{"id":7368,"date":"2025-11-13T09:01:24","date_gmt":"2025-11-13T09:01:24","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=7368"},"modified":"2025-11-13T09:01:24","modified_gmt":"2025-11-13T09:01:24","slug":"gwamna-nasarawa-ya-ce-za-su-samar-da-masanaantu-don-ayyukan-yi","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamna-nasarawa-ya-ce-za-su-samar-da-masanaantu-don-ayyukan-yi\/","title":{"rendered":"Gwamna Nasarawa Ya Ce Za Su Samar da Masana\u2019antu Don Ayyukan Yi"},"content":{"rendered":"<p>Gwamnan Jihar Nasarawa, <strong>Injiniya Abdullahi Sule<\/strong>, ya bayyana cewa hangen nesansa na <strong>\u0199arfafa masana\u2019antu a jihar<\/strong> shi ne domin <strong>\u0199ir\u0199irar ayyukan yi<\/strong> da kuma <strong>inganta rayuwar jama\u2019ar jihar.<\/strong><\/p>\n<p>Gwamnan ya bayyana haka ne a <strong>Fadar Gwamnati ta Lafia<\/strong>, yayin da yake kar\u0253ar bakuncin sabbin shugabannin <strong>\u0198ungiyar \u2018Yan Jarida Masu aiko rahotann dake Jihar (Correspondents\u2019 Chapel).<\/strong><\/p>\n<p>Ya ce baya ga jawo <strong>\u2018yan kasuwa masu saka jari<\/strong> a fannin masana\u2019antu da ma\u2019adinai, gwamnatin sa tana kuma <strong>zuba jari mai yawa a harkar noma.<\/strong><\/p>\n<p>\u201c\u018aaya daga cikin abubuwan da ke ba ni farin ciki shi ne harkar <strong>noman shinkafa<\/strong>. Ka san muna da wata \u0199aramar gona mai girman <strong>hektare 3,300<\/strong> domin noman shinkafa.<\/p>\n<p>Ina alfahari da gonar shinkafar mu domin mun fara girbi, kuma dukkan alamu sun nuna cewa <strong>amfanin gona a wannan kakar ya fi na bara<\/strong>, musamman a yawan amfanin da ake samu a kowace hekta,\u201d in ji shi.<\/p>\n<p>Gwamna Sule ya ce yana da cikakkiyar niyya ta \u0199addamar da <strong>aikace-aikace da shirye-shirye<\/strong> da za su <strong>tabbatar da amfanin kai tsaye ga jama\u2019ar jihar.<\/strong><\/p>\n<p>A cewarsa, \u0257aya daga cikin dalilan da ke haifar da <strong>kalubale da rashin tsaro a arewacin \u0199asar<\/strong>, shi ne <strong>mutane da yawa ba su da abin yi.<\/strong><\/p>\n<p>\u201cKa san wannan shi ne \u0257aya daga cikin abubuwan da ke jawo matsalar tsaro.<\/p>\n<p>A da, lokacin da muke yara, akwai <strong>masana\u2019antar yadi (textile)<\/strong> a Kaduna da \u0199ananan masana\u2019antu a sassa daban-daban na arewa, mutane suna da abin yi.<\/p>\n<p>Ba a cika jin labarin rashin tsaro ba, domin mutane suna zuwa gona, suna yin aikinsu da halaltattun hanyoyi,\u201d in ji gwamnan.<\/p>\n<p>Yayin da yake <strong>taya sabbin shugabannin \u0199ungiyar \u2018yan jarida murna<\/strong> bisa nasarar rantsar da su, Gwamna Sule ya kuma <strong>bukace su su tsaya kan \u0199a\u2019idar aikin jarida<\/strong> ta gaskiya da adalci.<\/p>\n<p>A nasa jawabin, <strong>Shugaban \u0198ungiyar \u2018Yan Jarida na Jihar Nasarawa<\/strong>, Alhaji <strong>Abubakar Abdullahi<\/strong>, ya ce ziyarar ta kasance ne domin <strong>gabatar da sabbin shugabanni ga gwamna<\/strong> da kuma <strong>\u0199arfafa dangantaka<\/strong> tsakanin gwamnati da \u2018yan jarida.<\/p>\n<p>Ya yaba wa Gwamna Sule bisa <strong>aikace-aikacen ci gaba<\/strong> da gwamnatin sa ke aiwatarwa, musamman <strong>gona mai girman hekta 3,300<\/strong> a <strong>Jangwa, karamar hukumar Awe<\/strong>, wadda amfanin shinkafar ta za ta shiga kasuwa a \u0199ar\u0199ashin <strong>sunan alamar jihar \u201cNASACCO Rice.\u201d<\/strong><\/p>\n<p>Ya kuma ambaci wasu muhimman ayyuka da suka ha\u0257a da <strong>gine-ginen gadar sama da \u0199asa a Lafia<\/strong>, ayyukan gadar <strong>Keffi\/Akwanga<\/strong>, <strong>sabuwar cibiyar ma\u2019aikata ta jihar<\/strong>, da kuma <strong>biyan fansho da hakkokin ma\u2019aikata a kan lokaci.<\/strong><\/p>\n<p>\u201cGwamnatinka tana ci gaba da nuna goyon baya ga ci gaban aikin jarida, kuma muna godiya da kyakkyawar dangantaka da muke da ita, tare da fatan za ta ci gaba da dorewa,\u201d in ji shi.<\/p>\n<p>Aliyu Muraki, Lafia.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya bayyana cewa hangen nesansa na \u0199arfafa masana\u2019antu a jihar shi ne domin \u0199ir\u0199irar ayyukan yi da kuma inganta rayuwar jama\u2019ar jihar. Gwamnan ya bayyana haka ne a Fadar Gwamnati ta Lafia, yayin da yake kar\u0253ar bakuncin sabbin shugabannin \u0198ungiyar \u2018Yan Jarida Masu aiko rahotann dake Jihar (Correspondents\u2019 Chapel). [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":7369,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,4],"tags":[1751],"class_list":["post-7368","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-lafiya","tag-xiyara"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/11\/f972d3bc-9f62-474f-9025-90d5ed9d85e1.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7368","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=7368"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7368\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":7370,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7368\/revisions\/7370"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/7369"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=7368"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=7368"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=7368"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}