{"id":6622,"date":"2025-09-22T19:57:15","date_gmt":"2025-09-22T19:57:15","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=6622"},"modified":"2025-09-22T19:57:15","modified_gmt":"2025-09-22T19:57:15","slug":"coret-ta-yaba-da-nasarar-shirin-ciyarda-daliban-makarantun-makiyaya","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/coret-ta-yaba-da-nasarar-shirin-ciyarda-daliban-makarantun-makiyaya\/","title":{"rendered":"CORET Ta Yaba Da Nasarar Shirin Ciyarda Daliban Makarantun Makiyaya"},"content":{"rendered":"<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Haddadiyar Kungiyoyin Makiyaya na kasashen Africa (CORET) ta bayyana cewa an samu karin yawan \u0257alibai a makarantun makiyaya cikin watanni goma da aka fara shirin ciyar da \u0257alibai.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Babban Sakataren CORET, Muhammed Bello Tukur, ya bayyana haka a taron kwana \u0257aya da aka gudanar a Kaduna domin \u0199ara wa ma\u2019aikata da abokan hul\u0257arsu \u0199warewa kan harkar ciyar da \u0257alibai.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Taron ya mayar da hankali ne wajen duba nasarorin da aka samu cikin watanni goma tun lokacin da aka fara shirin a Ladduga, Karamar Hukumar Kachia ta Jihar Kaduna, da kuma Maigatari a Jihar Jigawa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Babban Sakataren CORET, Muhammed Bello Tukur, ya bayyana cewa shirin ya shafi makarantun makiyaya kawai a jihohin Jigawa da Kaduna.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya ce ciyarwa na daga cikin manyan matsalolin da ke sa yara barin makarantu, don haka shirin ya \u0199unshi amfani da al\u2019ummomin yankuna wajen samar da abincin \u0257alibai.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya \u0199ara da cewa an sayi kayan abinci daga cikin al\u2019umma tare da ha\u0257a su wajen tabbatar da ingancin abincin da \u0257alibai ke ci. Bugu da \u0199ari, CORET ta samar da rijiyoyin burtsatse domin tabbatar da samun ruwa na sha da na yau da kullum.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Muhammed Bello Tukur ya yaba da irin goyon bayan da abokan hul\u0257a musamman ECOWAS, da kuma Gwamnatin Tarayya da Jihohi ke bayarwa wajen tabbatar da nasarar shirin.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A nasa jawabin, Ko\u2019odinatan Shirin, Dakta Abdu Umar Ardo, ya bayyana cewa shirin ya zama nasara daga komai zuwa abu mai amfani tun da jihohin suka rungumi karatun \u2019ya\u2019yan makiyaya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Haka kuma, a kasidarsa, Bashir Abbo ya bayyana cewa bincike ya nuna akwai bukatar \u0199wararrun malamai, farfa\u0257o da kwamitocin gudanar da makarantu da \u0199arfafa \u0199ungiyoyin mata domin su ri\u0199a taka rawar da ta dace.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya ce \u0257aukar \u0199arin malamai \u0199wararru zai samar da sakamako mai kyau nan gaba.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Mahalarta taron sun fito ne daga Ladduga, yayin da wasu daga cikin mahalarta daga Karamar Hukumar Maigatari ta Jihar Jigawa suka halarci taron ta yanar gizo.<\/p>\n<p>COV: Adamu Yusuf<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>&nbsp; Haddadiyar Kungiyoyin Makiyaya na kasashen Africa (CORET) ta bayyana cewa an samu karin yawan \u0257alibai a makarantun makiyaya cikin watanni goma da aka fara shirin ciyar da \u0257alibai. &nbsp; Babban Sakataren CORET, Muhammed Bello Tukur, ya bayyana haka a taron kwana \u0257aya da aka gudanar a Kaduna domin \u0199ara wa ma\u2019aikata da abokan hul\u0257arsu [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":21,"featured_media":6623,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[3,1,11,10],"tags":[],"class_list":["post-6622","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-ilimi","category-labarai","category-labaran-gida","category-noma"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/IMG-20250922-WA0048.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6622","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/21"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=6622"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6622\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":6625,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6622\/revisions\/6625"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/6623"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=6622"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=6622"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=6622"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}