{"id":7263,"date":"2025-11-09T05:46:06","date_gmt":"2025-11-09T05:46:06","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=7263"},"modified":"2025-11-09T13:52:23","modified_gmt":"2025-11-09T13:52:23","slug":"minista-goronyo-ya-duba-ci-gaban-aikin-titin-abuja-zuwa-kano","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/minista-goronyo-ya-duba-ci-gaban-aikin-titin-abuja-zuwa-kano\/","title":{"rendered":"Minista Goronyo ya Duba Ci Gaban Aikin Titin Abuja Zuwa Kano"},"content":{"rendered":"<p>Ministan Kasa a Ma\u2019aikatar Ayyuka ta Tarayya, Bello Muhammad Goronyo, ya sake jaddada kudirin Gwamnatin Shugaban Kasa Asiwaju Bola Ahmad Tinubu na tabbatar da kammala aikin gyaran titin Abuja zuwa Kaduna har zuwa Kano, da kuma wasu manyan tituna a Arewacin \u0199asar nan.<\/p>\n<p>Ministan, Barrister Bello Goronyo (ESQ), ya bayyana haka ne lokacin da ya kai ziyara don duba yadda aikin ke gudana, domin tabbatar da cewa ana sa idanu sosai, kuma \u2018yan kwangila suna gudanar da aikin cikin inganci da nagarta.<\/p>\n<p>Ministan ya fara duba aikin tun daga Tungan Maje, Madalla, Zuma Resort, Sabon Wuse, Jere, Abuja Junction, Gwanin Gora, sannan ya ci gaba zuwa Zaria har zuwa Kano, inda aikin ke ci gaba yadda ya dace.<\/p>\n<p>Haka kuma, Ministan ya ja kunnen kamfanin da ke gudanar da aikin\u00a0 daInfiouest International Limited da ya tabbatar sun kammala aikin kafin karshen shekarar 2026, kamar yadda Shugaban Kasa ya bayar da umarni.<\/p>\n<p>Barrister Bello Muhammad Goronyo ya bayyana cewa Shugaban Kasa Tinubu na da damuwa matu\u0199a kan wahalar da matafiya ke sha wajen amfani da wannan hanyar, wanda hakan yasa gwamnati ta maida hankali sosai kan aikin.<\/p>\n<p>A cewar Ministan, kamfanonin sun riga sun yi alkawarin kammala aikin a kan lokaci tare da tabbatar da \u0199yakykyawan aiki kamar yadda aka shimfi\u0257a ka\u2019idoji.<\/p>\n<p>Wannan ziyarar duba aikin dai an gudanar da ita ne bisa umarnin Shugaban Kasa ga Ministan Kasa na aikin, Honourable Bello Muhammad Goronyo (ESQ), domin tabbatar da cewa aikin yana tafiya yadda ya kamata ba tare da tangarda ba.<\/p>\n<p>Kaura Namoda\/ Wababe<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Ministan Kasa a Ma\u2019aikatar Ayyuka ta Tarayya, Bello Muhammad Goronyo, ya sake jaddada kudirin Gwamnatin Shugaban Kasa Asiwaju Bola Ahmad Tinubu na tabbatar da kammala aikin gyaran titin Abuja zuwa Kaduna har zuwa Kano, da kuma wasu manyan tituna a Arewacin \u0199asar nan. Ministan, Barrister Bello Goronyo (ESQ), ya bayyana haka ne lokacin da ya [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":7264,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[1731],"class_list":["post-7263","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-gyarantitu"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/11\/IMG-20251109-WA0007.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7263","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=7263"}],"version-history":[{"count":3,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7263\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":7275,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7263\/revisions\/7275"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/7264"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=7263"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=7263"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=7263"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}