{"id":7180,"date":"2025-11-02T21:52:43","date_gmt":"2025-11-02T21:52:43","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=7180"},"modified":"2025-11-02T22:22:35","modified_gmt":"2025-11-02T22:22:35","slug":"alummar-kauru-sun-koka-game-da-karuwar-hare-hare-da-ke-barazana-ga-gonaki-da-rayuka","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/alummar-kauru-sun-koka-game-da-karuwar-hare-hare-da-ke-barazana-ga-gonaki-da-rayuka\/","title":{"rendered":"Al\u2019ummar Kauru Sun Koka Game Da Karuwar Hare-hare Da Ke Barazana Ga Gonaki Da Rayuka"},"content":{"rendered":"<p><strong><em>Daga Yusuf Zubairu Kauru\u00a0<\/em><\/strong><\/p>\n<p>Al&#8217;ummar Karamar Hukumar Kauru ta Jihar Kaduna sun shiga halin kaka-ni-ka-yi duba da yadda rayukansu ke kasancewa cikin hadari yayin da suke gonakinsu.<\/p>\n<p>A wata tattaunawa ta wayar tarho, wani jagoran matasa, Junaidu Ishaq, ya bayyana cewa kusan shekaru biyar ke nan da hare-haren \u2019yan bindiga ke ta faruwa akai-akai, wanda ya bar al\u2019umma cikin fargaba da \u0199uncin rayuwa.<\/p>\n<p>Ya ce manoma suna shiga gonakinsu ne cike da fargaba domin komi na iya faruwa yayin da suke aiki a gonakin.<\/p>\n<p>Mazauna yankin sun bayyana cewa Kauru, wadda aka fi sani da yawan gonaki da ke taka muhimmiyar rawa wajen samar da abinci a jihar Kaduna, yanzu manoma ba sa iya shiga gonakinsu cikin kwanciyar hankali saboda yadda &#8216;yan bindiga ke yawan kai musu hare-hare.<\/p>\n<p>A koda yaushe iyayen yara suna fargaba kada \u2018ya\u2019yansu su yi nesa da su, yayin da iyalai da dama da ke fama da \u0199angin talauci ke kara shiga cikin matsanancin hali.<\/p>\n<p>Sun yi kira gwamnati da hukumomin tsaro su yi gaggawar kai \u0257auki wanda zai bai wa manoman karkara kwarin gwiwa, wa\u0257anda su ne ginshi\u0199in samar da abinci a yankin.<\/p>\n<p>Mazaunan sun yi gargadin cewa idan ba a \u0257auki mataki cikin gaggawa ba, hare-haren na iya haifar da \u0199aruwar matsalar rashin abinci da yawaitar \u0199aura daga yankin.<\/p>\n<p>\u201c<em>Idan zuwa gona zai sa mutumya rasa ransa, to lalle akwai babban matsala<\/em>,\u201d in ji Junaida Ishaq.<\/p>\n<p>Sun yi fatan cewa za a dawo da zaman lafiya a yankin, yadda \u0199asar da Allah Ya albarkace su da ita za ta ci gaba da ciyar da al\u2019ummar Kauru ba wurin binne su ba.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Yusuf Zubairu Kauru\u00a0 Al&#8217;ummar Karamar Hukumar Kauru ta Jihar Kaduna sun shiga halin kaka-ni-ka-yi duba da yadda rayukansu ke kasancewa cikin hadari yayin da suke gonakinsu. A wata tattaunawa ta wayar tarho, wani jagoran matasa, Junaidu Ishaq, ya bayyana cewa kusan shekaru biyar ke nan da hare-haren \u2019yan bindiga ke ta faruwa akai-akai, wanda [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":7182,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,8],"tags":[33,1424],"class_list":["post-7180","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-tsaro","tag-kaduna","tag-kauru"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/11\/Gunmen-used-to-illustrate-the-story.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7180","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=7180"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7180\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":7184,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7180\/revisions\/7184"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/7182"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=7180"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=7180"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=7180"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}