{"id":6510,"date":"2025-09-18T07:50:36","date_gmt":"2025-09-18T07:50:36","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=6510"},"modified":"2025-09-18T07:50:36","modified_gmt":"2025-09-18T07:50:36","slug":"gwamnatin-zamfara-ta-nemi-karin-tallafi-ga-yan-gudun-hijira","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamnatin-zamfara-ta-nemi-karin-tallafi-ga-yan-gudun-hijira\/","title":{"rendered":"Gwamnatin Zamfara Ta Nemi Karin Tallafi Ga &#8216;Yan Gudun Hijira"},"content":{"rendered":"<p>Gwamnatin Jihar Zamfara ta roki Hukumar Raya Kasashen Waje ta Kasa (FCDO), Premier Urgence Internationale (PUI), da sauran masu ruwa da tsaki da su kara tallafa wa \u2018yan gudun hijirar da ke jihar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Kwamishinan Bada Agaji na Jiha Alhaji Salisu Musa Tsafe ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake jawabi ga mahalarta taron na kwana guda kan shirin ceton rayuka da karfafawa da kuma juriya (LEARP) wanda kungiyar FCDO ta dauki nauyin shiryawa a Abuja.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A wata sanarwa dauke da sa hannun Daraktan Yada Labarai na Ma\u2019aikatar, Bashir Kabiru Ahmad, Kwamishinan ya bayyana cewa a halin yanzu jihar na karbar dubban \u2018yan gudun hijira daga al\u2019ummomi sama da 1,008 a fadin kananan hukumomin 14, kamar yadda aka gani a cikin rajistar zamantakewa na jihar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Alhaji Musa Tsafe ya bayyana cewa, tallafin da ake bukata ya hada da bangarorin Rayuwa, Karfafawa, samun tallafin Kudi da Manufofi da sauran abubuwan da za a iya yi da nufin rage radadin halin da \u2018yan gudun hijira \u00a0ke ciki a jihar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Alhaji Tsafe ya yabawa abokan aikin raya kasa bisa yadda suke ci gaba da tallafawa \u2018yan gudun hijira da sauran marasa galihu a Zamfara.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A cewarsa, aikin da aka tsara domin aiwatar da shi da kungiyar Premier Urgence International (PUI) za ta yi zai kasance muhimmin taimako ga al\u2019ummar jihar Zamfara.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya bayyana taron a matsayin wani ci gaba a kokarin jihar na inganta rayuwar \u2018yan gudun hijira da marasa galihu musamman mata da yara.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Alhaji Tsafe ya tabbatarwa da abokan huldar cewa jihar Zamfara karkashin Gwamna Dauda Lawal ta samar da tsarin siyasa da samar da yanayin da kungiyoyin agaji ke gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>REL\/AMINU DALHATU.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnatin Jihar Zamfara ta roki Hukumar Raya Kasashen Waje ta Kasa (FCDO), Premier Urgence Internationale (PUI), da sauran masu ruwa da tsaki da su kara tallafa wa \u2018yan gudun hijirar da ke jihar. &nbsp; Kwamishinan Bada Agaji na Jiha Alhaji Salisu Musa Tsafe ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake jawabi ga mahalarta [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":6511,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[5,1,11,10],"tags":[1564],"class_list":["post-6510","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-kasuwanci","category-labarai","category-labaran-gida","category-noma","tag-tallafi-gusau"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/ff6a60d6-ff21-4034-befc-59936c90add3.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6510","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=6510"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6510\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":6512,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6510\/revisions\/6512"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/6511"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=6510"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=6510"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=6510"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}