{"id":6611,"date":"2025-09-20T21:55:36","date_gmt":"2025-09-20T21:55:36","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=6611"},"modified":"2025-09-20T21:57:01","modified_gmt":"2025-09-20T21:57:01","slug":"yan-taaddan-lakurawa-sun-sake-zama-sanadin-mutuwar-mutane-da-dama-a-turmutsitsin-shiga-kwale-kwale","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/yan-taaddan-lakurawa-sun-sake-zama-sanadin-mutuwar-mutane-da-dama-a-turmutsitsin-shiga-kwale-kwale\/","title":{"rendered":"&#8216;Yan Ta&#8217;addan Lakurawa Sun Sake Zama Sanadin Mutuwar Mutane Da Dama A Turmutsitsin Shiga Kwale-kwale"},"content":{"rendered":"<p>Al&#8217;ummar Jihar Sakkwato na cike da fargaba da alhini bayan da wasu mazauna kauyuka da dama suka rasu a hatsarin kwale-kwale a Karamar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato.<\/p>\n<p>Lamarin ya faru ne lokacin da jama\u2019a ke tserewa daga wani sabon harin da \u2018yan ta\u2019addan Lakurawa suka kai, inda kwale-kwalen da ke dauke da mutane fiye da kima ya kife.<\/p>\n<p>Da aka tuntubi jami\u2019in hulda da jama\u2019a na Rundunar \u2018Yan sandan Jihar Sakkwato, ASP Abubakar Rufa\u2019i, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga wakilin Rediyon Najeriya a jihar.<\/p>\n<p>ASP Abubakar ya ce har yanzu ba a tantance adadin mutanen da suka shiga kwale-kwalen ba, yana mai jaddada cewa ana ci bincike da aikin ceto.<\/p>\n<p>Wani shaidan gani da ido, wanda bai so a bayyana sunansa ba ya shaida wa Rediyon Najeriya cewa wadanda lamarin ya rutsa da su mutanen kauye ne da suka tsere daga matsin lambar \u2018yan bindigar Lakurawa.<\/p>\n<p>Wannan hatsarin shi ne na hu\u0257u da ya yi sanadiyyar rasa rayuka a cikin watanni biyu a Sakkwato, lamarin da ya haifar da fargaba kan matsalar tsaro da kuma hatsarin shiga kwale-kwale a yankin.<\/p>\n<p>Mazauna Sabon Birni da kauyuka makwabta na ci gaba da zama cikin zullumi, inda miyagu ke kafa shingayen bincike, kona gonaki da korar jama\u2019a daga kauyuka.<\/p>\n<p>Rediyon Najeriya ta ruwaito cewa iyalan da suka rasa \u2018yan uwansu sun yi cirko-cirko a bakin kogin, yayin da masu aikin ceto ke ci gaba da nemo wadanda suka bace.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><strong><em>Daga Nasir Malali<\/em><\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Al&#8217;ummar Jihar Sakkwato na cike da fargaba da alhini bayan da wasu mazauna kauyuka da dama suka rasu a hatsarin kwale-kwale a Karamar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato. Lamarin ya faru ne lokacin da jama\u2019a ke tserewa daga wani sabon harin da \u2018yan ta\u2019addan Lakurawa suka kai, inda kwale-kwalen da ke dauke da mutane [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":6613,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,8],"tags":[1587,625,541],"class_list":["post-6611","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-tsaro","tag-hatsarin-kwale-kwale","tag-lakurawa","tag-sakkwato"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/image-77.png","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6611","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=6611"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6611\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":6614,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6611\/revisions\/6614"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/6613"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=6611"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=6611"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=6611"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}