{"id":680,"date":"2024-03-27T10:04:58","date_gmt":"2024-03-27T10:04:58","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=680"},"modified":"2024-03-27T10:04:58","modified_gmt":"2024-03-27T10:04:58","slug":"tarihi-da-darussa-7-daga-ya%c6%99in-badar-da-aka-gwabza-ranar-17-ga-ramadan","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/tarihi-da-darussa-7-daga-ya%c6%99in-badar-da-aka-gwabza-ranar-17-ga-ramadan\/","title":{"rendered":"Tarihi Da Darussa 7 Daga Ya\u0199in Badar Da Aka Gwabza Ranar 17, Ga Ramadan"},"content":{"rendered":"<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-681\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/vllkyt5en4tc0l5ih-720x375-1-300x156.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"156\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/vllkyt5en4tc0l5ih-720x375-1-300x156.jpg 300w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/vllkyt5en4tc0l5ih-720x375-1.jpg 720w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/p>\n<p>Ya\u0199in Badar ya faru ne a 17 ga watan Ramadan a shekara ta biyu bayan hijira, shi ne na farko tsakanin \u0199uraishawa da Annabi (SAW), wanda a \u0199arshe Allah ya bai wa Annabi (SAW) da sahabbansa nasara, a sanadiyyar abubuwan da suka wakana a ya\u0199in da irin sakamakon da ya haifar ya zama shi ne ya\u0199i mafi girma da falala a musulunci, sahabban da kuma suka halarci yakin suka zama na musamman.<\/p>\n<p>Wannan ya\u0199in yana \u0257auke da dimbin darussa wanda da al\u2019umma za ta kiyaye su to ba \u0199aramar nasara za ta cimma ba, ka\u0257an daga cikin wa\u0257annan darussa akwai:<\/p>\n<p>1- Muhimmancin Tsari Da Kyakkyawar Gudanarwa:<\/p>\n<p>\u2022\u201dTaron marasa lafiya ba ya samar da \u0199arfi sai dai ya samar da asibiti\u201d [Al-Mu\u2019utamid bin Abbad].<\/p>\n<p>A tsakanin bangarorin guda biyu, \u0253angaren Musulmai shi ne mafi ranuni ta fuskar yawa da kuma kayan ya\u0199in, domin daman can ba da niyyar ya\u0199in farko suka fito ba, amma a sakamakon kyakkyawan tsari na Annabi (SAW) da iya gudanarwa tun daga kan gaggauta fara isowa wurin da za a fafata (Badar), da za\u0253ar mafi dacewar wurin kafa sansani da kuma tsara su kansu mayakan da sauran abubuwa, musulmai suka iya cin nasara tare da cewa wa\u0257nada suke ya\u0199a \u0257in kafiran makka sun fi su yawa da kayan aiki da shirin ya\u0199in, wanda wannan yana nuna cewa \u0199arancin abun hannu ko arziki ba ya hana cin nasara da samun ci gaba matu\u0199ar al\u2019umma ko \u0199asa ko gwamnati tana da kyakkywan tsari da kuma iya gudanarwa, hakanan yawa da wadata ba ya bayar da nasara matu\u0199ar al\u2019umma ko \u0199asa ko gwmanti ta kasance a hargiste ko lalaltaciyya ba ta tsari ba, domin taron marasa lafiya baya ha\u0257a \u0199arfi sai dai ya ha\u0257a asibiti.<\/p>\n<p>2- Muhimmancin Shawara:<\/p>\n<p>\u2022\u201dJama\u2019a ta yi kuskure ya fi mutum \u0257aya ya yi daidai domin in ya iya cankar daidai sau \u0257aya to ya yi ta fa\u0257awa kuskure sau da yawa, kuma ya rasa wanda zai mai uzuri\u201d [Ibrahim Al\u2019andalusy].<\/p>\n<p>Shawara ta taka muhimiyyar rawa a nasarar Musulmai a wannan ya\u0199i, Annabi (SAW) duk da cewa shi ya fi kowa hankali da tinani da hangen nesa bugu da \u0199arima ana saukar masa da wahayi amma duk da haka sai da Allah ya umarce shi da ya dinga shawara har abu Huraira yake cewa: banga wani mai yawaita neman shawarar sahabbansa ba sama da Manzon Allah (SAW) ba. Wanda wannan yake nuna muhimmancin shawara kuma babu wanda yake wadatuwa daga gareta komai irin iliminsa da wayewarsa da kaifin tunaninsa, hakanan shawara ita ce mabu\u0257in ci gaba da nasar al\u2019umma da ita ne ake iya ha\u0257a kan al\u2019umma domin duk wanda ya ga ana yi da shi to wannan zai \u0199ara masa dangantuwa zuwa ga al\u2019ummarsa, zai ba ta gudunmowa sosai domin yana jin cewa al\u2019ummarsa ce ba ta wani ba, hakanan da shawara ne a kan iya na\u0257a wanda ya dace a idan ya dace, da kuma shawara ne ake iya kubuta daga fa\u0257awa hatsarin ringingimu da fa\u0257ace-fa\u0257ace, don haka wajibi ne a \u0257abba\u0199a shawara kuma a neme ta a wurin kowa domin iya aiwatar da shawarar, iya nasarar da za a cimma ko da kuwa wannan al\u2019umma musulma ce ko kafira.<\/p>\n<p>3- Dagewa Da Addu\u2019a Da Kuma Dogaro Da Allah:<\/p>\n<p>\u2022\u201dWatakila nasara tana jinkiri saboda al\u2019umma ta \u0199ara \u0199arfin ala\u0199arta da Allah a yayin da take fama take shan wahala, sai ta ga ba ta da wani sai Allah. Hakan sai ya sa ta dawo kan turba da gawadabe na gaskiya, kuma idan ta samu nasara hakan ba zai sa ta karkace daga kan hanyar gaskiya da alheri da adalci ba, don ta san da su ne Allah ya bata nasara.\u201d [ Sayyid Qudub].<\/p>\n<p>Duk da cewa Annabi (SAW) ya san shi da sahabbansa su ne a kan gaskiya, kuma Allah ma ya yi mai al\u0199awarin nasara amma bai shantake ba, bai ce \u201cCin Nasara Dole\u201d ba duk bai yi hakanan ba sai dai dagewa da dogewa a kan addu\u2019a har sahabbansa, sannan suka fara ganin kamar abun ya yi yawa, wanda a sanadiyyar haka Allah ya saukar masa da nasararsa.<\/p>\n<p>Anan zamu fahimci cewa Dogaro da Allah da kuma yin addu\u2019a shi ne babban makamin nasara bayan mutum ya gama \u0257aukar dukkanin matakai.<\/p>\n<p>Rashin riko da wannan jigo yana jawowa a gagara samun nasara a rayuwa, domin \u0199arfin musulmi daga Allah yake nasarar kuma ta shi ce, shi yake bayar da ita ga wanda ya ga dama, shi yasa a ko wane hali Annabi (SAW) yake ba ya \u0199in addu\u2019a, ba ya \u0199in saka Allah a lamarinsa, bal kodayaushe yana \u0199ara nasara da \u0257aukaka, yana \u0199ara ta\u2019allaka da Allah.<\/p>\n<p>4- Jagoranci Shi ne Ginshikin Al\u2019ummah:<\/p>\n<p>\u2022\u201dIdan kana son kassara ko wacce al\u2019umma, to ka fara gusar da jagororinta ko mayar da su \u0199ar\u0199ashinka\u201d<\/p>\n<p>A ya\u0199in Badar an kashe kafirai 70, a ya\u0199in Uhud kuma an kashe muslmai 70 amma a ya\u0199in Badar aka yanke cewa musulmai sun yi nasara a kan kafirai sa\u0253anin ya\u0199in Uhud wanda duk da an yi wa musulmai \u0253arna amma kuma ba a ci nasara a kansu ba, me ya bambanta wa\u0257annan ya\u0199e-ya\u0199en biyu? Abin da ya bambanta su shi ne jagorori, kafiran Makkah sun yi asarar jagororinsu da yawa a Badar, wanda rashinsu ne yasa daular Makkah ta fara shiga rauni har aka cinyeta a \u2018Fathu Makkah,\u2019 sabanin ya\u0199in Uhud wanda muslmai ba su yi wannan asarar ba shi yasa ma har Abu Sufyan ya shiga tambaya ko an kashe Annabi (SAW) da Abubakar da Umar? Saboda ya san a cikin kashe wa\u0257annan nasarar gaske take samuwa, daganan kafiran suka sake cin alwashin sai an sake ha\u0257uwa a Badar sun \u0257au fansa duk da irin barnar da suka yi uhud amma hakan bai gamsar da su ba.<\/p>\n<p>Jagorori su ne \u0199ashin bayan kowacce al\u2019umma, duk sanda aka yi niyyar kassara wata al\u2019umma ko tafiya ana farawa ne daga kan jagorinta ko dai a kawar da su, ko kuma a shigar da su \u0199arkashin wani ikon ta yadda za a dinga juya wannan al\u2019umma ko tafiya yadda ake so, don haka in kana son auna lafiyar al\u2019umma ko tafiya to ka duba jagorancinta.<\/p>\n<p>5- Sadaukarwar Sahabbai:<\/p>\n<p>\u2022\u201dNa je wurin Qaisar da Kisra da Najashi, amma banga wanda mutanesa suke girmama shi ba, suke son shi ba kamar yadda Sahabban Muhammad (SAW) Suke girmama Muhammad (SAW) ba\u201d [Urwa bin Mas\u2019ud Assaqafy].<\/p>\n<p>A wannan ya\u0199in zamu \u0199ara gane cewa lallai sahabban Annabi (SAW) za\u0253a\u0253\u0253u ne daga Allah, za mu ga yadda imani ya gama mamaye zukatansu ta yadda tun farko suka yadda suka marawa Annabi (SAW) baya a wannan ya\u0199in da duk wasu ma\u2019aunan \u0257an adam suna nuni da cewa ba yadda za a yi a ci nasara, amma haka suka yadda suka \u0199utsa cikin halaka ba tare da la\u2019akari da wannan ba, suna masu ya\u0199ar iyayensu da \u01b4an uwansu da \u01b4an danginsu ba don komai ba sai don \u0199asancewar imani sama yake da komai a wurinsu, sama yake da \u01b4an uwantaka sama yake da \u0199asa, da wannan imanin da sadaukarwar ne sahabbai suka kai matsayin da suka kai.<\/p>\n<p>6- Cikakken Kishi Da Soyayya Yana Ga Addinin Allah Ne:<\/p>\n<p>\u201cDa a ce a kan \u01b4an uwantaka ko \u0199abila ko \u0199asa ake kulla soyayya ko \u0199iyayya da Annabi (SAW) bai barranta daga baffansa Abu-Lahab ba ya\u0199i \u0198uraishawa ba, da kuma barin makkah ba sai ana gina wala\u2019ine a kan a\u0199ida wadda tafi jini da \u0199asa tsada\u201d [ Adham Assharqawy].<\/p>\n<p>A wannan ya\u0199in za mu ga yadda Annabi saw da sahabbansa suka yi ya\u0199in \u01b4an uwansu \u01b4an \u0199abilarsu \u01b4an garinsu wanda a ma\u2019aunin wannan zamanin hakan cin amanar \u0199asa ne da rashin kishinta. A nan za mu ga cewa a musulunci babu wata ala\u0199a da take sama da ta addini a kansa ne musulmi yake \u0199ulla soyayya yake kuma kulla \u0199iyayya ba tare da la\u2019akari da \u0199asa ko launi ko jinsi ba, hakanan a musulunci babu wani abu da ake kira da kishin \u0199asa a ma\u2019anarsa ta yau, kasar musulmai ita ce in da yake samun \u01b4ancin bautar Allah ba in da Turawa suka zana a takarda ba.<\/p>\n<p>7- Izzar Al\u2019umma Tana Cikin Aiwatar Da Jihadi:<\/p>\n<div class=\"google-auto-placed ap_container\">\n<p>\u2022\u201dJihadi yana kare al\u2019ummah ta sanadiyyarsa ya kuma sake dun\u0199ulewa, barinsa kuma shi yake kacaccalata ya \u0257ai\u0257aitata\u201d [ Abdul\u2019Aziz Attarify].<\/p>\n<p>Sakamakon ya\u0199in Badar Muslmai sun zama wani \u0199arfi da kowa yake tsoron tinkara, ya sanya musu kwarjini a idon abokan gaba, ya kuma \u0257aukaka su. Wannan shi yake \u0199ara nuna mana cewa lallai izzar al\u2019umma da \u0257aukakarta tana cikin aiwatar da jihadi, rashin aiwatar da shi shi zai kaita zuwa ga \u0199as\u0199anci da halaka, kamar yadda muke gani a yau, yana daga cikin alfanun jihadi kawar da sa\u0253ani da ha\u0257e kan al\u2019umma domin tunkarar babban abokin gaba, hakanan da jihadi ne al\u2019umma take \u0199ara samun kwanciyar hankali da yalwa da arziki shi yasa duk wanda ya karanta tarihin musulmai zai ga cewa babu sanda suka fi samun aminci da wadata sai a lokutan jihadi, babu sanda suka shiga \u0199askanci da rashin tsaro da talauci sai sanda suka saki jihadi, wanda daman wannan shi ne al\u0199warin Allah.<\/p>\n<p>Don haka duk da cewa yanzu ba aiwatar da jihadi ba, idan dai ba a inda suke fuskantar ya\u0199i ba, amma wajibi ne a sanar da al\u2019umma, shi ya zamanto a \u0199wa\u0199walenta ko da ba ta da halin aiwatar da shi.<\/p>\n<p>Wa\u0257annan wasu darussane da zamu iya amfana daga ya\u0199in Badar. Allah ya datar da mu.<\/p>\n<\/div>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Ya\u0199in Badar ya faru ne a 17 ga watan Ramadan a shekara ta biyu bayan hijira, shi ne na farko tsakanin \u0199uraishawa da Annabi (SAW), wanda a \u0199arshe Allah ya bai wa Annabi (SAW) da sahabbansa nasara, a sanadiyyar abubuwan da suka wakana a ya\u0199in da irin sakamakon da ya haifar ya zama shi ne [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":681,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[7,3,5,1,11,4,6,2,9,8],"tags":[209],"class_list":["post-680","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-fasaha","category-ilimi","category-kasuwanci","category-labarai","category-labaran-gida","category-lafiya","category-nishadi","category-siyasa","category-tattalin-arziki","category-tsaro","tag-sawa"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/vllkyt5en4tc0l5ih-720x375-1.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/680","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=680"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/680\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":682,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/680\/revisions\/682"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/681"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=680"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=680"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=680"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}