{"id":6640,"date":"2025-09-25T07:10:49","date_gmt":"2025-09-25T07:10:49","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=6640"},"modified":"2025-09-25T07:10:49","modified_gmt":"2025-09-25T07:10:49","slug":"gwamnatin-kano-ta-rarraba-takardun-guraben-karatu-ga-dalibai","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamnatin-kano-ta-rarraba-takardun-guraben-karatu-ga-dalibai\/","title":{"rendered":"Gwamnatin Kano Ta Rarraba Takardun Guraben Karatu Ga Dalibai"},"content":{"rendered":"<p>Gwamnatin jihar Kano, ta raba wa daliban da suka kamala karatun Furamare takardun gurbin karatu zuwa manyan makarantun sakandare a fadin jihar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Da yake jawabi yayin bikin kaddamarwar a makarantar sakandiren \u2019yan mata ta Maryam Aloma da ke Kano, Kwamishinan Ilimi na Jihar, Dakta Ali Haruna Makoda, ya ce shirin ya nuna yadda gwamnati ta himmatu wajen samar da ilimi kyauta da kuma wayar da kan al\u2019umma don bunkasa ilimi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Dokta Makoda ya bayyana sauye-sauyen da gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta bullo da su, da suka hada da daukar malamai aiki, gyaran makarantu, da samar da kayayyakin koyarwa, inda ya bayyana su a matsayin matakan farfado da harkar ilimi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya danganta fitowar jihar Kano a matsayin jihar da ta zo kan gaba a jarabawar NECO ta shekarar 2025 ga yadda Gwamna Yusuf ya ba da fifiko a fannin ilimi, inda ya yaba wa gwamnan kan yadda ya rika tallafa wa bukatun ma\u2019aikatar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>\u201cMai girma Alhaji Abba Kabir Yusuf yana aiki tukuru, shi ya sa harkar ilimi ta Kano ke tafiya cikin hanzari, misali, don magance matsalar karancin malaman lissafi, gwamna ya amince da daukar sabbin ma\u2019aikata, kuma nan ba da dadewa ba za a tura su makarantu a fadin jihar.\u201d Inji Dr. Makoda.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Kwamishinan ya kuma yi kira ga iyaye da su kara kaimi ga kokarin gwamnati ta hanyar tabbatar da \u2018ya\u2019yansu na zuwa makaranta akai-akai domin samun ilimi mai inganci.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A nasa jawabin, babban sakataren hukumar kula da manyan makarantun sakandire ta jihar Kano, Alhaji Rabi\u2019u Saleh Gwarzo, ya bayyana cewa, Kano ba ta taba shiga matsayi na gaba na NECO ba sai a yanzu, inda ya ce wannan nasarar ta samu ne sakamakon yadda Gwamna Yusuf ya himmatu wajen inganta ilimi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya jaddada bukatar yin aiki tare tsakanin Hukumar Kula da Ilimi ta (SUBEB), Hukumar Kula da Manyan Makarantu ta Sakandare, da Sashen Albarkatun Ilimi don ba da tabbacin samun sauyi ga dalibai.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Hakazalika, shugaban kungiyar iyaye da malamai ta jiha (PTA), Alhaji Dahiru Salisu Mai Jimiri da shugaban kwamitin kula da makarantu (SBMC), Tijjani Haladu Baraya, sun yaba da kokarin gwamnati na farfado da ilimi tare da yin kira ga iyaye da kungiyoyin farar hula da su ci gaba da tallafawa gwamnati.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Shirin wanda ake ganin wani muhimmin mataki ne na dorewar ci gaban ilimi a Kano, ya samu halartar daraktocin shiyya, jami\u2019an ma\u2019aikatar, da manyan wakilan SUBEB da kuma hukumar kula da manyan makarantun sakandire.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>COV\/KHADIJAH ALIYU<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnatin jihar Kano, ta raba wa daliban da suka kamala karatun Furamare takardun gurbin karatu zuwa manyan makarantun sakandare a fadin jihar. &nbsp; Da yake jawabi yayin bikin kaddamarwar a makarantar sakandiren \u2019yan mata ta Maryam Aloma da ke Kano, Kwamishinan Ilimi na Jihar, Dakta Ali Haruna Makoda, ya ce shirin ya nuna yadda gwamnati [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":6641,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[3,1,11],"tags":[1590],"class_list":["post-6640","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-ilimi","category-labarai","category-labaran-gida","tag-ilimi-kano"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/aa38b7a3-e92b-41f0-bb9c-ccf58817266e.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6640","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=6640"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6640\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":6642,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6640\/revisions\/6642"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/6641"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=6640"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=6640"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=6640"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}