{"id":6894,"date":"2025-10-15T12:15:21","date_gmt":"2025-10-15T12:15:21","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=6894"},"modified":"2025-10-15T12:15:21","modified_gmt":"2025-10-15T12:15:21","slug":"jihar-kano-na-aikin-gyaran-cibiyoyin-lafiya-da-za-su-yi-gogayya-da-na-%c6%99asashen-duniya","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/jihar-kano-na-aikin-gyaran-cibiyoyin-lafiya-da-za-su-yi-gogayya-da-na-%c6%99asashen-duniya\/","title":{"rendered":"Jihar Kano Na Aikin Gyaran Cibiyoyin Lafiya Da Za Su Yi Gogayya Da Na \u0198asashen Duniya"},"content":{"rendered":"<p>Shugaban Hukumar Kula da Asibitoci ta Jihar Kano (HMB), Dakta Mansur Mudi Nagoda, ya kai ziyarar ba-zata ta duba aiki a Asibitin karbar Haihuwa na Imamu Wali, na Marmara, da kuma Asibitin Sabon Bakin Zuwo.<\/p>\n<p>Ya kai ziyarar ce domin tabbar bin umarnin Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, na wucin gadi wajen sauya wuraren gudanar da ayyukan karbar haihuwa da na yara zuwa wasu cibiyoyi daban.<\/p>\n<p>A karkashin wannan umarni, an mayar da sashen haihuwa na Asibitin Koyarwa na Muhammad Abdullahi Wase zuwa Asibitin Haihuwa na Imamu Wali, yayin da aka mayar da ayyukan yara kyauta da ake yi a Asibitin Yara na Hasiya Bayero zuwa Asibitin Haihuwa na Marmara.<\/p>\n<p>Wadannan canje-canjen sun biyo bayan ci gaba da gyare-gyare da sabunta wadannan asibitoci, wani muhimmin bangare na hangen nesa na Gwamna Yusuf wajen inganta cibiyoyin lafiya a Kano zuwa matakin kasashen duniya da suka ci gaba.<\/p>\n<p>Domin tabbatar da ci gaba da bayar da ayyuka ba tare da tangarda ba, ma\u2019aikatan sassan da abin ya shafa suma an tura su zuwa sabbin wuraren da aka kebe musu.<\/p>\n<p>Yayin ziyarar, Dakta Nagoda tare da daraktoci da ma\u2019aikatan hukumar, ya jaddada muhimmancin bin umarnin gwamnati yadda ya kamata, tare da yabawa shugabanci da ma\u2019aikatan asibitocin da aka ziyarta saboda hadin kai da jajircewarsu.<\/p>\n<p>Ya kara tabbatar da kudirin hukumar wajen tabbatar da cewa bayar da ayyukan lafiya a Jihar Kano zai ci gaba da kasancewa cikin sauki, da inganci, tare da mayar da hankali kan marasa lafiya, duk da gyare-gyaren da ake yi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><strong><em>Daga Khadijah Aliyu<\/em><\/strong><\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Shugaban Hukumar Kula da Asibitoci ta Jihar Kano (HMB), Dakta Mansur Mudi Nagoda, ya kai ziyarar ba-zata ta duba aiki a Asibitin karbar Haihuwa na Imamu Wali, na Marmara, da kuma Asibitin Sabon Bakin Zuwo. Ya kai ziyarar ce domin tabbar bin umarnin Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, na wucin gadi wajen sauya [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":6895,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,4],"tags":[1480,733,39],"class_list":["post-6894","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-lafiya","tag-cibiyoyin-lafiya","tag-gyara","tag-kano"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/10\/IMG-20251015-WA0019.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6894","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=6894"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6894\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":6896,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6894\/revisions\/6896"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/6895"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=6894"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=6894"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=6894"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}