{"id":7079,"date":"2025-10-24T09:03:38","date_gmt":"2025-10-24T09:03:38","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=7079"},"modified":"2025-10-24T09:03:38","modified_gmt":"2025-10-24T09:03:38","slug":"majalisar-tattalin-arziki-ta-amince-da-shirin-gyara-cibiyoyin-horar-da-jamian-tsaro","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/majalisar-tattalin-arziki-ta-amince-da-shirin-gyara-cibiyoyin-horar-da-jamian-tsaro\/","title":{"rendered":"Majalisar Tattalin Arziki Ta Amince da Shirin Gyara Cibiyoyin Horar da Jami\u2019an Tsaro"},"content":{"rendered":"<p>Majalisar Tattalin Arzikin \u0198asa (NEC) ta amince da shirin Shugaban \u0198asa Bola Ahmad Tinubu na sake fasalin da kuma zamanantar da cibiyoyin horar da jami\u2019an tsaro a fa\u0257in \u0199asar. Wannan mataki ya biyo bayan taron majalisar na 152 da aka gudanar a Fadar Shugaban \u0198asa da ke Abuja, inda Ministan Tsare-tsaren Kasafi da Tattalin Arziki, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, ya gabatar da jawabi kan dabarun cimma burin Shugaban \u0198asa na samar da tattalin arzikin da ya kai darajar dala tiriliyan guda.<\/p>\n<p>An kafa kwamitin da Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah, ke jagoranta don tsara cikakken tsari na gyaran da sabunta cibiyoyin horar da jami\u2019an \u01b4an sanda da sauran hukumomin tsaro cikin wata guda. Mambobin kwamitin sun ha\u0257a da gwamnonin jihohin Kaduna, Ogun, Taraba, Akwa Ibom, Zamfara, da Nasarawa, yayin da tsohon Sufeton \u01b4an sanda na \u0199asa, Baba Usman, zai zama sakataren kwamitin.<\/p>\n<p>Shugaba Tinubu ya jaddada muhimmancin inganta yanayin cibiyoyin horar da jami\u2019an tsaro domin \u0199ara \u0199arfin horo da \u0199warewa tare da tabbatar da \u0199wararru da \u0199warin gwiwar ma\u2019aikatan tsaro.<\/p>\n<p>Mataimakin Shugaban \u0198asa, Kashim Shettima, wanda ya jagoranci taron, ya shawarci gwamnatocin jihohi su mai da hankali wajen inganta rayuwar jama\u2019a ta hanyar gwamnati mai ma\u2019ana da shiri na gaba. Haka kuma, majalisar ta duba bayanin da Ofishin Mai Ba da Shawara Kan Tsaron \u0198asa (ONSA) ya gabatar kan tsarin tunkarar matsalar ambaliyar ruwa, wanda ke da nufin \u0199arfafa tsarin gargadin gaggawa da shirin kare jama\u2019a daga ambaliyar ruwa a \u0199asar baki \u0257aya.<\/p>\n<p>Dangane da burin tattalin arzikin gwamnati, Sanata Bagudu ya gabatar da taswirar cimma tattalin arzikin dala tiriliyan guda nan da shekarar 2033, wanda ke ta\u2019allaka da daidaiton tattalin arziki, samar da ayyukan yi, wadatar abinci da inganta gasa tsakanin jihohi.<\/p>\n<p>NEC ta kuma yaba da tsarin cimma Muradin aikin gona na jihar Katsina tare da shawartar sauran jihohi su rungumi irin wannan tsarin na fasaha domin \u0199ara yawan amfanin gona da ha\u0257a manoma da tsarin gwamnati. Majalisar ta kuma umarci Ma\u2019aikatar Noma da samarda Abinci ta ha\u0257a da kafa cibiyoyin bayanai da lura da harkokin noma a kowace yankin siyasa a kasafin 2026.<\/p>\n<p>Kwamitin NEC na wucin gadi kan <strong>satar man fetur<\/strong>, \u0199ar\u0199ashin jagorancin Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, ya bayyana cigaba da aka samu wajen ha\u0257a kai da manyan masu ruwa da tsaki a masana\u2019antar mai don dakile satar man. Majalisar ta \u0199arfafa kwamitin da ya \u0199ara zage damtse wajen \u0199ara yawan fitar da danyen mai sama da ganga miliyan 1.72 a kowace rana tare da fa\u0257a\u0257a aikin sa zuwa kan satar ma\u2019adinai. Ana sa ran Najeriya za ta kai matakin samar da ganga miliyan 2.5 na danyen mai a kowace rana nan da \u0199arshen shekarar 2025.<\/p>\n<p><strong>Bello Wakili<\/strong><\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Majalisar Tattalin Arzikin \u0198asa (NEC) ta amince da shirin Shugaban \u0198asa Bola Ahmad Tinubu na sake fasalin da kuma zamanantar da cibiyoyin horar da jami\u2019an tsaro a fa\u0257in \u0199asar. Wannan mataki ya biyo bayan taron majalisar na 152 da aka gudanar a Fadar Shugaban \u0198asa da ke Abuja, inda Ministan Tsare-tsaren Kasafi da Tattalin Arziki, [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":7080,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[5,1,11],"tags":[1699],"class_list":["post-7079","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-kasuwanci","category-labarai","category-labaran-gida","tag-digital"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/10\/5ecf1024-da06-406a-a019-0e41cd4c8092.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7079","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=7079"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7079\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":7081,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7079\/revisions\/7081"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/7080"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=7079"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=7079"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=7079"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}