{"id":7501,"date":"2025-11-22T14:01:20","date_gmt":"2025-11-22T14:01:20","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=7501"},"modified":"2025-11-22T14:01:20","modified_gmt":"2025-11-22T14:01:20","slug":"hukumar-alhazai-ta-jihar-jigawa-za-ta-mayar-da-rarar-kudi-ga-maniyyatan-2026","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/hukumar-alhazai-ta-jihar-jigawa-za-ta-mayar-da-rarar-kudi-ga-maniyyatan-2026\/","title":{"rendered":"Hukumar Alhazai Ta Jihar Jigawa Za Ta Mayar Da Rarar Kudi Ga Maniyyatan 2026"},"content":{"rendered":"<p><strong><em>Daga Usman Muhammad Zaria<\/em><\/strong><\/p>\n<p>Hukumar Jin Da\u0257in Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce ta shirya fara mayar da rarar ku\u0257in ga maniyyata, sakamakon rage kudin kujerun Hajjin 2026 da Hukumar Alhazai ta Kasa, NAHCON, ta sanar.<\/p>\n<p>A cikin wata sanarwa da jami\u2019in hul\u0257a da jama\u2019a na hukumar, Habibu Yusuf Babura, ya rabawa manema labarai, ya ce Daraktan Hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ya bayyana cewa za a mayar da rarar ku\u0257in ne ga maniyyatan da suka kammala biyan kudadensu a fadin jihar kafin a sanar da rage kudaden.<\/p>\n<p>Ahmed Labbo ya ce NAHCON ta bayyana sabon farashin cewa yankin Arewa zai biya sama da Naira Miliyan 7.6, yayin da wa\u0257anda za su tashi daga yankin Kudu za su biya sama da Naira Miliyan 7.9.<\/p>\n<p>A cewarsa, matakin mayar da ku\u0257in umarni ne daga Hukumar Alhazai ta Kasa, sakamakon gagarumin ragin da aka samu.<\/p>\n<p>Saboda haka, ya umarci dukkan shugabannin sassa na hukumar da su fara kar\u0253ar takardun neman mayar da ku\u0257i daga maniyyatan nan take.<\/p>\n<p>&#8220;<em>Muna kira ga dukkan shugabannin sassa da su gaggauta tattara takardun da ake bukata tare da bayanan asusun banki na wadanda za a mayarwa kudaden<\/em>.&#8221;<\/p>\n<p>Daraktan ya bukaci jami\u2019an da su tabbatar ku\u0257in ya isa ga wa\u0257anda suka cancanta ba tare da bata lokaci ba.<\/p>\n<p>Ya ce shirin gudanar da aikin hajjin 2026 ya yi nisa sosai, a jihar da ma a \u0199asar Saudiyya.<\/p>\n<p>Ya kara da cewa hukumar na aiki tukuru don samun mafi kyawun tsari Alhazan jihar, kamar yadda aka saba gudanarwa a baya.<\/p>\n<p>&#8220;<em>Ina kuma kira ga dukkan maniyyata da su tabbatar sun biya kudadensu kafin ranar 24 ga watan Disamba don kaucewa matsaloli ko rasa damar zuwa aikin Hajjin<\/em>.&#8221;<\/p>\n<p>Ahmed Labbo ya yaba wa Gwamna Umar Namadi bisa cikakken goyon baya da jajircewarsa ga hukumar, wanda ya ce ya kasance ginshi\u0199i wajen kula da jin da\u0257i da walwalar alhazai na jihar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Usman Muhammad Zaria Hukumar Jin Da\u0257in Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce ta shirya fara mayar da rarar ku\u0257in ga maniyyata, sakamakon rage kudin kujerun Hajjin 2026 da Hukumar Alhazai ta Kasa, NAHCON, ta sanar. A cikin wata sanarwa da jami\u2019in hul\u0257a da jama\u2019a na hukumar, Habibu Yusuf Babura, ya rabawa manema labarai, ya [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":7502,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[1439,59,1491],"class_list":["post-7501","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-hajjin-2026","tag-jigawa","tag-rarar-kudi"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/11\/IMG-20251122-WA0029.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7501","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=7501"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7501\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":7503,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7501\/revisions\/7503"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/7502"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=7501"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=7501"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=7501"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}