modified_gmt":"2025-11-22T16:00:06","slug":"gwamnatin-neja-ta-rufe-makarantu-saboda-matsalar-tsaro","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamnatin-neja-ta-rufe-makarantu-saboda-matsalar-tsaro\/","title":{"rendered":"Gwamnatin Neja Ta Rufe Makarantu Saboda Matsalar Tsaro"},"content":{"rendered":"<p><strong><em>Daga Aliyu Lawal\u00a0<\/em><\/strong><\/p>\n<p>Gwamnatin Jihar Neja ta bayar da umarnin rufe dukkan makarantun firamare da sakandare na gwamnati da na masu zaman kansu a fadin jihar sakamakon sace dalibai da aka yi a Makarantar St. Mary\u2019s Catholic School da ke Papiri a Karamar Hukumar Agwara.<\/p>\n<p>Gwamna Mohammed Umar Bago ne ya sanar da hakan a Minna bayan wata tattaunawar tsaro gaggawar\u00a0 ta da aka gudanar da shugabannin hukumomin tsaro, malaman addini da sauran masu ruwa da tsaki.<\/p>\n<p>Ya ce matakin ya zama wajibi domin kare rayukan dalibai yayin da ake kara kokarin ceto yaran da aka sace.<\/p>\n<p>Gwamna Bago ya jaddada cewa yanzu lokaci ne na daukar mataki a maimakon zargin juna, inda ya bayar da umarnin cewa a rufe dukkan makarantun mishan, da na Islamiyya da kuma kwalejojin gwamnati na tarayya har sai wani lokaci.<\/p>\n<p>Haka kuma ya umurci a rufe dukkan manyan makarantu da ke yankin Neja ta Arewa da wasu yankuna masu hadari a Neja ta Gabas.<\/p>\n<p>Gwamnan ya bukaci hukumomin tsaro, kungiyoyin fararen huhula, na kwadago da shugabannin addini su mayar da hankali wajen aikin ceto, yana mai tabbatar da kudirin gwamnati na kare rayuka da dukiyoyin al\u2019umma.<\/p>\n<p>Yayin da yake bayyana lamarin a matsayin \u201c<em>abin bakin ciki da takaici<\/em>,\u201d Gwamna Bago ya yi kira ga jama\u2019a da su kwantar da hankalinsu tare da yin addu\u2019a.<\/p>\n<p>Ya ce har yanzu ba a tabbatar da yawan daliban Makarantar St. Mary\u2019s Catholic School da aka sace ba, domin jami\u2019an DSS, Rundunar \u2018Yan Sanda da sauran hukumomin tsaro na kan aiki don tantance sahihin adadin daliban da abin ya shafa.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Aliyu Lawal\u00a0 Gwamnatin Jihar Neja ta bayar da umarnin rufe dukkan makarantun firamare da sakandare na gwamnati da na masu zaman kansu a fadin jihar sakamakon sace dalibai da aka yi a Makarantar St. Mary\u2019s Catholic School da ke Papiri a Karamar Hukumar Agwara. Gwamna Mohammed Umar Bago ne ya sanar da hakan a [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":7512,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[3,1,11,8],"tags":[836,1790],"class_list":["post-7511","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-ilimi","category-labarai","category-labaran-gida","category-tsaro","tag-neja","tag-rufe-makarantu"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/11\/IMG-20251122-WA0035.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7511","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=7511"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7511\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":7513,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7511\/revisions\/7513"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/7512"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=7511"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=7511"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=7511"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}