{"id":7034,"date":"2025-10-22T14:18:11","date_gmt":"2025-10-22T14:18:11","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=7034"},"modified":"2025-10-22T14:18:11","modified_gmt":"2025-10-22T14:18:11","slug":"jihar-jigawa-za-ta-kashe-sama-da-naira-biliyan-2-wajen-binciken-albarkatun-kasa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/jihar-jigawa-za-ta-kashe-sama-da-naira-biliyan-2-wajen-binciken-albarkatun-kasa\/","title":{"rendered":"Jihar Jigawa Za Ta Kashe Sama Da Naira Biliyan 2 Wajen Binciken Albarkatun Kasa"},"content":{"rendered":"<p>Majalisar zartarwa ta jihar Jigawa ta amince da kashe Naira biliyan 2.55 domin gudanar da binciken na musamman, wanda zai mayar da hankali kan albarkatun mai, gas, da sinadarin uranium, tare da cikakken binciken kimiyyar kasa kan ma\u2019adinai a fadin jihar.<\/p>\n<p>A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ya fitar, ya bayyana cewa wannan muhimmin shiri na gwamnatin yanzu babban mataki ne na gaba wajen cika alkawarin gwamnati na ganowa da kuma amfani da albarkatun kasa masu tarin yawa da ke cikin jihar Jigawa.<\/p>\n<p>A cewarsa, wannan bincike zai samar da bayanai masu muhimmanci game da ma\u2019adinai, da mmn fetur da iskar gas da ke karkashin kasa, wanda zai taimaka wajen yanke shawara mai inganci, jawo hankalin masu zuba jari, da kuma tallafawa ci gaban tattalin arziki mai dorewa.<\/p>\n<p>Ya kara da cewa, majalisar ta sake jaddada kudirin gwamnati na bunkasa tattalin arziki ta hanyar bincike da hakar albarkatun kasa bisa tsari da kuma amfani da bayanai na kimiyya.<\/p>\n<p>Sagir ya jaddada cewa, ta hanyar zuba jari a nazarin kimiyyar kasa mai inganci, jihar na da burin samar da sababbin hanyoyin samun kudaden shiga, bunkasa damar samar da ayyukan yi ga matasa, da kuma shimfida tubalin ci gaban masana\u2019antu.<\/p>\n<p>Ya kara da cewa, binciken albarkatun kasa, da mai da iskar Gas zai kasance a hannun kwararrun masana, bisa bin ka\u2019idoji da dokokin kasa da kasa, domin tabbatar da sahihanci, inganci, da amfani mai tsawo na sakamakon da za a samu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><em><strong>Usman Mohammed Zaria<\/strong><\/em><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Majalisar zartarwa ta jihar Jigawa ta amince da kashe Naira biliyan 2.55 domin gudanar da binciken na musamman, wanda zai mayar da hankali kan albarkatun mai, gas, da sinadarin uranium, tare da cikakken binciken kimiyyar kasa kan ma\u2019adinai a fadin jihar. A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ya [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":7035,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,9],"tags":[1691,59],"class_list":["post-7034","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-tattalin-arziki","tag-albarkatun-kasa","tag-jigawa"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/10\/IMG-20251022-WA0009.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7034","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=7034"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7034\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":7036,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/7034\/revisions\/7036"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/7035"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=7034"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=7034"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=7034"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}