{"id":6803,"date":"2025-10-09T09:00:40","date_gmt":"2025-10-09T09:00:40","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=6803"},"modified":"2025-10-09T09:00:40","modified_gmt":"2025-10-09T09:00:40","slug":"gwamnatin-neja-ta-bayyana-shirintan-hada-gwiwa-da-nsme-domin-bunkasa-hako-maadinai","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamnatin-neja-ta-bayyana-shirintan-hada-gwiwa-da-nsme-domin-bunkasa-hako-maadinai\/","title":{"rendered":"Gwamnatin Neja Ta Bayyana Shirintan Hada Gwiwa Da NSME Domin Bunkasa Hako Ma&#8217;adinai"},"content":{"rendered":"<p>Gwamnatin jihar Neja ta bayyana shirinta na yin hadin gwiwa da kungiyar injiniyoyin ma\u2019adanai ta Najeriya a matakin jiha da tarayya domin tabbatar da aiwatar da kudurorin da aka cimma a karshen taron kasa da kasa karo na ashirin da hudu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Gwamnan jihar Mohammed Umar Bago ya bayyana haka a lokacin da yake bayyana bude taron shekara-shekara da taron kasa da kasa na shekara ashirin da hudu da aka gudanar a Minna babban birnin jihar Neja.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Gwamnan wanda ya samu wakilcin shugaban ma\u2019aikata Injiniya Idris Abubakar ya bayyana cewa hakan ya zama dole domin dorewa da aikin hakar ma\u2019adanai na da matukar muhimmanci wajen kare shirin makamashi maras illa a matsayin Jigon gwamnatin sa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A nasa jawabin shugaban kungiyar injiniyoyin ma\u2019adanai ta kasa ta Najeriya Dakta Umar Hassan ya ce duk da cewa akwai dokoki da ka\u2019idoji amma aiwatar da su na da rauni sosai, wanda hakan ya faru ne saboda rashin isassun kudade na gudanar da ayyuka na ma\u2019aikatun da hukumomin tare da yin kira da a dauki matakin don magance irin wadannan matsalolin.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Dokta Umar Hassan ya bayyana cewa ba za a iya gudanar da aikin hakar ma\u2019adinai ba sai da isasshen tsaro domin ana samun ma\u2019adanai a lunguna da sako na kasa sannan kuma masu hakar ma\u2019adinai su yi aiki yadda ya kamata akwai bukatar Gwamnatin Tarayya ta yi duk abin da ya kamata don inganta a irin wannan yanayin.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ita ma da take magana shugabar ma\u2019adinan Najeriya ta kasa, Ms Rose Ndong wacce ta yabawa masu shirya taron kan shirya irin wannan taro mai tasiri wanda ta bayyana a matsayin wanda ya dace kuma a kan lokaci, ta ce dole ne Najeriya ta dauki jagoranci ta hanyar sarrafa arzikinta na ma\u2019adinai yadda ya kamata.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Taken taron shi ne &#8220;Dorewar Ayyukan Hako Ma&#8217;adanai A Matsayin Mahimmancin Tallafawa Don Canjin Nijeriya Zuwa Tushen Makamashi&#8221;. a yayin da Gwamna Umar Bago na jihar Neja da wasu \u2018yan Najeriya masu kishin kasa suka samu lambar yabo ta \u2018yan uwa na Cibiyar, saboda hidimar da suke yi wa bil\u2019adama.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>COV\u00a0\u00a0Aiyu Lawal.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnatin jihar Neja ta bayyana shirinta na yin hadin gwiwa da kungiyar injiniyoyin ma\u2019adanai ta Najeriya a matakin jiha da tarayya domin tabbatar da aiwatar da kudurorin da aka cimma a karshen taron kasa da kasa karo na ashirin da hudu. &nbsp; Gwamnan jihar Mohammed Umar Bago ya bayyana haka a lokacin da yake bayyana [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":6804,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[5,1,11],"tags":[1645],"class_list":["post-6803","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-kasuwanci","category-labarai","category-labaran-gida","tag-maadinai-minna"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/10\/7c14414e-4c2d-42ee-b206-eee1c7b6e9b9.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6803","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=6803"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6803\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":6805,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6803\/revisions\/6805"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/6804"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=6803"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=6803"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=6803"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}