{"id":6764,"date":"2025-10-04T08:11:16","date_gmt":"2025-10-04T08:11:16","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=6764"},"modified":"2025-10-04T08:11:16","modified_gmt":"2025-10-04T08:11:16","slug":"gwamnati-ta-sa-wutar-lantarki-ta-amfani-da-hasken-rana-a-kasuwar-dutsen-jigawa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamnati-ta-sa-wutar-lantarki-ta-amfani-da-hasken-rana-a-kasuwar-dutsen-jigawa\/","title":{"rendered":"Gwamnati Ta Sa Wutar Lantarki Ta Amfani Da Hasken Rana A Kasuwar Dutsen Jigawa"},"content":{"rendered":"<p>Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da aikin samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana a Kasuwar Dutse Ultra-Modern Market, inda ya cika alkawarin gwamnatinsa na samar da tsaftataccen makamashi ga \u2018yan kasuwa a jihar Jigawa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Aikin wanda Hukumar Samar da Tattalin Arzikin Kasa da Samar da ayyukan yi ta Jihar Jigawa ta gudanar, ya hada shaguna 300 da wutar lantarki daga na\u2019urorin hasken rana da aka sanya a cikin kasuwar, inda kowane shago kuma an saka masa fanka amfani da hasken rana kyauta.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Da yake jawabi a wajen bikin kaddamar da kasuwar a hukumance, Malam Umar Namadi ya ce shirin zai saukaka harkokin kasuwanci, da rage kashe kudi, da kuma bunkasa ribar \u2018yan kasuwa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya kuma yi alkawarin kafa fitilun masu amfani da hasken rana a kasuwar domin inganta tsaro, sannan ya bayyana wasu matakai na tallafa wa \u2018yan kasuwa a jihar Jigawa, wadanda suka hada da samar da reshen bankin masana\u2019antu (BOI) a jihar da kuma sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da bankin, inda gwamnatin jihar ta zuba naira biliyan 4 domin tallafa wa masu kananan sana\u2019o\u2019i.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Namadi ya kuma bukaci \u2019yan kasuwa a jihar da su yi amfani da wannan wurin su samu kudaden da kungiyar ta BOI ke da su don fadada kasuwancinsu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A nasa jawabin shugaban kungiyar \u2018yan kasuwa ta jihar Jigawa Alhaji Yahaya Ibrahim ya yabawa gwamnan bisa samar wa kasuwar wutar lantarki da hasken rana da kuma shirye-shiryen karfafawa \u2018yan kasuwa daban-daban.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya kara da cewa aikin samar da wutar lantarkin kasuwar ya kasance farkon shirin Gwamna Namadi ga \u2018yan kasuwa a jihar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Gidan rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, wani bangare na aikin, na sanya na&#8217;urar samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana, mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ne ya kaddamar da shi a shekarar da ta gabata yayin wata ziyarar aiki da ya kai jihar, kuma a lokacin gwamnatin jihar ta yi alkawarin sa wutar a rumfuna kowa da kowa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>USMAN MZ<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da aikin samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana a Kasuwar Dutse Ultra-Modern Market, inda ya cika alkawarin gwamnatinsa na samar da tsaftataccen makamashi ga \u2018yan kasuwa a jihar Jigawa. &nbsp; Aikin wanda Hukumar Samar da Tattalin Arzikin Kasa da Samar da ayyukan yi ta Jihar Jigawa ta [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":6765,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[5,1,11],"tags":[1630],"class_list":["post-6764","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-kasuwanci","category-labarai","category-labaran-gida","tag-lantarkin-hasken-rana"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/10\/e1fa2d24-176c-4add-a165-aa1a0c38126d.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6764","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=6764"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6764\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":6766,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6764\/revisions\/6766"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/6765"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=6764"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=6764"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=6764"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}