{"id":6540,"date":"2025-09-18T14:52:26","date_gmt":"2025-09-18T14:52:26","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=6540"},"modified":"2025-09-18T14:52:26","modified_gmt":"2025-09-18T14:52:26","slug":"hukumar-alhazai-ta-jigawa-za-ta-shirya-taron-bita-na-musamman-ga-jamianta","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/hukumar-alhazai-ta-jigawa-za-ta-shirya-taron-bita-na-musamman-ga-jamianta\/","title":{"rendered":"Hukumar Alhazai Ta Jigawa Za Ta Shirya Taron Bita Na Musamman Ga Jami&#8217;anta"},"content":{"rendered":"<p>A kokarin ta na ci gaba da zaburar da ma&#8217;aikatan ta, Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce za ta shirya taron bitar sanin makamar aiki ga jami&#8217;an ta dake dawainiya da alhazai a gida da kuma kasa mai tsarki.<\/p>\n<p>Darakta Janar na hukumar, Alhaji Ahmed umar labbo ya bayyana haka bayan kamala taro na musamman da shugabannin sassa na hukumar da aka gudanar a shelkwatar hukumar dake Dutse babban birnin jihar.<\/p>\n<p>Yayi bayanin cewar, hukumar zata bada bitar ne ga jami&#8217;an da kuma shugabannin shiyya-shiyya kan hanyoyin kara kula da walwala da jin dadin maniyyata da kuma dabarun magance kalubale yayin gabatar da aikin hajji.<\/p>\n<p>Yana mai cewar bada horo na da matukar mahimmaci duba da yadda aka fara biyan kudin kujerun aikin hajjin 2026.<\/p>\n<p>Alhaji Ahmed Umar Labbo, yace tuni shirye-shirye sunyi nisa waje fara shirin dunkarar aikin hajjin shekarar 2026.<\/p>\n<p>A cewar sa, tsarin gudanar da aikin hajjin wannan shekarar yasha bam-bam da na shekarar 2024.<\/p>\n<p>Yayi nuni da cewar, a bana, 8 ga watan Oktoba wannan shekerar da muke ciki itace ranar karshe ta biyan kudin kujeran aikin hajji kamar yadda hukumar kasar Saudi Arabia ta bayyana.<\/p>\n<p>A sabili da haka nema Labbo yayi kira ga maniyyata aikin hajjin badi da su gaggauta biyan kudin ajiyar su na naira miliyan 8 da dubu dari 5 kamar yadda hukumar aikin hajji ta kasa NAHCON ta bayyana.<\/p>\n<p>Ahmed Labbo, ya yabawa Gwamna Umar Namadi bisa kula da ayyukan hukumar a kowane lokaci.<\/p>\n<p>NAHCON dai ta baiwa Jihar Jigawa kason kujeru fiye da 1,600 na maniyyatan aikin hajjin.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Usman Mohammed Zaria<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>A kokarin ta na ci gaba da zaburar da ma&#8217;aikatan ta, Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce za ta shirya taron bitar sanin makamar aiki ga jami&#8217;an ta dake dawainiya da alhazai a gida da kuma kasa mai tsarki. Darakta Janar na hukumar, Alhaji Ahmed umar labbo ya bayyana haka bayan kamala [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":6541,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[380,118,59],"class_list":["post-6540","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-bita","tag-hukumar-alhazai","tag-jigawa"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/IMG-20250918-WA0012.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6540","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=6540"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6540\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":6542,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6540\/revisions\/6542"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/6541"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=6540"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=6540"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=6540"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}