{"id":6714,"date":"2025-10-02T09:34:37","date_gmt":"2025-10-02T09:34:37","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=6714"},"modified":"2025-10-02T09:34:37","modified_gmt":"2025-10-02T09:34:37","slug":"gwamnan-jigawa-ya-taya-alumma-murnar-samun-yancin-kai","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamnan-jigawa-ya-taya-alumma-murnar-samun-yancin-kai\/","title":{"rendered":"Gwamnan Jigawa Ya Taya Al&#8217;umma Murnar Samun &#8216;Yancin Kai"},"content":{"rendered":"<p>Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa, ya taya gwamnati da al\u2019ummar Nijeriya murnar cika shekaru 65 da samun \u2018yancin kai, inda ya bayyana ranar a matsayin abin tunawa da hadin kai, juriya, sadaukarwa da suka gina kasar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A sakonsa na fatan alheri, Gwamna Namadi ya ce bikin ba wai kawai lokacin yin tunani ne kan irin gwagwarmayar da iyayen da suka kafa kasar suka yi ba, har ma wata dama ce ta sabunta sadaukarwar hadin gwiwa don samar da zaman lafiya, ci gaba, da wadata.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&#8220;A yau, muna bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun &#8216;yancin kai cikin alfahari da godiya. Wannan ranar tana tunatar da mu sadaukarwar da jaruman mu suka yi a baya, wadanda hangen nesa da jajircewarsu suka kafa tushen kasarmu mai kauna. A matsayinmu na al&#8217;umma, dole ne mu ci gaba da tabbatar da akidar hadin kai, adalci, da yiwa bil&#8217;adama hidima,&#8221; in ji gwamnan.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Malam Umar Namadi ya bayyana cewa, duk da kalubalen da Najeriya ke fuskanta, Najeriya na ci gaba da samun ci gaba a karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, wanda manufofinsa ke da nasaba da karfafa tattalin arziki, inganta tsaro, da samar da damammaki ga &#8216;yan kasa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A cewarsa, gwamnatinsa ta dukufa wajen ganin ta kara kaimi ga kokarin gwamnatin tarayya ta hanyar baiwa al\u2019ummarmu fifiko, zuba jari a fannin noma, ilimi, kiwon lafiya, samar da ababen more rayuwa, da samar da damammaki ga matasa da mata.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&#8220;Tare, za mu gina kasa mai karfi da kuma ba da gudummawa ga daukakar Najeriya.&#8221;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Namadi ya bukaci \u2018yan Najeriya da su ci gaba da kasancewa da hadin kai da kuma fata, yana mai jaddada cewa bambancin al\u2019ummar kasa ne tushen karfi maimakon rarrabuwa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya yi kira ga \u2018yan kasa da su ci gaba da marawa manufofi da shirye-shiryen gwamnati goyon baya domin samun ci gaba mai dorewa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&#8220;Yayin da muke daga tutarmu mai kore da fari a yau, bari mu tuna cewa alhakin gina Najeriya mai ci gaba ya rataya a kan mu baki daya. Tare da hadin kai, imani, da azama, za mu shawo kan kalubalen mu, mu cika burinmu na kasa mai girma&#8221;.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>USMAN MZ\/Dutse<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa, ya taya gwamnati da al\u2019ummar Nijeriya murnar cika shekaru 65 da samun \u2018yancin kai, inda ya bayyana ranar a matsayin abin tunawa da hadin kai, juriya, sadaukarwa da suka gina kasar. &nbsp; A sakonsa na fatan alheri, Gwamna Namadi ya ce bikin ba wai kawai lokacin yin tunani ne [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":6715,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[5,1,11],"tags":[1606],"class_list":["post-6714","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-kasuwanci","category-labarai","category-labaran-gida","tag-jigawa-murna"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/10\/d1016d51-2e90-4c83-b762-5c99a9040e50.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6714","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=6714"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6714\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":6716,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6714\/revisions\/6716"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/6715"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=6714"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=6714"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=6714"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}