{"id":732,"date":"2024-03-29T09:13:32","date_gmt":"2024-03-29T09:13:32","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=732"},"modified":"2024-03-29T10:10:18","modified_gmt":"2024-03-29T10:10:18","slug":"gwamnan-jihar-kaduna-ya-%c9%97auki-nauyin-karatun-%c9%97aliban-kuriga","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamnan-jihar-kaduna-ya-%c9%97auki-nauyin-karatun-%c9%97aliban-kuriga\/","title":{"rendered":"Gwamnan Jihar Kaduna Ya \u018aauki Nauyin Karatun \u018aaliban Kuriga"},"content":{"rendered":"<p>Gwamna Uba Sani, na jihar Kaduna ya yi alkawarin bai wa \u0257aliban Kuriga 137 da aka kubutar daga hannun \u2019yan bindiga tallafin karatu.<\/p>\n<p>Uba Sani ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga daliban da suka kubuta daga hannun \u2018yan bindiga a gidan gwamnatin jihar a ranar Alhamis.<\/p>\n<p>Gwamnan ya ce gidauniyarsa ta Uba Sani za ta gyara makarantun Kuriga domin bai wa yara a garin damar samun ingantaccen ilimi.<\/p>\n<p>Sani, ya Kara da cewar bayan sako daliban, gwamnatin jihar ta dauki masana ilimin halayyar dan adam aiki wadanda suka shafe lokaci suna tattaunawa da daliban don tabbatar da lafiyarsu.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-738\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/IMG-20240328-WA0016-300x225.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"225\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/IMG-20240328-WA0016-300x225.jpg 300w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/IMG-20240328-WA0016-1024x768.jpg 1024w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/IMG-20240328-WA0016-768x576.jpg 768w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/IMG-20240328-WA0016.jpg 1080w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/p>\n<p>Sai dai ya bayyana cewar \u0257aya daga cikin malaman da aka sace, mai suna Malam Abubakar ya rasa ransa sakamakon matsalar rashin lafiya.<\/p>\n<p>Gwamnan ya ce gwamnatin jihar za ta dauki nauyin karatun \u2019ya\u2019yan malamin da ya rasu, tare da bai wa iyalansa kyautar Naira miliyan 10.<\/p>\n<p>Sani ya ce, \u201cJiya iyayen daliban suka zo nan, sun hadu da yaran, kowa ya yi murna. Ina so na yaba wa yaran. Sun yi hakuri da mu. Sun kuma fahimci halin da suka tsinci kansu a ciki.<\/p>\n<p>\u201cLokacin da suka dawo, mun fahimci wasu na cikin matsanancin hali. Wannan shi ne dalilin da ya sa muka dauko masana ilimin halayyar dan adam, wadanda suka ba su shawarwari. Na yi farin ciki kamar yadda yaran suka yi farin ciki.<\/p>\n<p>\u201cKwana biyu da kubutarsu, sun nuna ba sa son komawa gida, sun so zama da ni a nan na tsawon mako biyu. Amma na sanar da su cewar ba zai yiwu ba dole su koma gida. Iyayensu na muradin ganin su bayan shafe kimanin kwana 17 a hannun \u2018yan bindiga.\u201d<\/p>\n<p>Gwamnan ya kara da cewa, \u201cNa kuma bayar da umarnin yin gyare-gyare a garin da kuma makarantunsu, domin Kuriga na daya daga cikin yankuna mafi zaman lafiya a Kaduna.\u201d<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><strong><em>Aminu Dalhatu<\/em><\/strong><\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamna Uba Sani, na jihar Kaduna ya yi alkawarin bai wa \u0257aliban Kuriga 137 da aka kubutar daga hannun \u2019yan bindiga tallafin karatu. Uba Sani ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga daliban da suka kubuta daga hannun \u2018yan bindiga a gidan gwamnatin jihar a ranar Alhamis. Gwamnan ya ce gidauniyarsa ta [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":18,"featured_media":737,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[3,1,11,8],"tags":[248,249,67,247],"class_list":["post-732","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-ilimi","category-labarai","category-labaran-gida","category-tsaro","tag-dalibai","tag-daukar-nauyi","tag-karatu","tag-kuriga"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/IMG-20240328-WA0012.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/732","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/18"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=732"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/732\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":739,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/732\/revisions\/739"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/737"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=732"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=732"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=732"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}