{"id":7212,"date":"2025-11-04T05:24:37","date_gmt":"2025-11-04T05:24:37","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=7212"},"modified":"2025-11-04T05:24:37","modified_gmt":"2025-11-04T05:24:37","slug":"uba-sani-ya-kaddamar-da-gidaje-100-ga-wa%c9%97anda-rikici-ya-shafa-a-jihar","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/uba-sani-ya-kaddamar-da-gidaje-100-ga-wa%c9%97anda-rikici-ya-shafa-a-jihar\/","title":{"rendered":"Uba Sani Ya Kaddamar Da Gidaje 100 Ga Wa\u0257anda Rikici Ya Shafa A Jihar"},"content":{"rendered":"<p>Gwamnatin Kaduna Da Hadin Gwiwar UINL Da FHFL Sun Gina Gidaje 100 Ga Mutanen Da Rikici Ya Raba Da Muhallans<\/p>\n<p>Daga Abdullahi Shettima<\/p>\n<p>Gwamnatin Jihar Kaduna tare da ha\u0257in gwiwar kamfanin Ummi International Nigeria Ltd (UINL) da Family Homes Funds Ltd (FHFL), bisa tallafin Ma\u2019aikatar Tsare-tsare da Kasafin Ku\u0257i ta Tarayyar Najeriya, sun kammala ginin gidaje 100 domin mutanen da rikici ya raba da muhallansu da kuma marasa galihu a cikin jihar.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-7213\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/11\/IMG-20251104-WA0038-300x170.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"170\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/11\/IMG-20251104-WA0038-300x170.jpg 300w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/11\/IMG-20251104-WA0038-768x435.jpg 768w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/11\/IMG-20251104-WA0038.jpg 900w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/p>\n<p>Wannan aiki ya gudana ne a yankin Rigachikun, inda kamfanin Ummi International Nigeria Ltd ya bayar da fili, yayin da Gwamnatin Kaduna, Family Homes Funds, da Ma\u2019aikatar Kasafi da Tsare-tsare suka \u0257auki nauyin ginin gidajen gaba \u0257aya.<\/p>\n<p>A yayin \u0199addamar da ginin da kuma mi\u0199a ma wa\u0257anda za su zauna, Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana cewa aikin ya samo asali ne daga kudirin gwamnatinsa na taimaka wa wa\u0257anda suka rasa matsuguninsu sakamakon rikice-rikice, tare da dawo musu da martabar rayuwa.<\/p>\n<p>Gwamna Uba Sani ya ce wannan aiki yana cikin shirin gwamnatin jihar na inganta walwalar marasa galihu da tabbatar da ci gaban da ya shafi kowa a fadin jihar.<\/p>\n<p>A nasa jawabin, Ministan Ma\u2019aikatar Tsare-tsare da Kasafin Ku\u0257i, Sanata Atiku Bagudu, ya yabawa wannan ha\u0257in gwiwa tare da tabbatar da cewa ma\u2019aikatar za ta ci gaba da yin aiki tare da kamfanoni masu zaman kansu da kungiyoyin agaji domin cimma burin ci gaba mai \u0257orewa.<\/p>\n<p>Ita kuma tsohuwar Ministar Mata ta Tarayyar Najeriya, Dame Pauline Tallen, ta bayyana ginin a matsayin wani muhimmin aiki na alheri wanda zai taimaka wajen farfa\u0257o da rayuwar zawarawa, marayu da sauran masu bu\u0199ata a cikin al\u2019umma.<\/p>\n<p>A nata bangaren, Dr. Umma Sani (Zinariyar Gabasawar Zazzau), shugabar kamfanin Ummi International Nigeria Ltd, ta bayyana cewa gidauniyarta ta dade tana gudanar da irin wannan aiki na samar da matsuguni ga zawarawa da marayu domin inganta rayuwar su kamar sauran jama\u2019a.<\/p>\n<p>Ta kuma gode wa Gwamna Uba Sani bisa cikakkiyar gudunmawar da ya bayar wajen ganin an samu wannan nasara, tare da bayyana shi a matsayin shugaba mai kishin al\u2019umma da tausayi.<\/p>\n<p>Haka kuma Ambasada Dr. Fatima Mohammed Goni, shugabar Global Business Network Initiative (GBNI), ta bayyana Dr. Umma Sani a matsayin abin koyi ga mata a Najeriya, la\u2019akari da yadda ta ke aiwatar da ayyukan jin kai don tallafa wa mabukata.<\/p>\n<p>Ta kuma yi kira ga wadanda suka amfana da gidajen da su kula da su da kyau, domin tabbatar da dorewar manufar da aka samar da su saboda ta alheri ce ta gaskiya.<\/p>\n<p>Taron \u0199addamarwar ya gudana ne a yau Litinin, inda ya sami halartar manyan baki, jami\u2019an gwamnati, da wakilan kungiyoyi masu zaman kansu daga sassa daban-daban na Jihar Kaduna.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnatin Kaduna Da Hadin Gwiwar UINL Da FHFL Sun Gina Gidaje 100 Ga Mutanen Da Rikici Ya Raba Da Muhallans Daga Abdullahi Shettima Gwamnatin Jihar Kaduna tare da ha\u0257in gwiwar kamfanin Ummi International Nigeria Ltd (UINL) da Family Homes Funds Ltd (FHFL), bisa tallafin Ma\u2019aikatar Tsare-tsare da Kasafin Ku\u0257i ta Tarayyar Najeriya, sun kammala ginin [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":7214,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[1721],"class_list":["post-7212","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-kaddamar-wa"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/11\/IMG-20251104-WA0035.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7212","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=7212"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7212\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":7215,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7212\/revisions\/7215"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/7214"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=7212"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=7212"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=7212"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}