{"id":6413,"date":"2025-09-13T10:13:05","date_gmt":"2025-09-13T10:13:05","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=6413"},"modified":"2025-09-13T10:13:05","modified_gmt":"2025-09-13T10:13:05","slug":"sarkin-birnin-gwari-ya-yaba-da-tsarin-zaman-lafiya-a-yankinsa-yayi-kira-ga-manoma-su-ci-gaba-da-noma","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/sarkin-birnin-gwari-ya-yaba-da-tsarin-zaman-lafiya-a-yankinsa-yayi-kira-ga-manoma-su-ci-gaba-da-noma\/","title":{"rendered":"Sarkin Birnin Gwari Ya Yaba da Tsarin Zaman Lafiya A Yankinsa, Yayi Kira Ga Manoma Su Ci Gaba Da Noma"},"content":{"rendered":"<ul>\n<li><\/li>\n<\/ul>\n<p>Sarkin Birnin Gwari, Alhaji Zubairu Jibril Maigwari ya yaba da nasarar tsarin zaman lafiya da aka kaddamar a yankin kusan watanni goma da suka gabata, yana mai cewa ya dawo da kwanciyar hankali tare da karfafa wa manoma gwiwa su koma gonakinsu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Da yake magana a lokacin ziyarar gani da ido domin duba yadda tsarin zaman lafiya yake a Birnin Gwari, Sarkin ya ce yarjejeniyar zaman lafiya\u2014wadda ta samu da ha\u0257in gwiwar Mai Bai wa Shugaban \u0198asa Shawara kan Tsaro (NSA), Gwamnatin Jihar Kaduna, hukumomin tsaro da kuma wakilan \u0199ungiyoyin \u2019yan bindiga\u2014ya taimaka sosai wajen rage matsalar rashin tsaro a yankin.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya bayyana cewa ko da yake har yanzu ana samun yan kwace kwace daga wasu miyagu amma lamarin tsaron yayi sau\u0199i sosai idan aka kwatanta da shekarun baya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Sarkin ya bayyana cewa a tarukan da aka gudanar da shugabannin al\u2019umma, an shawarci manoma su koma gonakinsu duk da kalubale, ko da hakan na nufin amfani da taki na gargajiya a maimakon na zamani.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A cewarsa, da dama daga cikin manoma sun bi wannan shawara, abin da ya haifar da dawowar ayyukan noma a yankin saboda zaman lafiya da aka samu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Alhaji Zubairu Maigwari ya jaddada cewa nan da shekara mai zuwa, ana sa ran karin manoma za su koma cikakke gonakinsu idan zaman lafiya ya ci gaba da inganta.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A tattaunawa da aka yi da Danmasanin Birnin Gwari, Alhaji Zubairu AbdurRauf, ya bayyana cewa tsarin zaman lafiyar ya samar da damar zama tare, inda makiyaya da manoma ke aiki tare domin kare wannan yarjejeniya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya kara da cewa harkokin tattalin arziki sun fara farfa\u0257owa a Birnin Gwari, inda al\u2019ummomi da kansu ke taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya kuma roki Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Kaduna su fa\u0257a\u0257a tsarin zuwa wasu wurare masu fama da rikice-rikice, musamman \u0199auyukan kan iyaka da ke fuskantar barazanar shiga daga jihohin makwabta.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya jaddada cewa irin tsarin tabbatar da zaman lafiya da akayi a Birnin Gwari zai taimaka wajen dakile matsalolin tsaro a yankunan kan iyaka tare da \u0199arfafa \u0199o\u0199arin zaman lafiya a fadin \u0199asar nan.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A halin yanzu, an ziyararce yammacin Birnin Gwari\u2014ciki har da Dam \u0257in Fagoma da Sabon Layi da Gagumi da Kakangi da Kuma Randagi domin duba yadda manoma suka koma gonakinsu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A matsayin wani \u0253angare na yarjejeniyar, tsoffin \u2019yan bindiga da al\u2019ummomin yankin ana sa ran za su tashi tsaye domin kare yankinsu daga dukkan wani kallubalen tsaro.<\/p>\n<p>PR: Adamu Yusuf<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Sarkin Birnin Gwari, Alhaji Zubairu Jibril Maigwari ya yaba da nasarar tsarin zaman lafiya da aka kaddamar a yankin kusan watanni goma da suka gabata, yana mai cewa ya dawo da kwanciyar hankali tare da karfafa wa manoma gwiwa su koma gonakinsu. &nbsp; Da yake magana a lokacin ziyarar gani da ido domin duba yadda [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":21,"featured_media":6414,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,8],"tags":[1549,984,381,41,1548,956,1393,1550,327],"class_list":["post-6413","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-tsaro","tag-birnin-gwari","tag-ci-gaba","tag-manoma","tag-noma","tag-sarkin","tag-tsarin","tag-yaba","tag-yankinsa","tag-zaman-lafiya"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/IMG-20250913-WA0012.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6413","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/21"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=6413"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6413\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":6415,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6413\/revisions\/6415"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/6414"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=6413"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=6413"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=6413"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}