{"id":6685,"date":"2025-09-30T11:00:49","date_gmt":"2025-09-30T11:00:49","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=6685"},"modified":"2025-09-30T11:00:49","modified_gmt":"2025-09-30T11:00:49","slug":"dole-arewa-ta-yi-magana-da-murya-%c9%97aya-kan-tsaro-da-tattalin-arziki-in-ji-gwamnan-zamfara","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/dole-arewa-ta-yi-magana-da-murya-%c9%97aya-kan-tsaro-da-tattalin-arziki-in-ji-gwamnan-zamfara\/","title":{"rendered":"Dole Arewa Ta Yi Magana Da Murya \u018aaya Kan Tsaro Da Tattalin Arziki, In ji Gwamnan Zamfara"},"content":{"rendered":"<p>Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya bu\u0199aci jihohin Arewa 19 da su tsaya \u0199yam su jajirce su yi magana da murya \u0257aya kan harkokin tsaro da tattalin arziki.<\/p>\n<p>Gwamnan ya jagoranci taron ranar farko ta bangaren Zuba Jari da Bun\u0199asa Masana\u2019antu ta Arewacin Nijeriya a ranar Litinin a otel \u0257in Abuja Continental.<\/p>\n<p>Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa \u0198ungiyar Dattawan Arewa \u0199ar\u0199ashin jagorancin Farfesa Ango Abdullahi ce ta shirya taron zuba jarin.<\/p>\n<p>Sanarwar ta \u0199ara da cewa, taken taron shi ne \u201cBu\u0257e Dabarun Damarmaki\u201d, kuma ya tattaro duk masu ruwa da tsaki a sassan Arewacin Nijeriya.<\/p>\n<p>A nasa jawabin, Gwamna Lawal ya yaba wa \u0198ungiyar Dattawan Arewa bisa jajircewar da take yi wajen ci gaban yankin Arewa.<\/p>\n<p>&#8220;Ta hanyar kiran wannan taro a \u0199ar\u0199ashin taken &#8216;Bu\u0257e Dabarun Damarmaki,&#8217; kun sake nuna kyakkyawar manufar ku kan makomarmu baki \u0257aya.<\/p>\n<p>\u201cBangarori kamar \u2013 Ma\u2019adinai, Noma, da Makamashi \u2014 ba bisa ha\u0257ari aka same su ba, ginshi\u0199ai ne wa\u0257anda dole ne a gina su don ci gaban Arewacin Nijeriya. A Zamfara muna sane da halin da muke ciki: \u0199asa mai albarkar ma\u2019adanai masu tarin yawa da \u0199asar noma, amma duk da haka mutanenmu ba su ci cikakken ribar wa\u0257annan abubuwan ba.<\/p>\n<p>&#8220;Muhimmin tambaya a gare mu a matsayinmu na shugabanni ba shi ne yin abin da ya kamata ba, amma ta yaya za mu iya juya akalar abin da ake muke da shi zuwa ci gaban al&#8217;umma. Don jawo jarin da ake bu\u0199ata da kuma samar da masana&#8217;antu a yankinmu don amfanin al&#8217;umma, dole ne mu tsaya hai\u0199an, mu rungumi sabuwar hanyar ha\u0257in gwiwa.&#8221;<\/p>\n<p>Gwamna Lawal ya ci gaba da jaddada cewa, Arewa mai zaman lafiya, Arewa ce mai \u0199arfin tattalin arziki, yanki ne da ya kamata shugabannin jihohinta 19 su zurfafa ha\u0257in gwiwa fiye da siyasa.<\/p>\n<p>&#8220;Dole ne mu ha\u0257a \u0199arfi da \u0199arfe wajen kare mutane da saka hannun jari. Tsaro shi ne babban abin da ake bu\u0199ata na duk wani ci gaba mai ma&#8217;ana. Masu zuba jari, na cikin gida da na lasa da \u0199asa, ba masu hannu da shuni ba ne; su masu gaskiya ne. Ba za su saka jari a inda babu tsaro ba. Dole ne mu ha\u0257a \u0199arfin tsaron mu, mu raba hankali a cikin ha\u0199i\u0199anin lokaci, da kuma samar da manyan jami&#8217;an tsaro na al&#8217;umma don samar da ingantaccen tsaro.<\/p>\n<p>\u201cA Zamfara, \u0199o\u0199arinmu a fili yake, mun \u0199aura daga halin da ake ciki a da na rashin gaskiya da rashin bin doka da oda a fannin ma\u2019adinai zuwa yanayin na gaskiya da amana. Mun farfa\u0257o da harkar noma ta hanyar inganta noman zamani, sarrafa kayan noma, da samun rance. Kuma muna samar da yanayi mai tsaro da kwanciyar hankali wanda shi ne \u0199ashin bayan komai.<\/p>\n<p>&#8220;Kirana a yau shi ne Yarjejeniyar Tattalin Arziki na Arewacin Nijeriya \u2014 ala\u0199ar mai \u0199arfi tsakanin jihohi 19 da su yi magana da murya \u0257aya kan harkokin tsaro da tattalin arziki. Samar da hanya guda \u0257aya ga manyan masu zuba jari da ke neman yin kasuwanci a fa\u0257in yankin. A hafa hannu a muhimman ababen more rayuwa kamar wutar lantarki da jirgin \u0199asa, igiya mai \u0199arfi da zara ha\u0257e jihohin mu.&#8221;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya bu\u0199aci jihohin Arewa 19 da su tsaya \u0199yam su jajirce su yi magana da murya \u0257aya kan harkokin tsaro da tattalin arziki. Gwamnan ya jagoranci taron ranar farko ta bangaren Zuba Jari da Bun\u0199asa Masana\u2019antu ta Arewacin Nijeriya a ranar Litinin a otel \u0257in Abuja Continental. Wata sanarwa da [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":6686,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[5,1,11],"tags":[115],"class_list":["post-6685","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-kasuwanci","category-labarai","category-labaran-gida","tag-zamfara"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/IMG-20250929-WA0036.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6685","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=6685"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6685\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":6687,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6685\/revisions\/6687"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/6686"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=6685"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=6685"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=6685"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}