{"id":6745,"date":"2025-10-03T08:37:59","date_gmt":"2025-10-03T08:37:59","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=6745"},"modified":"2025-10-03T08:37:59","modified_gmt":"2025-10-03T08:37:59","slug":"gwamnatin-jihar-nasarawa-ta-ware-naira-biliyan-biyu-domin-biyan-alawus-alawus","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamnatin-jihar-nasarawa-ta-ware-naira-biliyan-biyu-domin-biyan-alawus-alawus\/","title":{"rendered":"Gwamnatin jihar Nasarawa ta ware naira biliyan biyu domin biyan alawus alawus \u00a0"},"content":{"rendered":"<p>Gwamnatin jihar Nasarawa ta ce ta ware naira biliyan biyu domin biyan kudaden tallafin karatu da alawus alawus na guraben karatu a jihar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana hakan ne a lokacin bikin kaddamar da biyan alawus-alawus na shekarar 2023\/2024 da aka gudanar a Kwalejin Ilimi ta karamar hukumar Akwanga ta jihar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Gwamnan a lokacin da yake kaddamar da shirin raba kudaden ya jaddada cewa baya ga biyan kudaden NECO, gwamnatin jihar tana biyan dalibai sama da 155 tallafin karatu na kasashen waje da sama da dalibai 30,000 a fadin kasar nan.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Shima da yake nasa jawabin, kakakin majalisar dokokin jihar Nasarawa, Dokta Danladi Jatau wanda shugaban kwamitin majalisar kan harkokin ilimi Mista Abel Yakubu Bala ya wakilta ya yaba da yunkurin kawo sauyi da gagarumar gudunmawar da gwamnan jihar ya bayar a fannin ilimi tare da bayyana cewa ayyukan da gwamnan ke yi a fannin na samar da sakamako mai kyau yana mai kira da a ci gaba da gudanar da shi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya ce Majalisar Dokokin Jihar za ta ci gaba da bayar da dukkan goyon bayan da ya dace ga manufofin Gwamnatin Jihar a fannin Ilimi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A nata bangaren, babbar sakatariyar hukumar bayar da tallafin karatu ta jihar Nasarawa, Hajiya Sa\u2019adatu Yahaya ta bayyana cewa sama da dalibai dubu goma sha shida da dari bakwai ne za su ci gajiyar wannan Shirin da ya lakume sama da naira miliyan dari biyar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Kwamishinan Ilimi na Jihar, Dokta John Mamman wanda ya bayyana muhimmancin shirin ilimi na Gwamnatin Jihar ya bukaci daliban da suka amfana da su yi amfani da kudaden alawus din yadda ya dace<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Shugaban kungiyar daliban jihar Nasarawa NASSA na kasa, Kwamared Abimiku Ovy David ya yabawa Gwamna Abdullahi Sule bisa wannan karimcin tare da bada tabbacin cewa alawus-alawus din zai taimaka musu wajen tafiyar da karatunsu tare da jaddada aniyar daliban na ci gaba da zama jakadu nagari a jihar a duk inda suke.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>COV\/Aliyu Muraki\/Lafia.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnatin jihar Nasarawa ta ce ta ware naira biliyan biyu domin biyan kudaden tallafin karatu da alawus alawus na guraben karatu a jihar. &nbsp; Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana hakan ne a lokacin bikin kaddamar da biyan alawus-alawus na shekarar 2023\/2024 da aka gudanar a Kwalejin Ilimi ta karamar hukumar Akwanga ta jihar. &nbsp; Gwamnan [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":6747,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[3,5,1,11],"tags":[1621],"class_list":["post-6745","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-ilimi","category-kasuwanci","category-labarai","category-labaran-gida","tag-alawus-nasarawa"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/10\/ebc4389f-3f66-4019-aa15-56492a0dcb43.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6745","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=6745"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6745\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":6751,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6745\/revisions\/6751"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/6747"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=6745"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=6745"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=6745"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}