{"id":7217,"date":"2025-11-04T14:50:22","date_gmt":"2025-11-04T14:50:22","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=7217"},"modified":"2025-11-04T14:50:22","modified_gmt":"2025-11-04T14:50:22","slug":"kaduna-ta-zama-jihar-farko-a-nijeriya-da-ta-aiwatar-da-shirin-samar-da-abincin-mai-gina-jiki-ga-yara-unicef","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/kaduna-ta-zama-jihar-farko-a-nijeriya-da-ta-aiwatar-da-shirin-samar-da-abincin-mai-gina-jiki-ga-yara-unicef\/","title":{"rendered":"KADUNA TA ZAMA JIHAR FARKO A NIJERIYA DA TA AIWATAR DA SHIRIN SAMAR DA ABINCIN MAI GINA JIKI GA YARA \u2013 UNICEF"},"content":{"rendered":"<p>KADUNA TA ZAMA JIHAR FARKO A NIJERIYA DA TA AIWATAR DA SHIRIN SAMAR DA ABINCIN MAI GINA JIKI GA YARA \u2013 UNICE<\/p>\n<p>Daga Abdullahi Shettima.<\/p>\n<p>Hukumar Asusun kula da yara kananan yara ta majalisar dinkin duniya (UNICEF) ta jinjinawa gwamnatin jihar Kaduna bisa zama jihar farko a Nijeriya da ta amince kuma fara aiwatar da shirin samar da abinci mai gina jiki da lafiya ga yara kanana (RUTF) wanda hakan ya zama wani muhimmin mataki wajen yakar karancin abinci mai gina jiki tsakanin yara.<\/p>\n<p>Da take jawabi yayin wani taron hadin gwiwa da gwamnatin jihar Kaduna, wakiliyar UNICEF a Nijeriya, Wafaa Saeed Abdelatef, ta bayyana yadda jihar Kaduna ta nuna gagarumar jajircewa a bangaren kiwon lafiya tare da samar da walwalar yara da cika alkawuran ku\u0257in ha\u0257in gwiwa akai-akai.<\/p>\n<p>Tace \u201cJihar Kaduna ta zama abin koyi ga sauran jihohi. Yadda gwamnati ta rungumi shirin samar da abinci mai gina jiki da lafiya ( RUTF) da sauri kuma ta fara aiwatar da shi na nuna cikakkiyar niyya wajen kare rayuwar yara da tabbatar da cewa babu wani yaro da zai ci gaba da fama da rashin abinci mai gina jiki,\u201d<\/p>\n<p>Taron wanda aka gudanar da shi a fadar gwamnatin jihar Kaduna, ya zama abin tarihi a dangantakar hadin gwiwar da ke tsakanin UNICEF da gwamnatin jihar Kaduna wajen inganta lafiya da walwalar yara.<\/p>\n<p>Gwamna Uba Sani ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da gina kan wannan nasara, inda ya bayyana shirin RUTF a matsayin wani muhimmin \u0253angare na dabarar gwamnatin sa wajen yakar rashin abinci mai gina jiki da inganta ci gaban jama\u2019a baki \u0257aya.<\/p>\n<p>\u201cKaddamar da rabon abincin RUTF a fadin jihar Kaduna wani babban mataki ne na kawo \u0199arshen cutar karancin abinci mai gina jiki,\u201d<\/p>\n<p>\u201cMun kuduri aniyar cewa babu wani yaro da za a bar shi a baya wajen ya\u0199ar yunwa, rashin lafiya, da kuma samar da makoma mai kyau.\u201d inji gwamna Uba Sani<\/p>\n<p>Gwamnan ya kuma godewa UNICEF bisa wannan ha\u0257in gwiwar da ke samar da sauye-sauye masu amfani a fannoni kamar su lafiya, abinci mai gina jiki, ilimi, da tsaftar ruwa da muhalli.<\/p>\n<p>Ya kara da cewa shiga jihar Kaduna cikin muhimman shirye-shirye irin su RUTF da ASWA III wanda Kaduna ita ka\u0257ai ce ta shiga cikinsa a Nijeriya na nuna hangen nesan gwamnatinsa na gina tsarin da ke tallafa wa marasa \u0199arfi a fadin jihar baki daya.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>KADUNA TA ZAMA JIHAR FARKO A NIJERIYA DA TA AIWATAR DA SHIRIN SAMAR DA ABINCIN MAI GINA JIKI GA YARA \u2013 UNICE Daga Abdullahi Shettima. Hukumar Asusun kula da yara kananan yara ta majalisar dinkin duniya (UNICEF) ta jinjinawa gwamnatin jihar Kaduna bisa zama jihar farko a Nijeriya da ta amince kuma fara aiwatar da [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":7218,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[3,1,11],"tags":[33],"class_list":["post-7217","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-ilimi","category-labarai","category-labaran-gida","tag-kaduna"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/11\/IMG-20251104-WA0053.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7217","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=7217"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7217\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":7219,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7217\/revisions\/7219"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/7218"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=7217"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=7217"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=7217"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}