{"id":7320,"date":"2025-11-12T08:22:13","date_gmt":"2025-11-12T08:22:13","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=7320"},"modified":"2025-11-12T08:22:13","modified_gmt":"2025-11-12T08:22:13","slug":"gwamnatin-tarayya-za-ta-farfado-da-filin-jirgin-sama-na-kano","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamnatin-tarayya-za-ta-farfado-da-filin-jirgin-sama-na-kano\/","title":{"rendered":"Gwamnatin Tarayya Za Ta Farfado Da Filin Jirgin Sama Na Kano"},"content":{"rendered":"<p>Shugaban Hukumar Gudanarwa Filayen Jiragen Sama ta Kasa (FAAN), Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya sake tabbatar da kudirin Gwamnatin Tarayya na dawo da tsohon martabar Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano.<\/p>\n<p>Dakta Ganduje ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar duba aiki da ya kai filin jirgin a Kano.<\/p>\n<p>Ya jagoranci wata tawaga mai \u0199arfi ta jami\u2019an FAAN domin tantance halin da filin jirgin yake ciki yanzu, ciki har da ayyukan da ake gudanarwa da kuma wa\u0257anda aka bari da nufin samar da cikakken tsari na zamani da dorewar ci gaba.<\/p>\n<p>Ya bayyana a matsayin \u0257aya daga cikin tsofaffin filayen jiragen sama masu tarihi a Najeriya da yankin Yammacin Afirka, wanda a da yake \u0257aya daga cikin manyan cibiyoyin tashi da saukar jirage da ke ha\u0257a Najeriya da sauran sassan duniya.<\/p>\n<p>\u201cMun zo ne mu gani da idonmu, tsoffin ayyuka da sababbi, domin mu tsara sabuwar hanya ta farfado da wannan fili tare da dawo da matsayinsa cikin fitattun filayen jiragen sama na yankin,\u201d in ji Ganduje.<\/p>\n<p>Ya jaddada cewa hukumar FAAN za ta tabbatar da inganta jin da\u0257in fasinjoji, kiyaye \u0199a\u2019idodin tsaro, da kuma ha\u0253aka ingancin aiki bisa ka\u2019idodin \u0199asa da \u0199asa.<\/p>\n<p>Dakta Ganduje ya tabbatar da cewa abubuwan da tawagar ta gano a yayin ziyarar za su zama ginshi\u0199i wajen tsara sabuwar manuniya ta dabarun sake farfado da filin domin ya zama abin koyi a harkar gudanar da filayen jiragen sama da kuma abin \u0199arfafa tattalin arzikin Arewa.<\/p>\n<p>Tawagar ta ziyarci sassa daban-daban na filin jirgin, ciki har da zauren sauka da tashin fasinjoji, hanyar tashi da saukar jirage, da kuma rukunin jigilar kaya, domin gano wuraren da ake bukatar gaggawar gyara.<\/p>\n<p><strong>ABDULLAHI JALALUDDEEN, Kano.<\/strong><\/p>\n<p><strong>\u00a0<\/strong><\/p>\n<p><strong>\u00a0<\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Shugaban Hukumar Gudanarwa Filayen Jiragen Sama ta Kasa (FAAN), Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya sake tabbatar da kudirin Gwamnatin Tarayya na dawo da tsohon martabar Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano. Dakta Ganduje ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar duba aiki da ya kai filin jirgin a Kano. Ya jagoranci wata tawaga mai [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":7321,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[5,1,11],"tags":[1740],"class_list":["post-7320","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-kasuwanci","category-labarai","category-labaran-gida","tag-filin-jirgin-kano"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/11\/f26c07a6-d36f-454d-a0eb-c97d770ddb5f.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7320","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=7320"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7320\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":7322,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7320\/revisions\/7322"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/7321"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=7320"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=7320"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=7320"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}