{"id":7082,"date":"2025-10-24T09:05:09","date_gmt":"2025-10-24T09:05:09","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=7082"},"modified":"2025-10-24T09:05:09","modified_gmt":"2025-10-24T09:05:09","slug":"agile-kano-ta-tattauna-da-malamai-da-limamai-don-%c6%99arfafa-goyon-bayan-ilimin-yan-mata","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/agile-kano-ta-tattauna-da-malamai-da-limamai-don-%c6%99arfafa-goyon-bayan-ilimin-yan-mata\/","title":{"rendered":"AGILE Kano Ta Tattauna da Malamai da Limamai Don \u0198arfafa Goyon Bayan Ilimin \u2019Yan Mata"},"content":{"rendered":"<p>Shirin <strong>karfafa ilimin \u2018ya\u2019ya mata<\/strong> a jihar Kano ya shirya taron tattaunawa da malamai da limaman masallatan Juma\u2019a domin \u0199arfafa ha\u0257in gwiwa da shugabannin addini wajen inganta goyon bayan al\u2019umma ga ilimin \u2019yan mata a fadin jihar.<\/p>\n<p>Taron, wanda yake \u0257aya daga cikin dabarun ha\u0257in kai na masu ruwa da tsaki na AGILE, yana da nufin \u0199ara samun damar karatu, tsayawa da kuma kammala karatun \u2019yan mata ta hanyar daidaita ayyukan shirin da dabi\u2019u da imanin al\u2019umma.<\/p>\n<p>A jawabinsa, <strong>Shugaban Shirin AGILE na Jihar Kano<\/strong>, Malam Mujtapha Aminu, ya bayyana cewa an shirya taron ne domin fayyace wasu rashin fahimta da ake da su game da shirin, da kuma tabbatar da fahimtar juna tsakanin shugabannin addini.<\/p>\n<p>A cewarsa, \u201cShigar malamai da limaman masallatan Juma\u2019a cikin wannan shiri yana da matu\u0199ar muhimmanci domin suna da tasiri wajen gina ra\u2019ayin jama\u2019a. Mun gayyace su ne domin mu wayar da kan su game da manufofi, sassa, da matakan aikin shirin AGILE.\u201d<\/p>\n<p>Malam Mujtapha ya \u0199ara bayyana cewa shirin ya riga ya ha\u0257a kai da shugabannin gargajiya da na addini wajen duba kundin horarwa don tabbatar da cewa yana tafiya da koyarwar addinin Musulunci da kuma dabi\u2019un Hausawa.<\/p>\n<p>Ya ro\u0199i dukkan masu ruwa da tsaki da su ci gaba da ba da goyon baya ga shirin tare da neman bayani a duk lokacin da wani abu ya taso, domin kauce wa rashin fahimta. Ya jaddada cewa, <em>\u201cMalamai sune manyan masu tasiri wajen bun\u0199asa ilimin \u2019yan mata a Kano da Najeriya gaba \u0257aya.\u201d<\/em><\/p>\n<p>A sakon sa na fatan alheri, <strong>Shugaban Majalisar Malamai ta Jihar Kano<\/strong>, Sheikh Ibrahim Khalil, wanda Sakatarensa Sheikh Ibrahim Abubakar Tofa ya wakilta, ya shawarci tawagar AGILE da su tabbatar dukkan sassan shirin suna tafiya da ka\u2019idojin Musulunci da al\u2019adun mutanen Kano, domin jihar na da tsarin rayuwa mai zurfi da al\u2019adu masu \u0199arfi.<\/p>\n<p>Ya ce, <em>\u201cA matsayarmu na manyan masu ruwa da tsaki, muna da muhimmiyar rawa wajen tallafa wa ilimin \u2019yan mata domin Musulunci yana \u0199arfafa neman ilimi ga maza da mata duka.\u201d<\/em><\/p>\n<p>Haka kuma, ya yi kira ga masu gudanar da shirin da su ci gaba da ha\u0257a kai da dukkan masu ruwa da tsaki don gujewa ya\u0257uwar bayanan \u0199arya da kuma tabbatar da gaskiya a duk matakan aiwatarwa.<\/p>\n<p>Taron ya \u0199unshi gabatar da cikakkun bayanai kan manyan sassan uku na shirin AGILE, tattaunawa tsakanin mahalarta, da zaman tambayoyi da amsoshi inda malamai suka gabatar da tambayoyi kan wasu bangarorin shirin kuma aka basu bayanai dalla-dalla.<\/p>\n<p><strong>Khadijah Aliyu<\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Shirin karfafa ilimin \u2018ya\u2019ya mata a jihar Kano ya shirya taron tattaunawa da malamai da limaman masallatan Juma\u2019a domin \u0199arfafa ha\u0257in gwiwa da shugabannin addini wajen inganta goyon bayan al\u2019umma ga ilimin \u2019yan mata a fadin jihar. Taron, wanda yake \u0257aya daga cikin dabarun ha\u0257in kai na masu ruwa da tsaki na AGILE, yana da [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":7083,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[7,3,1,11],"tags":[1700],"class_list":["post-7082","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-fasaha","category-ilimi","category-labarai","category-labaran-gida","tag-agile-kano"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/10\/fda18fb6-5347-4989-9a0c-4b8f852ca02b.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7082","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=7082"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7082\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":7084,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7082\/revisions\/7084"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/7083"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=7082"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=7082"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=7082"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}