{"id":6845,"date":"2025-10-11T14:43:19","date_gmt":"2025-10-11T14:43:19","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=6845"},"modified":"2025-10-11T14:43:19","modified_gmt":"2025-10-11T14:43:19","slug":"gwamna-uba-sani-ya-gana-da-ministan-ayyuka-domin-ganin-an-kammala-aikin-titin-abuja-zuwa-kaduna","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamna-uba-sani-ya-gana-da-ministan-ayyuka-domin-ganin-an-kammala-aikin-titin-abuja-zuwa-kaduna\/","title":{"rendered":"Gwamna Uba Sani Ya Gana Da Ministan Ayyuka Domin Ganin An Kammala Aikin Titin Abuja Zuwa Kaduna\u00a0"},"content":{"rendered":"<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A cikin nuna jajircewa da hadin kai tsakanin gwamnati jiha da ta tarayya, Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, a ranar Juma\u2019a ya gana da Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi, CON, domin yin cikakken bitar aikin titin Abuja\u2013Kaduna\u2013Abuja<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Taron, wanda aka gudanar a birnin Abuja, ya nuna irin salon jagorancin Gwamna Uba Sani na jajircewarsa wajen tabbatar da kammala wannan muhimmin titi wanda ke da matu\u0199ar tasiri ga tattalin arzikin \u0199asa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Tattaunawar ta mayar da hankali ne kan yadda za a hanzarta kammala \u0253angaren Abuja\u2013Jere da Kaduna, wanda ke da muhimmanci ga miliyoyin \u2018yan Nijeriya da ke amfani da shi kullum wajen sufuri, kasuwanci da hul\u0257ar zamantakewa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Gwamna Uba Sani ya jaddada cewa wannan titin ba na yankin Arewa kadai ba ne, ya bayyana shi a matsayin jijiyar \u0199asa da \u0199asa ne wadda ke ha\u0257a yankuna daban-daban tare da \u0199arfafa ha\u0257in kai da bun\u0199asar tattalin arziki.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya kara da cewa titin Abuja- Kaduna da Kano na \u0257aya daga cikin manyan ayyukan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a \u0199ar\u0199ashin Manufar Sabon Fata na (Renewed Hope Agenda), wadda ke nufin sabunta manyan gine-ginen \u0199asa da inganta tattalin arziki.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Yace \u201cWannan titi ba hanya ce kawai ba inda yace wata hanya ce ta tattalin arziki wadda ke ha\u0257a mutane, kasuwanni, da dama a fadin Arewacin Nijeriya da ma bayan haka,\u201d<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A nasa jawabin, Sanata Umahi ya yaba wa Gwamna Uba Sani bisa yadda yake kaiwa da komowa domin kare muradun al\u2019ummar Kaduna, tare da tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ta kuduri aniyar kammala aikin cikin lokaci. Ya bayyana cewa an umarci kamfanonin da ke aikin da su rika aiki sau biyu a rana domin hanzarta cigaba ba tare da rage inganci ba.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ministan ya kara da cewa amfani da fasahar siminti mai \u0257orewa wanda zai tabbatar da cewa titin zai dawwama tare da rage kudin gyara nan gaba.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Kamfanonin da ke aikin sun yi alkawarin \u0199ara gaggautawa musamman a yankin Jere dake jihar Kaduna, inda ake sa ido sosai kan ci gaban aiki. Gwamnatin Jihar Kaduna ta kuma tabbatar da ci gaba da ha\u0257in kai da Ma\u2019aikatar Ayyuka ta Tarayya domin magance \u0199alubalen da ke iya janyo tsaiko.<\/p>\n<p>PR: Shettima Abdullahi<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>&nbsp; A cikin nuna jajircewa da hadin kai tsakanin gwamnati jiha da ta tarayya, Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, a ranar Juma\u2019a ya gana da Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi, CON, domin yin cikakken bitar aikin titin Abuja\u2013Kaduna\u2013Abuja &nbsp; Taron, wanda aka gudanar a birnin Abuja, ya nuna irin salon jagorancin Gwamna Uba Sani [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":21,"featured_media":6846,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,9],"tags":[425,875,1655,33,774,1656,1258],"class_list":["post-6845","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-tattalin-arziki","tag-abuja","tag-aikin","tag-gwamna-uba-sani-ya-gana-da-ministan-ayyuka","tag-kaduna","tag-kammala","tag-titin","tag-zuwa"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/10\/IMG-20251011-WA0011.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6845","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/21"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=6845"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6845\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":6847,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6845\/revisions\/6847"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/6846"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=6845"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=6845"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=6845"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}