{"id":7476,"date":"2025-11-21T14:35:56","date_gmt":"2025-11-21T14:35:56","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=7476"},"modified":"2025-11-21T14:35:56","modified_gmt":"2025-11-21T14:35:56","slug":"zaman-majalisar-amurka-kan-zargin-kisan-kiristoci-a-najeriya","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/zaman-majalisar-amurka-kan-zargin-kisan-kiristoci-a-najeriya\/","title":{"rendered":"Zaman Majalisar Amurka Kan Zargin Kisan Kiristoci A Najeriya"},"content":{"rendered":"<p class=\"\">\u0198aramin kwamitin majalisar dokokin Amurka kan harkokin kasashen Afirka ya yi wani zama kan batun zargin kisan kiyashin da ake yi wa Kiristoci a Nijeriya da batun yadda Shugaba Donald Trump ya ayyana kasar a matsayin \u201cwadda Amurka ke nuna damuwa a kanta kan walwalar addini,\u201d sai dai kawunan mambobin majalisar sun rarrabu a kan batun na Nijeriya.<\/p>\n<p class=\"\">Zaman, wanda aka yi a Majalisar Dokokin Amurka da ke birnin Washington a ranar Alhamis ya \u0199unshi \u2019yan majalisa da masu kare hakkin dan\u2019adam da kuma wasu kungiyoyin fararen hula.<\/p>\n<p class=\"\">An shafe lokaci ana lugudan la\u0253\u0253a da musayar yawu tsakanin mambobin majalisar da sauran wa\u0257anda suka halarci zaman, wanda aka kuma yada shi kai-tsaye ta intanet.<\/p>\n<p>Masu magana a wajen sun ha\u0257a da Babban Jami\u2019i na Cibiyar Harkokin Amurka Jonathan Pratt da Mataimakin Sakataren Cibiyar Dimokuradiyya, Hakkokin Dan\u2019adam da \u0198wadago, Jacob McGee.<\/p>\n<p>Sai kuma Daraktar Cibiyar \u2018Yancin Addini, Ms Nina Shea; da Bishop Wilfred Anagbe na Cocin Katolika ta Makurdin Nijeriya; da Ms Oge Onubogu ta Cibiyar Dabaru da Karatun Ilimin \u0198asa da \u0198asa, wa\u0257anda suka sha tambayoyi daga \u2018yan majalisar.<\/p>\n<p>Yayin da wasu mambobin suka goyi bayan ayyana Nijeriya a matsayin \u201ckasar da Amurka ke nuna damuwa a kanta kan walwalar addini\u201d da daukar mataki kan Nijeriya lokacin da suke jawabi, akwai wasu daga cikin mambobin majalisar da suka bukaci a sake duba matsayin da Amurkan ta \u0257auka, inda suka ce abubuwan da ke faruwa suna da sar\u0199a\u0199iya kuma suna bukatar a duba su da idon basira.<\/p>\n<p class=\"\">Ko da yake Shugaban Kwamitin, Chris Smith wanda \u0257an jam\u2019iyya mai mulki ta Republican ne kuma yana wakiltar Jihar New Jersey, yayin da yake jawabin bude taron ya bayyana cewa zaman yana da muhimmancin gaske, don Amurka ba za ta zuba ido kan abubuwan da suke faruwa a Nijeriya ba, kuma hakan ne ya sa yake yawan kira kan cewa akwai bukatar a dauki mataki kan \u0199asar.<\/p>\n<p class=\"\">Sai dai wasu \u2019yan majalisar dokokin Amurka ba su goyi bayan matsayin Shugaba Trump kan cewa ana kisan Kiristoci a Nijeriya ba.<\/p>\n<p class=\"\">\u2019Yar majalisar wakilai \u2019yar jam\u2019iyyar adawa ta Democrat Pramila Jayapal ta ce ba ta goyon bayan daukar matakin soji a kan Nijeriya, inda ta bayyana cewa Nijeriya tana da matukar muhimmanci ga Amurka da \u0199asashen Afirka.<\/p>\n<p>Ta ce kashe-kashen da ke faruwa a Nijeriya ba Kiristoci kawai yake shafa ba, inda ta ce ana kashe hatta mabiya sauran addinai a kasar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>\u0198aramin kwamitin majalisar dokokin Amurka kan harkokin kasashen Afirka ya yi wani zama kan batun zargin kisan kiyashin da ake yi wa Kiristoci a Nijeriya da batun yadda Shugaba Donald Trump ya ayyana kasar a matsayin \u201cwadda Amurka ke nuna damuwa a kanta kan walwalar addini,\u201d sai dai kawunan mambobin majalisar sun rarrabu a kan [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":18,"featured_media":7478,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,12],"tags":[204,1134,410,211,20,1425],"class_list":["post-7476","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-ketare","tag-amurka","tag-kiristoci","tag-kisa","tag-majalisa","tag-najeriya","tag-zargi"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/11\/0d613f2f470e519ed6cae2181831b328ad334106885f0e64396aafa1c43dbea7.webp","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7476","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/18"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=7476"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7476\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":7477,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7476\/revisions\/7477"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/7478"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=7476"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=7476"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=7476"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}